13/3/2017 9:36am *muneerat*✍
*JININ JIKINA*
_*106-110*_
NA *NEETATLURV*π
_based on fiction and love tale story_
_Dedicated to Aunty Sis_π
*PERFECT WRITERS FORUM*
(P.W.F)
_Thank y'all for the #teams MUSKAN & FARIS voters i really appreciate it though nobody vote the #team fatyπbut she says she loves y'all #onelurv π_
Kwanaki sunata shudewa hakama ranaku abubuwa da dama sun faru cikin wadannan kwanakin har zuwa yanxu da ake gobe daurin auren FARIS da faty, duk iya kokarin MUSKAN na ganin ta had'iye mai ke damunta takasa kullum cikin kuka take dama -dama ma dasu fareeda ke dan debemata kewa suna tayata hira da k'wantar mata hankali da kalamai masu taushi, ba a bar su mum da dad a baya ba awajen kula da farantawa MUSKAN rai, tunda incident d'innan yafaru tsakanin MUSKAN da FARIS batasake kulasaba, duk hanyanda zata hadasu kauracewa take haka da zarar yashiga d'aki ta tabba shi dinne zata kwanta kamar mai bacci haka zai kare wa kyak'yawan fuskarta da jikinta kallo wani sa'in ya bata peck (light kiss )a kumatu ko a lip ko ya gyramata kwanciya yatafi."
"Su faty amarya anyi events kala -kala na keche raini akayi duk event din ta hade da ita da angonta, ta gaiyato kawayenta daga kasashe daban -daban kuma duk yan duniya ne, haka shima FARIS ya gayyato abokansa amma basukai na faty yawa ciki harda su Anwar da Aliyu wanda da kyar yasamu suka yarda zuwa auren dan su afad'arsu suna yin MUSKAN ne ba faty ba."
"events sunyi ba karya saidai dangin FARIS kodaya ba wanda ya hallaci event din kama daga mum, MUSKAN su fareeda da yan uwa sabida duk cikinsu ba wanda yake murna da wanga auren."
"sanin ba wanda zai kulasa yasa bai ma yimusu maganar zuwaba, faty kam taji dadin rashin zuwan nasu ma hakkan shi Yafimata alheri a ganinta."
"A gidanan 9ja zasu xauna FARIS yasake gina tangamemen gida tsarin gidan hak na turawa sabida mr fauzy ne yayi zanen gidan tsaya fadin tsaruwan gidan da girmansa bata lokacine amma gidan yakai gida kowacce mace da part dinta kuma gidan upstair ne, a nan nijeriya zasu tare da zama saidai shi FARIS idan yagama cin amarci zai koma bakin aiki ansamowa MUSKAN transfer daga can tadawo da karatu Nile University dake abuja fadar Dad abarta anan sabida zata fi samin nutsuwa."
"Yau jumma'a misalin karfe 2:00pm aka daura auren faty da FARIS akan sadaki naira dubu dari auren da manya -manyan yan siyasa da kasuwa suka hallata sai dai ko kotan mutannenda suka hallacin daurin auren MUSKAN faty bata samuba."
"Andaura aure lafiya lau ango sai washe hakora yake wani dadi yake ji wanda shi kansa baisan na meyeba, abokansa sai faman tsokanansa suke da yimasa tsiya."
"A cikin guest house na daddy akayi reception na maza."
"lokacinda MUSKAN taji an daura auren FARIS wani irin kukan bakin ciki ta rushe dashi duk yan uwa sunyita rarashinta da kyar ta tsaida kukan amma can cikin zuciyarta *Hawayen masoyi* (sis rabi'at sk mash &Mr smile ) shike zuba daga idanunta."
"Wow! Amarya faty basai na tsaya fad'a muku yadda zata kasanceba danyin haka bata lkc ne amma baki haryakasa rufewa dan murna ko kunya bataji yadda take abu kamar ba amarya bane."
"Da dare andauki amarya aka kaita gidan mijinta dake ashokoro, yadda part nata ya hadu hmmmm ba karya komai nata ja da baki kamadaga kushin, kayan kitchen, pent ds."
"lokacinda kowa ya watse aka barta da kawayenta nan suka bude babin hira harda ita kamar ba itaceba amaryan sabida lullubinta ta yane tazauna acikinsu sunta shan hira kuma duk akan zaman da zatayi da MUSKAN suke munafunci iri -iri da abuba da dama suke kunsawa faty akai yadda zata maida MUSKAN mowa wajen FARIS suke fad'amata sai babbake dariya suke kamar gidan rawa haka gidan ya koma."
"kafin FARIS yatafi wajen amaryansa dad yace yabiya yadau MUSKAN itama yau zata koma gida kuma yahad'ata da humaira sutafi tare sabida zaman kad'aici taji dad'in hakan dukda bason komawa takeba."
"An ajiyesu ansake musu nasiha kamar sabon auren Dad yace yamasan MUSKAN batada matsala saidai kai FARIS ka kula kazama adali mai adalci tsakanin matanka, ire -ire wadannan nasihan yarinka masa, saida ya tabbata yamasa nasiha sosai yabasu izinin tafiya,yabawa MUSKAN key mota sabuwa pill kirar KIA Yacenatane kyauta yabata harda kuka dan murna tayitamasa gdy, ba'abar mum abayaba itama tayimusu nata nasihan ankai ruwa tukun akaraba MUSKAN da mum da fareeda tana matsar kwalla suka kama hanya taki zama a gaba a bayan mota tazauna tare da humaira."
"kamar FARIS yasan *bad'akala* (kwaishe) da ake a gidansa baiyi gigin gayyatan abokai su rakasaba daga shi MUSKAN da humaira kadai suka hanyan gidansa."
"lokacinda suka isa gidan tundaga waje har suka doshi falon suna jiyo muryansu, bangaren MUSKAN yanunawa humaira yace taje ta tajirasu itakuma MUSKAN babban falon gidan dake kasa yanuna mata yace tajirasa yana zuwa ba musu duk suka bi umarnin sa."
"A lokacinda ya isa kofan d'akin faty kamar kunnensa ya fashe dan yadda suke ihu suna babbake dariya, rai yahada fuskarsa a murtuke ya bankaje kofar, a rayuwa ba abinda FARIS ya tsana kamar hayaniya, ido curu -curu suka a lokacinda suka hango FARIS ko wacce tasoma tattara kwarmatsonta suna shirin barin gidan, angrily yace faty tasamesa a falon kasa bai jira mai zataceba yajuya yabarta a d'akin, mchwww! Duk sukaja tsaki itakuma tabi mijinta, duk fita sukayi kowa tayi gidan ubanta."
"Duk ya tarasu a falon tunda faty tashigo taga MUSKAN tasoma wani shu'umin murumushi tana wani rankwasa da juya ido,zama tayi kusa dashi jikin FARIS ta shige da gangan dan ta bakantawa MUSKAN rai amma ko kallon inda suke MUSKAN batayi, shikuma tunda faty ta shige jikinsa yaji wani rin yarrrrr a jikinsa gawani dan iskan kamshin turare dayake fitadaga jikinta rikitasa take yanemi nutsuwarsa yarasa da kyar ya daidaita yasoma musu nasiha kamar yadda addinin islama ta tadana a gurguje yasamu ya kammala bayan yace da zarar yagama sati daya a d'akin faty girki zai koma 2-2days, ba abinda MUSKAN tace dasu haryagama yatambayeta ko tana da wani abin fada tace babu, yace toh ta wuce d'akinta saida safe, baby mujemana faty tace dashi ok toh haka tana kallonsu suka wuce faty rungume dashi, dan bakin ciki dayawa MUSKAN yawa kasa kuka tayi kawai murmushin takaici tayi ta wuce nata part din."
"wow! Part na MUSKAN yaci uban na faty nesa ba kusaba duk da iyayen faty sun narka arziki amma bai kai wanda aka narkawa MUSKAN ba ita kallon nata komai ligh purple da pink falo da kitchen d'akuna kuma Golden haka babban royal bed dinta na duka dakunan side dinta golden ne komai nata yayi wanne yar wata sarki ko shugaban kasa haka dakinta yake, ta sami humaira harta sauya kaya zuwa na bacci itama haka ta sauya ta dauro alwala tazo tayita nafiloli, saida ta idar suka soma dan taba hira da humaira ko abinda yafaru bata fadawa humaira bacci tasoma ji tacewa humaira su kwanta dan gobe zasu makaranta kasancewar itama humaira a nile University tuke karantu, kuma ita MUSKAN a goben zata fara fita School din."
"Amarya da ango kam saidai muce sam barka sabida suna shiga d'aki ba kunya faty tasoma romancing din FARIS abunka da mai nema tuni ya biyemata da kyar yasasu sukayi sallah'n raka biyu da ya wajaba nan ma ita ta nemi yahada kwanciya da ita."
_waiyazibullah ya Allah ka tsaremu daga irin halin mata kamarsu faty, ace anyi mace ba kamun kai ba aji, ko kunya, yaku yan mata da manya mata mu na lura muzama daya daga cikin matan da Allah s.w.t yake suffantasu da matan hurul ayn, mukance masu alkunya da kamun kai..Allah yasa mudace AMIN YA RABBI_
"Ango FARIS fa an angwance duk da ba a Virgin yasami faty ba but bayida nacewa sabida yadda tsafi ke dako dashi."
"saida suka sami nutsuwa bayan sundibi kusan tsawon awa 2-3 suna abu daya, wanka ma duk tare sukayi suna zuba love abinsu."
"ko da suka gama duk abinda zasuyi suka nemi lafiyar gado."
Su amarsu ta ango saidai muce asuba ta gari............
**
Washegari tun sallah'n asuba da sukayi MUSKAN batasake komawa kwanciyaba azkar tarinka yi harsaida taga gari yadanyi haske nan dinma ba baccin ta komaba kitchen ta nufa dake bangarenta tasoma had'a breakfast na gidan gaba daya, Irish potatoes ta fere ta soya sa da eggs dinta ga peppers soup nata na chicken sai shayinta dayasha kayan kamshi ta hada ta juyewa su FARIS a warmers tazuba nasu da humaira takaimusu dining suma FARIS takaimusu part din faty a bude ta tara suma a dining ta ajiyemusu tabar dakinsu."
"data koma tahada komai na kitchen datayi amfani dashi ta wanke tasss tayi mopping haka falonta ta kunna turaren wuta na yan Maiduguri dana kaimata gudumawa π duk gidan ya bulbule da kamshi, ganin har kusan 8:00 yasa bata koma bacciba dan dama 9:00takeda lectures, d'aki tawuce tayi wanka data fitone ta tada humaira tace tayi wanka itama, humaira da bacci bai ishetaba ta mike a wahale tayi wanka tafito tasami MUSKAN ta shirya tsabb cikin wata super lemon green dinki zamani akawa rigar tadaura zaninta kwass abinta tasha ado kamar wata amarya sai shining take like a star, baki wangale humaira take gininta tace mata kai aunty kinyi kyau, na gode tace da ita kiyi maza kishirya yanxu kusameni a falo toh ta bita dashi kawai, Itama atamfa tasa amma ita d'inki riga da skirt tayi kyau itama, a falo ta sami MUSKAN, dining MUSKAN taja suje suci abinci full of surprise tace MUSKAN yaushe kika tashi har kinyi breakfast and all those work, hmmm kekike bacci ni nagama komai nasu FARIS ma na kaimu-humaira bata bari ta karasa maganarba tace kardai kucemin ke kikamusu girki? Of course yes ni namusu ta bata amsa, you are stupid wlh yanxu har girki zaki musu Allah kinbatan rai nikam, sorry lil sis amma kinsan hakkina ne na musu and kinga ni fa duk abinda suke kansu sukewa kuma fadar ubangiji da nasu mum nake bi if not am not gonna do it babe."
"Toh naji yanxu muci abincin mutafi school karmuyi missing lectures ko, toh MUSKAN tace bayan ta zuzzubamusu abincin da tea suka soma ci.,"
"inless than 20mins suka kammala komai suka fito a sabuwar motanta da dad ya siyomta KIA tajazu suka tafi school kota kansu FARIS basubiba."
"toh su amarya kuma sai 11:00suka tashi wanka suka chaba ita da angonta dasuka fito sukaga warmers a kan dining nan suka baje suka kwashi girki abinsu."
"koda suka gama garden na gidan suka fita shan iska suna zuba love wane su cinye junansu ko fita yau FARIS baida niyan yi idan baki sunzoma wajen amarya ma hira ka'dan suke taba ta sulale wajen mijinta π."
"FARIS baidamu daya duba MUSKAN ba kuma baiji motsintaba koda yamma dasuka dawo basu haduba suma basu nemesaba, nan ma indomie dinsu suka dafa da eggs sukayi pilling suka ci nayanxu kam basu kaiwa su faty ba.
•••••
Lives moved on haka rauywarsu ta kasance har 1week koda FARIS zai koma d'akin MUSKAN ranar ma faty bata kyalesaba har saida yabiya mata buka tarta taga ta mantar dashi MUSKAN har tasake jansa suka kwana tare, kullum haka take da zarar randa tasan girkin MUSKAN ne saitayi abinda FARIS bazasa wajen MUSKAN ba."
"ita dai MUSKAN na gani ikon Allah amma ko ajikinta bata taba nunawa koda a fuskaba and bata sakewa humaira ta gane komai dake gudana, kuma ko mum takira ta tambayeta ya zamansu? da Matsala? Duk saidai tace masha Allah ba komai shiyasa mum ke kara son MUSKAN cikin ranta."
"duk kwanakinda suke shudewa FARIS basu cika haduwa da MUSKAN ba watarana su hadu yaxo shiga gida tana fita ko yana fita tana shiga, girkima yanxu taciresu kowa shi ke nasa, karatu ya kankama yanxu suna second semester exams zasu fara duk hankalin MUSKAN na akan karatunta dad'inta ma daya course dinsu daya da humaira kuma aji daya suke shiyasa kullum zaka gansu da laptop ko test books agabansu suna karatu."
"duk iya zamansu ba wanda ke zuwar musu gida sai zaryan kawayen faty dasuka maida gidan kamar gidan ubansu, kullum suna cikin zuwa gidan."
"Abun FARIS fa sai addu'a sabida aikin ma yanxu saida suka yomasa transfer yadawo gidan Nigeria da aikin."
Yanxu almost getting a month da aurensu faty while MUSKAN kuma tana 3month 2weeks da auren FARIS."
"yau kamar kullum ba school humaira tafita unguwa while faty itama taje gidan wata kawarta, MUSKAN kadaice a gida tana zaune batama jin dadi 2days kasala da yawan bacci sun mata yawa ga yawan kwadayi tarasa mai yasameta tana cin gautanema yanxu dan tashin zuciyar da yake damunta karar tsayuwar mota taji cikin ranta tace Allah yasa humaira ce dan ni nagaji dazama ni daya wlh."
"FARIS ne yashigo bayan ya Parker motarsa ya shiga cikin gida yunwa yakeji yaje part na faty bata nan duk iya bincike yayi amma ba abinci a part dinta, haushi duk ya cikasa har ya zauna komai ya tuna oho ya mike yayi hanyar dakin MUSKAN da sallamarsa yashiga ta amsa masa amma bata waiwayi inda yakeba."
"gefenta yaje yasamu yazauna yace MUSK- bai karasa tamike a guje tayi hanyan kitchen sink tasamu tasoma kwarara amai wane hanjinta zasu fito waje kamshin turarensa kadai dataji shi yasata amai."
"A guje yabiyota kitchen din bayanta yaje yatsaya duk ya kidime yanajin yadda take amai saiji yayi tausayinta ya darsu cikin ransa he cannot stand any more zuwa yayi, yayi hugging dinta yana bubbuga bayanta yanata fad'in sorry har saida tagama ta kuskure bakinta tana juyawa ta kwace jikinta daga hugging din da yamata binta yasoma dayaga tana tafiya yana kiranta amma ita ko juyawa batayi ba harta kai falo ta zauna.
"shima biyota yayi yasoma tambayarta bata da lapiyane taki amsasa dayaga haka yace ta tashi suje asibiti, tabb nan fa tace ba inda zata, dayaga da gaske take, yabata rai shima forcefully yasoma janta bayan yaja hijabinta dake kan kujera tana tirjewa yana janta saida yadakamata wani irin tsawa daya tsoratata ba shiri tayi tsitt haryasa a mota ya kama hanyar asibiti."
"suna isa asibiti basu wani sha wuyaba suka sami ganin Doctor kasancewar FARIS yasansa, Doctor yama MUSKAN wasu yan tambayoyi duk ta amsamasa nan yasa wata nurse ta karbi fitsarinta a gwada."
"in less than 30mins nurse din tadawo da result na fisarin, Doctor yana gani yakaranta yana ganawa yace wa FARIS congratulations matarka na dauke da juna biyu na wata daya da yan kwanaki."
"FARIS daya tashi daga zaunenda yake yayi hugging na MUSKAN yana bata peck ta ko ina yama manta asibiti suke saida tadan cijesa a kunne yadawo hankalinsa, gdy da kyauta ya ma Doctor da nurse din, bayan doctor yakaranta musu jawabai da ya kamata suka kama hanya, yama rasa idanda xaisa kansa duk da FARIS ba a hankalinsa yakeba but yana son baby musamman daga MUSKAN wacce takasance *JININ JIKINA* he can't deny it he loves it and yakasa boyewa."
"tun a hanya yasoma sayesayen kayan kolama sabida Doctor yafadamasa mata masu ciki na kwadayi itadai MUSKAN ido take binsa dashi kawai bata magana."
"kafin su karasa gida saida yayi siyesiye dayawa, suna Parker mota faty na shigowa gidan itama ganinsu tare kuma FARIS yazaga yana budewa MUSKAN kofa yasa faty fitowa a harzuge tayo wajensu da saurinta amma ina kafin takarasa MUSKAN takama hanyan shiga cikin gida FARIS kadai ta tarar ko sannu dazuwa babu tace baby daga ina?."
"Daga asibiti yabata amsa."
"doing what at hospital? Tasake tambaya "
"MUSKAN ce ba lafiya nakaita ganin Doctor."
"And sukace mai yake damunta."
"Enough! Ya kina ta min tambaya kamar wacce take a lawyer."
"yes dole na tambaya i wanna know what happen to her."
"okay fine kinaso kiji ko toh ciki ne da ita she's taking my baby."
"WHAT! Tafada da kakkausar murya CIKI Noooooo bazai yuba I have to do something bazata zauna da cikin nan ba da gudu tadau motarta ta fita a gidan @360."
"shikam FARIS ko kallonta baiyiba yasa kai ya shige cikin gidan ".
neeratlurvblog.wordpress.com
© *NEETATLURV*π
New Post
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Popular Posts
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO* π· ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ Na *Abdul azizu AAJ* ✍ ...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ π©π» *MAYA* π©π» ❣❣ ❣ ...
-
11/2/2017 6:55pm *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*π _Dedicated to Aunty Sis_...
-
❣❣ ❣ MAYA! ❣❣ ❣ Via OHWπ Neeratlurv.blogspot.com Wattpad@neerat_lurv 36_37 ***Sati daya da auren Ba abinda ya canza ku...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*π· ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *Abdulazizu AAJ*✍ Da *Neeratlu...
-
❣❣ ❣ *MAYA! ππ»♀* ❣❣ ❣ 1⃣1⃣ Via O. H. Wπ Neeratlurv.blogspot.co.ke Wattpad @neerat_lurv *** Tafiya suke kan hanya...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ π©π» *MAYA* π©π» ❣❣ ...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*π· ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *NEERATLURV*π Da *ABDULAZIZU AAJ*✍ Via O....
-
15/3/2017 1:33pm *Muneerat*✍ *JININ JIKINA* _*111-115*_ NA *NEETATLURV*π _Based on fiction and love tale story_ _Dedicated to Aun...
-
19/2/2017 7:00am *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*π _Dedicated to Aunty Sis...
No comments:
Post a Comment