New Post

Friday, 17 March 2017

SHAUKIN SO

✨✨✨✨✨✨✨✨✨
    ❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
       ✨✨✨
         ✨✨
           ✨

NA

*ABDULAZIZU AAJ*✍
              DA
*NEERATLURV*😍

Via O.H.W📚

               *41-45*

  _*Second to the last page*_

       ****        ****

Tun da safe Da Abdul yayi sallar Asuba, ko tsayawa karyawa bai yi ba yayi bankwana da mutumin ya tafi.”
  “ Bayan Abdul ya baro gidan mutumin sai kuma ya dawo kofar gidansu Mama, yana zuwa ya tsaya wurin wata bishiya batare da ya aika kowa kiran Mama ba.
Yana zaune sai ga Mahaifin Mama ya fito zai tafi cikin gari, wurin dube-dubensa sai yaga Abdul, ganin Abdul yayi matukar bashi mamaki dan bai yi tsammanin Abdul zai sake dawowa ba, kuma sai yaga raunuka ajikinsa amma hakan bai hana shi dawowa ba, batare da ya cewa Abdul komai ba ya kada kansa ya tafi, shima kuma Abdul bai cemasa komai saboda gudun fushinsa, shi dai kawai ya zauna ne koda Allah zai sa yaga masoyiyarsa.”

 “Da Yamma Mahaifin Mama ya dawo gida, amma kafin ya shiga ya sake ganin Abdul batare da yace masa komai ba ya shige cikin gida.”

 “Har dare yayi Abdul bai ga Mama ba, sai ya yanke shawarar kwana karkashin bishiyar saboda ba inda ya sani, haka kuwa yayi.”

 “Washe gari mahaifin Mama zai fita ya sake ganin Abdul amma baice masa komai ba ya wucewarsa, da Yamma da ya dawo ya sake ganinsa, wannan karon ma baice masa komai ba ya shige cikin gida. Abdul kuwa mamaki ya ishe shi dan tsawon kwana biyu kenan bai ga koda lekowar Mama garka ba, amma kuma a zuciyarsa bai cire tsammanin ganinta ba, haka yasa ya sake kwanciya anan gindin bishiyar.”
  “Tsawon kwana Hudu Abdul yana wurin ba abinda yake ci sai ruwan da yake sha a wani Fanfo da yake unguwar, ba abinda yake sa ya dauke idonsa ga kofar gidansu Mama sai Sallah amma duk tsawon kwanakin nan bai ga abar kaunarsa ba Mama. Kuma kullum sai mahaifin Mama ya gansa.”

  “Mahaifiyar Mama ta kawo wa Malam abinci wato mahaifin Mama, sai ta zauna, bayan ya kammala cin abinci ya dubeta yace “Mamar Mama kin kuwa san wani abu da yake faruwa?” sai ta dubesa tace “Malam ai sanin abinda yake faruwa sai ku dake fita waje” sai yaci gaba da cewa “Yaron nan wanda Mama ta kafe shi take so, yau tsawon kwana hudu kenan yana bakin garkar nan, duk tsananin abinda nasa yara suka yi masa amma bai hanashi dawowa ba” sai tace “To Malam wallahi ina tausayawa yaran nan, ka dubi yadda suke son junan su, banga abin aibu ba idan kuka bari suka auri junansu ba, ka dubi yarinyar nan yau tsawon kwana shida bata gidan nan mun yi nemanta amma mun rasa duk inda ake tsammanin taje bamu sameta ba, yaron da kake kokarin aura mata yanzu yana can ko ajikinsa babu wata damuwa, amma mu gamu cikin damuwa ko zowa gidan nan ya daina”.
Sai ta numfasa sannan taci gaba da cewa “muna ta zargin ko tana wurin yaron nan, to gashi ashe ba can take ba, ni daman nasan bazata je can ba, dan tasan sai anje nemanta can. To amma Malam me yasa tun farko baka gayamasa bata nan ba” sai Malam yace “saboda shi nakeso ya nemo muna ita, in yaso idan ya dawo muna da ita saina koresa” sai tace “Haba Malam ai wannan daukar alhaki ne, baka tunanin Allah ya tambayeka?” sai yace “ke gafara ke kullum baki ganewa, shin ya za’ayi na baiwa Bahaushe auren ‘ya ta” sai ya tashi tsaye sannan yaci gaba da cewa “Bari na fita nasan yanda zanyi” batare da ya jira amsa ba ya fita waje.
Yana fita waje yaje ya samu Abdul zaune yayi masa sallama, Abdul cikin rawar jikin murnar ganin Mahaifin Mama yazo wurinsa ya amsa sallama, ya durkusa ya gaishe sa, sannan mahaifin Mama ya dubi Abdul yace “Nasan na walakantaka amma kuma hakan baisa kayi fushi damu ba, sannan munyi kokarin rabaku, to amma yanzu nagane lallai idan muka yi haka, to muma zamu dawo nadama, dan haka in dai ni ne na amince da aurenka da Mama” cikin fara’a da murna Abdul yace “Baba nagode sosai, tsawon lokaci kunnuwa basu ji kalma mafi dadin saurare ba irin wannan, ina Mamar take?” sai Mahaifinta  yace “Yau tsawon kwana shida Mama tabar gida bamu san inda taje ba, duk inda muke sa ran mu ganta munje amma bamu ganta ba” sai Abdul yayi zaune cikin sanyin jiki, sannan ya dubi mahaifin Mama yace “Baba kada kadamu insha Allahu duk inda Mama take saina nemo ta indai tana duniyar nan” sai yace “bakomai nagode, Allah yabaka sa’a” “Amin” Abdul yace haka, sai mahaifin Mama ya shiga gida.”

  “Bayan ya tafiyarsa sai Abdul ya dawo tunanin inda zai fara neman Mama, gashi Mama ba waya bace da ita ba yanzu, sakamakon mahaifinta ya karbe, gashi shima kuma mahaifinsa ya karbe wayarsa ballai yayi tunanin zata kirasa. Yana cikin wannan tunani sai ya runtse idanuwansa, yana nazarin inda zuciyarsa zata bashi Mama take. Can sai ya bude idanuwansa sakamakon zuciyarsa ta gayamasa inda Mama take.
Kafin Abdul ya tafi yaje gidan bawan Allah nan wanda ya taimakesa lokacin da Yara suke jifansa domin ya samu taimakon kudin mota awurinsa, bayan yaje ya nemeshi taimakon kudin mota cikin nasara ya dauko kudin ya bashi, sai Abdul yayi godiya ya tafi.”

Abdul yazo bakin titi ya tare motar zuwa garin Fakai nan yake tunanin somota gidan kawunta dake fakai ya shiga motan. Bayan sun iso Fakai aka sauke shi ya biya, bai tsaya ko ina ba sai gidan Kawun Mama don nan zuciyarsa ta gayamasa masoyiyarsa taje, yana zuwa ya samu yaro ya tare sai yace dashi “Dan Allah shiga gidan nan kace Abdul na kiran Mama” sai yaron ya shiga cikin gidan ya isarwa mutanen gidan sakon da aka aiko shi, sai yaro ya fito ya sanar da Abdul ya isar da sakon da ya aikesa, Abdul yayi godiya ga yaro, sannan yaron ya tafi.”

   “ Yana tsaye sai ga Kawun Mama ya fito a firgice, yana zuwa Abdul ya durkusa ya gaishe shi, sai Kawunta yace “Kai ne Abdul?” Abdul ya kada kai yace “Eh ni ne Kawu” sai yace “Wallahi tunda Mama tazo gidan nan kwananta biyu tabar gidan bamu san inda taje ba, saboda ana yawan yimata zancen ta hakura da kai” cikin firgita Abdul yace “Kawu nan ma bata nan kenan, Inalillahi wa’inna ilaihir raju’un” sai Kawunta yace “Daman ba gurinka taje ba, dan nasan bazata koma gida saboda dalilinka tabaro gidan” sai Abdul yace “Bata wurina naje gidansu akace kwanan ta shida bata gida, shi ne nazo nan, amma baraz an bincika wani wuri” sai Kawu yace “dan Allah kataimaka ka nemo muna ita bamu san halin da take ciki ba” “Bakomai” Abdul ne yace haka, batare da ya jira Kawunta ya sake cewa wani abu ba, kawai yabar kofar gidan.”

Daga alkalamin:-

 *NEERATLURV*😍
          &
*ABDULAZIZU AAJ*✍
 (Na England)...

  _Dedicated to Maryam (Mama)_❣

No comments:

Post a Comment

Popular Posts