(3/2/2017 8:16am) *Muneerat*✍
♦ *JININ JIKINA*♦
_Based on fiction and lo6e tale story_
NA *NEERATLURV*😍
_Dedicated to Aunty Sis_💞
®O.H.W
*61-65*
*** ***
Da dare bayan sallah'n magrib yawancin mutane sun watse daidai kune suka rage da dangi, suna shirye2 mika amarya gidanta."
"MUSKAN na kwance bisa gadon idonta a lumshe tana cize lebbenta ta dafe kanta arrrrrhhh tace alamar kan na Mata ciwo.'"
"Sis lpy ko dai kanki ne ke ciwo fareeda ce tayi maganar."
"Eh Sis kaina ke ciwo, ina ji kamar fadowa zai wlh.'
"Sorry bara na gayawa Mum toh , ta mike tare da ficewa dakin."
"Meena ce ta matso kusa da MUSKAN cikn kunnenta ta rad'amata amarya mun kusa kaiki wajen angon zaki warke inkin kasance dashi ki daure ta kanne Mata ido (wink)."
"Dukan wasa MUSKAN ta kaimata ta turo dan karamin bakinta tace Allah meena Bana son hk fa."
"Ai gsky na fad'a anyways mu bar zancen kawai."
"Mum ce da wata Yar uwarta Aunty maijidda suka shigo dakin fareeda na'a biye da su, har bakin gado inda MUSKAN Take Mum taje ta zauna."
"Daughter ciwon Kai ko? Nasan za'a Rina sabida yawan hayaniya da gajiya sannu yanxu Zan Kira FARIS d'in ya saimiki magani, yanzu ki tashi a shiryaki ga Aunty maijidda nan Zan turo Aunty Sis (ummu sultan ) su shiryaki kinji ki daure."
"Aunty maijidda sai kuyi hanzari sabida kar yan daukar amarya su zo baku shiryaba yanzu as Aunty Sis zata shigo."
"Tana fita Ba dadewa sai ga Aunty Sis, nan ita da Aunty maijidda suka shige ciki da MUSKAN."
_naso binsu daga ciki dan dauko rohoto amma mommah (Aunty sis) ta zunguro kaina ta koroni waje wai nayi karama kar naga abin manya_😃😃😃
"Wanka suka Mata da ruwan turaruka, jikinta sai sheki take zubawa da kamshi ga shi kuma ta sha gyran amare wacce Yar Maiduguri ta Mata."
"Cikin mintuna 30 su aunty sis suka shiryata cikin wata milk color lipaya jikin lipayan duk stones da flowers Wanda kalan flowers din golden color, MUSKAN ta fito daban kamar wata shuwa Arab ta zama ga wani fitinanen kamshi dake fita a jikinta.'
"Bayan an bata hadin amare taci takuma sha na sha nan Aunty sis suka ja hannunta zuwa falo inda su, Hauwa. M. Jabo, banaxir umar, ummu beenah, su batul mamnan, dasu Aunty Sdy Jegal, Ya hajja ce duk suke zaune dasu Mum."
"Bayan an zaunar da ita aka ta zuba Mata nasihohi hade da sirrikan rike miji, kamar su tsabta, kissan magana, kissan tafiya na kwanciya, gyran jikin mace, kula da Miji, da sauransu."
"Ita dai MUSKAN shiru tayi dan duk sun sata kunya kanta a kasa suka jera zuwa wajen Dad, dan yan daukar amarya tuni sun zo."
"Bangaren Dad zaune yake da shi da FARIS nan Mum da MUSKAN suka zauna bayan sunyi sallama an musu iso."
"Dad shima ya hada MUSKAN da FARIS duk ya musu nasiha sosai mai ratsa jiki, bayan yasake jaddadawa FARIS kan ya rike MUSKAN amana Dan ita amana ce wajensa, karka cutar da ita, kazamo mai faranta Mata da share Mata hawaye, banda cutarwa duk da nasan Baxakayi Ba but FARIS Ka kula."
"Da irin wadannan nasihan yata musu anyavasa izinin tafiya da amaryarsa."
"MUSKAN kuka ta soma ganin dad yace su tafi, shima Dad kwalla ya dinga shara FARIS ganin Baby boo na kuka kuma yanajii har cikin zuciyarsa yasa sa varin gidan gabadaya sabida he can't stand watching his baby boo crying."
"Har bakin mota Mum ta rakata hugging din Mum tayi tanata kuka su fareeda da humaira duk suka rufomata suna tayata da kyar aka ban bare ta jikin Mum aka sata mota nan aka dau hanyan gidanta dake unguwar game village.'
"Gidane dayaji kayan alatu Dana more rayuwa, upstairs ne, falon gidan guda uku daya na FARIS Wanda ya kasance komai nacikinsa blue and white har bedroom haka, sai kuma falon MUSKAN daya kasance pink and purple, falon baki kuma komai red and arsh color.'
"Bangaren kayan kitchen kuma ba'a magana komai daga Dubai akayi order duk wani abin yayi na kitchen Dad ya saimata kitchen dinta babba da store dinsa."
"Dakuna 6 ne a gidan, daya na part na FARIS, daya na part na MUSKAN sai guda biyu kuma Wanda akayisa na yara, dakuma biyun na saukar baki,."
"Komai na gidan yayi kyau duk waenda suka kawota sai sun yabatsarin gidan, sai 9:00 yan kawo amarya suka watse bayan Aunty sis tasake yiwa muskan durln dinta nasiha suka tafi, nan aka bar MUSKAN dasu fareeda, meena da kubrah, sai Yar rigamata Mjay dasu little, xubie, cute xarah, huddalah, yar fucika,da dai sauransu sunsa MUSKAN gaba sai tsokanar ta suke."
"9:30pm dadai FARIS da abokansa Anwar da Aliyu, sai su Mr fauxy, Dr sameer ameer, Dr meerah, al'amin, el Bahrain, da dai sauransu suka rako ango FARIS."
"Suna jiyo sallamar angwaye suka lullube fuskar nan suka sake sambada turaren wuta gaba daya gidan ya gwaraye da kamshi."
"Da sallama suka shiga bayan an ansa musu suka gabatar da abinda zasu gabatar, su Mjay sai fari da ido ake dan anga mr fauxy har da kashe murya wai ita ala dole taga handsome lolx."
"Nasiha su Mr fauxy sukawa ango da amarya bayan sun musu fatan samun zuri'a d'ayyiba suka musu sallama, har wajen motocin su FARIS ya rakasu."
"A kunne cute xarah da huddallah suka rad'awa MUSKAN wani Abu Wanda duk jin gulmana ban Kai ga jiba sai da na hakura, hannu suke dagamata suna kanne Mata ido daya."
"Bayan FARIS ya rakasu ya dawo ya rurrufe ko ina ya wuce dakin MUSKAN, a tsakiyar gado ya taddata Tasha lullubi, zuwa yayi har inda take ya yaye lullubin wani kamshine ya bugi hancinsa nan ya lumshe idanunsa yace."
"Tsarki ya tabbata ga allah da mallakamin wannan kyakyyawar, yakuma vani ikon saminta matsayin matar aure hakika nayi dace."
"Hannu bibbiyu tasa tana kare fuskarta dan wani fittinannen kallo da FARIS ke binta da shi."
"Baby boo kunyata kike ji? Pls ki bud’e fuskarki, ko kina so kisani hawan jini ne, kinsan yadda na azbatu da rashin ganinki a kwanakin nan Ku pls kibud'e hannu yasa kan Nata hannun ya cire Nata daga fuskar."
"Murmushi ta sakar masa shima maida Mata yayi yace ki tashi muje muyi alwala mu nuna gdyr mu wajen ubangiji."
"Alwala yaje yayi bayan ya fito itama taje tayi, nan ya jasu sallah raka'a biyu vayan sun yi sallama ya dafa goshinta ya musu addu'oi da dama nasamun zaman lpy da zuri'a ta gari."
"Kallonta yayi yace Baby boo tashi ki mikomin wancan ledar, tashi tayi ta d’auko ta mika masa, tashi yayi yaje ya dauko tray da tumblers cup ya dawo ya baxa Kazan kan tray ya bude fresh milk ya juye a cups."
"Matso ki ci yace da ita Yana kaffeta da ido."
"Uhmmm nifa a koshe nake."
"A'a ban yardaba yaushe hid'ima ya barki kika ci abinci, wlh ko kizo kici kona d’uramiki."
"Jin yace zai d’uramata yasata matsowa da sauri, can kasan zuciyarta tsoro ne ya cika dan su cute xarah sun gayamata ta sake taci kazar wlh shima sai yayi abun."
"Jinta kawai tayi a cinyar mutum xatayi ihu taji yace shhhh nine FARIS oya bude bakin ki ki daina tsoro ba abinda Zan miki."
"A tsorace ta bude bakin nan yata feeding dinta har saida ya tabbata ta koshi ya kyaleta, shima yaci nasa.'
"Bayan sun gama ci ya umar ceta da ta sauya kaya tazo su kwanta yabata wani sleeping dress yace tasa."
"Toilet ta shiga ta kullo kofar ta sa kayan, amma ina bazata iya fita FARIS ya ganta da shigar nan Ba OMG ya zanyi, zama tayi kan seater'n toilet din."
"FARIS dama yasan za'ayi haka, mikewa yayi yaje kofar toilet din yace Baby boo ki fito Ba abinda Zan miki kinji."
"Shiru tayi can kuma tace toh Ka kulle idonka sai in fito."
"Ok na kulle ki fito."
"Bude kofar tayi ta leka saida ta tabbatar da baya ganinta tayi gudu sai kan gado ta shige cikin blanket din."
"Dariya yayi yaje shima ya shige cikin blanket din ya ringino inda take ya rungumota.”
"Tanajin ya rungumeta jikinta ya dau rawa, FARIS ganin haka yace Baby Boo ki daina tsorona Ba abinda Zan miki kawai ina son jin dumin jikinki ne pls let me be Baby boo."
"Ajiyan zuciya ta sauke, daga nan kuma batasake cewa komai Ba haka shima, a rungume sukayi bacci.......
_*MusFar*_ asuba ta gari...........
© *NEERATLURV*😍
New Post
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Popular Posts
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO* 🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ Na *Abdul azizu AAJ* ✍ ...
-
11/2/2017 6:55pm *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis_...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ❣ ...
-
❣❣ ❣ MAYA! ❣❣ ❣ Via OHW📚 Neeratlurv.blogspot.com Wattpad@neerat_lurv 36_37 ***Sati daya da auren Ba abinda ya canza ku...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *Abdulazizu AAJ*✍ Da *Neeratlu...
-
❣❣ ❣ *MAYA! 🙍🏻♀* ❣❣ ❣ 1⃣1⃣ Via O. H. W📚 Neeratlurv.blogspot.co.ke Wattpad @neerat_lurv *** Tafiya suke kan hanya...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *NEERATLURV*😍 Da *ABDULAZIZU AAJ*✍ Via O....
-
15/3/2017 1:33pm *Muneerat*✍ *JININ JIKINA* _*111-115*_ NA *NEETATLURV*😍 _Based on fiction and love tale story_ _Dedicated to Aun...
-
19/2/2017 7:00am *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis...
No comments:
Post a Comment