✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
NA
*Abdul azizu AAJ*✍
Da
*Neeratlurv*😍
Via O.H.W📚
*11-15*
*** *** ***
Washe gari da misalin karfe goma sha daya na rana,Abdul ya shirya tsaf ya shiga motarsa yaje gidansu Mama, yana zuwa ya kira wayarta ya sanar da ita yana bakin kofar gidansu.
"Yana tsaye sai ga Mama ta fito tana taku daya-daya, cikin yanayin Annashuwa Abdul ya rinka kallonta ko kifta ido baya yi, a hankali ta iso wurinsa tare da yin sallama, amma bai samu amsa mata sallamarta ba, cikin kallon mamaki Mama ta Dubi Abdul tare da kada masa hannu awurin idanuwansa, firgit ya dawo da hankalinsa wuri daya, sai kuma ta dubesa tace “Me kuma kake tunani haka, nazo wurinka ina sallama amma baka amsamin ba?” gyara tsayi yayi, sannan ya dubeta yace."
“zaki iya ganina a kowanne yanayi, saboda idanuwana sun tsinci kansu awurin kyakkyawar halitta wacce basu taba gani ba, kyawo mai gwarjini tareda tafiyarda hankalin mai kallo, wurinki nazo amma kyakkyawar fuskarki ta tafi da tunani na zuwa kallon fararen idanuwanki wadan da bansan dame zan misalta farinsu ba, naga adonki wanda ya zarce na dawisi, kunnuwana kuma suka ji zazzakar muryarki wacce ni ban taba jin sauti mai dadi irinta ba” sai ya kara zura mata ido tare da cewa."
“shin wannan kyawun da kwarjininki kina tunanin bazai iya zautar dani ba, nifa ina ganin kyawonki ya yiwa idanuwa yawan kallo zasu iya makancewa da ganin kyawon kowa wanda ba ke ba” murmushi ta saki tare da cewa."
“ai kuwa da zan samu haka da nafi kowa jin dadi, domin bazan so kaga kyawon wata wacce ba, wadda ba ni ba” sai ya sake sakin murmushi yace.
“in dai wannan ne baki da matsala, kafin ganinki naga ‘yan mata da dama amma banga wacce takai ki ba, ban kuma samu wacce ta mallaki zuciyata a ganin farko irinki ba, sannan bana jin SHAUKIN SON kowacce mace in bake ba, ni fa kasancewa ta tare dake a yanzu sai nake jina tamkar wani basarake wanda yake sarautar duniya”.
Mama ta fuskancesa tare da kallon so zuwa garesa tace “.
"ni tunda nake a rayuwata ban taba sanin dadin kalamai ba, sai da na hadu da kai, tunda nake ban taba jin abu mafi saurin magance damuwar zuciyata ba irin kalamanka ba, a rayuwata bana banbance kamshi da wari, amma zuwanka a kusa dani sai nake jin daddadan kamshi yana shiga hanci na tare gamsar da zuciyata, tabbas ina da yakinin zaka zamo jagora a rayuwata wanda zai zamo mafi kawo taimakon gaggawa acikin zuciyata, wanda zai zamo mai kore dukkanin dattin da yake zuciyata”.
"Abdul cike da SHAUKIN SO yace “ai ni da ke mun yi bankwana da dukkanin wani bakin ciki, na zamo fitilar zuciyarki mafi kawo haske a koda yaushe acikinta, sannan ke kuma kin zamo farin ciki acikin zuciyata wacce ta mamayeta tare da rufe dukkanin kofofinta babu yadda bakin ciki zai samu hanyar shiga, dan haka nake rokon Allah da yabarmu acikin aminci da son junan mu tare da yimasa godiya koda yaushe na babbar kyautar da ya bani wato ke!.”
"sai Mama tace “ni kuwa ina fargaba acikin zuciyata, saboda wannan farin ciki da nake ji a zuciyata mafin dadi kar wata rana ya zamo min bakin ciki mafi kuna a rayuwata”.
" cikin yanayin razana Abdul yace “haba Tauraruwa me yasa kike wannan tunani?”.
sai tace “saboda ina tunani ne akan Abbana, bana tunanin zai iya baka aurena”.
" da hanzari yace “saboda me?”.
" tace “saboda kai ba yaren mu daya da kai ba, dangin mu basu aurar damu ga wani yare wanda ba namu ba, haka zalika dan dangin mu baya auren wata wacce ba yaren mu ba”.
" jikinsa a sanyaye yace “in dai wannan ne ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu ni da ke ba zamu taba rabuwa ba”.
" sai tace “Allah yasa haka”.
" ya amsa da “Amin” sannan suka cigaba da hirarsu cikin farin ciki da jin dadi.
"Sai da aka Kira sallah 'n magriba tuku Abdul ya Mata sallama ya tafi zuciyarsa fal cike take Da *shaukin sonta* haka itama Nata zuciyar."
*** ***
Bayan wasu kwanaki soyayya mai karfi takara kulluwa tsakanin Abdul da Mama, duk tsananin tsoron da Mama take yiwa mahaifinta sakamakon ya dauki alwashin bazai aurar da ita ba, sai ga dan danginsu wanda suke yare daya wato FAKANCI kamar yadda suka saba, amma tsananin soyayyar da ta shiga tsakaninta da Abdul yasa ta debe dukkanin wani tsoro ko fargabar mahaifinta, hakan yasa ta baiwa Abdul damar ya turo iyayensa dan a tsayar da Magana wato ayi musu baiko. Wannan Magana tayi matukar saka Abdul cikin farin ciki sosai. "
"Amma yacemata da zarar yaje gida can wajen mahaipainsa zai sanar dasu inyaso ko bayan ya koma gidane sai ya turo."
'"Mama tayi na'am da zancen masoyinta."
"Rayuwa tana tafiyar musu cikin kwanciyan hankali suna zuba soyayyarsu yadda ya kamata, soyayyane tsabtatatce Ba irin na zamaniba."
"Abdul ya sanar da kawunsa sun yanke shawaran da zarar Abdul ya koma gida zai sanar da abbansa inyaso suji daga garesa akan wannan shawaran suka zauna."
"Haka itama Mama duk fargaba da tsoron mahaipinta datake hakan batajin zai iya hanata tunkarar sa da maganar Abdul duk da tasan abune mai wuyan yuwa amma zata gwada fasaharta ko Allah zai sa a dace."
"Dan ita a gaskiya idan aka rabata da Abdul toh tamkar anrabata ne da numfashinta dan son sa shine bugun zuciyarta, fatan ta da addu'arta Allah yasa mahaipinta ya janye zancensa na aurar da ita wa FAKANCI yan uwan su, kuma ya mallaka Mata Abdul matsayin mijinta."
_Masu karatu nasan kun matsu kusan waye ABDALLAH (Abdul) da MARYAM (Mama ) toh Ku biyo neeratlurv da Abdul AAJ dan sanin asalinsu_."
*NEERATLURV*😍
&
*ABDUL AZIZU AAJ*✍
(Na England)..
_Dedicated to Maryam (Mama)_❣
New Post
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Popular Posts
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO* 🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ Na *Abdul azizu AAJ* ✍ ...
-
11/2/2017 6:55pm *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis_...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ❣ ...
-
❣❣ ❣ MAYA! ❣❣ ❣ Via OHW📚 Neeratlurv.blogspot.com Wattpad@neerat_lurv 36_37 ***Sati daya da auren Ba abinda ya canza ku...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *Abdulazizu AAJ*✍ Da *Neeratlu...
-
❣❣ ❣ *MAYA! 🙍🏻♀* ❣❣ ❣ 1⃣1⃣ Via O. H. W📚 Neeratlurv.blogspot.co.ke Wattpad @neerat_lurv *** Tafiya suke kan hanya...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *NEERATLURV*😍 Da *ABDULAZIZU AAJ*✍ Via O....
-
15/3/2017 1:33pm *Muneerat*✍ *JININ JIKINA* _*111-115*_ NA *NEETATLURV*😍 _Based on fiction and love tale story_ _Dedicated to Aun...
-
19/2/2017 7:00am *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis...
No comments:
Post a Comment