(30/1/2017 7:12am) *Muneerat*✍
*JININ JIKINA*
_based on fiction and love tale story_
NA *NEERATLURV*😍
_Dedicated to Aunty Sis_💞
®O.H.W
*51-55*
_*Here is a page of honour for u Jamila Bello (JB) am speechless this is more than love, Babe ILYSM Moon round the back.. Thanks for your support and care.*_
#one love💞
*** ***
Washegari da sassafe bayan sunyi Karin kumallo FARIS yace musu su shirya zai kaisu shopping, rawa suka hau yi suna tsalle saida ya daka musu tsawa suka nutsu kuma yakara dacewa wlh cikin 10mins idan basu shiryaba zaiyi tafiyarsa fuuuu yafice xuwa motansa yana jiransu."
'"Gudu2 sauri2, suka je daki dama da shirinsu mayafi kawai suka dauko suka d'an gyra make up na fuskarsu basuyi wani makeover Ba illah light one dasukayi, dukkansu sanye suke cikin bakaken Arabian gown sunyi rolling d'in Kansu da d'ank’walin gown d'in sunyi kyau sosai barin ma MUSKAN datake blowing wani haske kamar balarabiya."
"A mota suka samesa ya had'a giran sama data kasa bud'e motan sukayi suka shiga MUSKAN a gaba fareeda da humaira abaya, tunda suka shiga bai tanka musuba, sudai dariyane yake son gifta musu amma haka suka danne basuyiba gudun hukuncin da FARIS zai yanke musu."
"Stupid girls, kun rainani ko? eh Zan had’une da Ku ai maras kunyan yara kawai , nama yi niyan tafiya buh Dan akoi Baby boo shiyasa I can't go inba haka fitowa zakuyi Ku tarar bani ya bugawa musu wani dirty look dasuka sha jinin jikinsu, mota yaja da d'an banzan gudu yafita , basu tsaya KO inaba sai _shoprite_ na cikin garin abuja."
"Sayayya yamusu sosai na kayan sawa, kayan makeup da kayan makuleshi, daga nan yawuce dasu ice cream shop ya saimu su ."
"Park ya wuce dasu shan iska, acan suka keb’e da Baby boo d'insa suka sha love sai yamma lis suka koma gida da gajiyan yawo."
"Da dare suka sha hirannsu yadda suka Saba."
*** *** ***
_*2days later*_
Kamar yadda Dad yafad'a toh hka akayi ya karb’i adreshin gidansu MUSKAN dake bauchi shida Dan uwansa da abokansa biyu suka isa garin bauchi,direct unguwarda MUSKAN ta basu adreshi sukaje basu wani sha wuyaba suka sami gidan nan suka aika yaro yamusu sallama da mai gidan."
"A cikin gida yaro yace Ana sallama da Baffa, kasancewar bai fita aikiba yasa yaje har kofan gidan, KO da zuwansa yaga manyan mutane nan ya musu iso har cikin gida , a babban falon gidan ya ajiyesu aka kawo musu drinks da snacks."
"Bayan sunci sunsha nan suka sanar dashi meye ke tafiya dasu sun zo nemarwa dansu ne auren MUSKAN kuma itama MUSKAN din na awajensu.".
"Bud'an bakin Baffa yace sai mai intana wajenku, ai ni tuni na tsameta daga jinin na tunda yarinya yawon dandi taje ni Ba ubanta bane kuma Ba hadina da ita."
"Ta inda yake shiga bata nan yake fitaba matsifa sosai yayiwa su Dad ya koresu kuma har da cewa daga rana ita yau karsu sake zuwar masa da maganar shegiyan yarinya nan."
'"Jiki a sanyaye su Dad suka bar garin bauchi , tun a hanya Dad ya rinka baiwa abokansa hakuri da gayamusu abinda ya faru da MUSKAN duk sun tausayamata kuma su sun yarje kanin Dad yace shi zai wakilci a matsayin uba."
"Iya murna Dad yayi har suka karasa garin Abuja."
"Sukayanke gobe su Dad su je gidan (Usman)Dan uwansa nemar auren MUSKAN wajensa."
"Da wannan shawaran da suka yanke suka isa gida".
"Sai bayan isha misalin 8:30 suna a zazzaune a falon kasa Dad yayi gyran murya ya kwashe duk yadda sukayi da Baffa da sukaje har da abinda abokansa da Dan uwansa yafad'a, ya Kara da cewa gobe zasu je Neman aurenta wajen Dan uwansa (Usaman) insha Allah."
"Godia sosai MUSKAN tayiwa Dad, har Baba Usman akakira Mata suka gaisa ta masa godia hira sukayi dashi sosai kamar ta mahaifi da 'da."
"Baffa kam ko vayan tafiyarsu
Dad yashiga wajen matarsa yasanar da ita suwaye Dad da abinda yake tafe da su itama ta hau sababi wai Allah yarabasu da alakakai yanzu kuma saida suka soma cin arziki zata dawo tab ai baxai yibu nan suka ta zagi da matsifa."
_ni dai neerat nace tirr da halayensu Baffa da matarsa_
Washegari!
Su Dad sunje neman aure anvasu har sun yanke aure bayan MUSKAN tagama neco da sati daya za'ayi aure."
"Dad ya sanar dasu Mum abinda suka yanke "
"Nan aka soma shirye shirye kasancewar su MUSKAN sun Fara neco Ba kanta "
"Amma kullum suna manne a waya da FARIS wani'sain kuma suna tare a gida."
_*Faty*_
Tun bayan da sukayi magana da kawarta meemah bata sake waiwayar FARIS Ba ko a waya bata kiransa amma can cikin zuciyarta kuma ta kudura niyan da zarar malamin ya dawo zasu wajensa."
*** ***
A haka rayuwa taci gaba da gudana, MUSKAN na faman preparation na gama school da bikin candyn su wani bangare Nata kuma na shirye shiryen bikinta da FARIS."
"Haka shima FARIS yana busy yanxu Sam baida lokaci yana can yana gyran gidan da zasu zauna da baby boo duk da ko anyi auren Ba nan zasu zaunaba can London zasu sabida aikin sa kuma bazai iya zuwa can Baby boo na nan Ba shiyasa su Dad suka yarje masa kan bayan aure zasu tare can da matarsa."
_*Faty*_ sunje wajen malamin amma kash sun tarar baida lpy sosai nan suka baro gidansa suka dawo gida duk ran Faty a bace."
"Dan Ba karamin tashin hankaliba Faty ta shiga jin ansa ran auren FARIS da MUSKAN shiyasa tasa meemah a gaba sai sunje wajen malam, kuma koda sukaje sai su Ka tarar baida lpy."
"Meemah ce tayita k’wantar ma ta da rai kancewa ta barsu ai ko bayan auren sai su je inyaso su fitar da ita daga gidan, dan akoi wani hatsabibin boka a garin _Bebeji_ dake kano toh can zasu."
" da wannan shawaran Faty tasama zuciyarta ruwan sanyi, takoma shanawa."
_*sati biyu*_ ya rage auren MUSKAN yanxu ta gama neco har sunyi candy aurenta kawai take jira."
"Mum ta tafi Dubai hado kayan lefe da kayan kitchen da furniture's."
#Team JJ💞
© *NEERATLURV*😍
New Post
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Popular Posts
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO* 🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ Na *Abdul azizu AAJ* ✍ ...
-
11/2/2017 6:55pm *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis_...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ❣ ...
-
❣❣ ❣ MAYA! ❣❣ ❣ Via OHW📚 Neeratlurv.blogspot.com Wattpad@neerat_lurv 36_37 ***Sati daya da auren Ba abinda ya canza ku...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *Abdulazizu AAJ*✍ Da *Neeratlu...
-
❣❣ ❣ *MAYA! 🙍🏻♀* ❣❣ ❣ 1⃣1⃣ Via O. H. W📚 Neeratlurv.blogspot.co.ke Wattpad @neerat_lurv *** Tafiya suke kan hanya...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *NEERATLURV*😍 Da *ABDULAZIZU AAJ*✍ Via O....
-
15/3/2017 1:33pm *Muneerat*✍ *JININ JIKINA* _*111-115*_ NA *NEETATLURV*😍 _Based on fiction and love tale story_ _Dedicated to Aun...
-
19/2/2017 7:00am *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis...
No comments:
Post a Comment