New Post

Friday, 17 March 2017

SHAUKIN SO

✨✨✨✨✨✨✨✨✨
    ❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
      ✨✨✨
        ✨✨
          ✨

NA

*NEERATLURV*😍
        Da
*ABDULAZIZU AAJ*✍

Via O.H.W📚

             *46-50*
     
         _*Last page*_

   ****                ****

Bayan ya bar kofar gidan sai kuma ya sake runtse idanuwansa domin nazarin inda zai sake zuwa don ganin Mama, bayan wani dan lokaci ya bude idanuwansa ya doshi cikin wani babban daji, don nan zuciyarsa tabasa masoyiyarsa Mama tana nan.”
Yayi tafiya mai nisa acikin daji gashi yunwa da kishirwa na damunsa amma bai hangi kowa ba acikin jinsin mutane ballai ya nemi taimakon koda ruwan sha ne. Can yana tafiya yakara yin nisa sosai cikin daji sai ya hango wasu mafarauta sun zagaye wata yarinya, tun yana nesa ya hango su, bai tsaya bata lokaci ba ya karasa inda suke, yana zuwa koda ya kalli yarinyar dake tsakiyar sai yaga Mama dinsa ce, cikin karfin hali yayi sauri ya tsallaka tsakiyarsu ya isa wurin masoyiyarsa, Mama na ganinsa tayi wata irin murna wacce ta jima bata yi irinta ba, sai daya daga cikin,mafarautan yace “kai wanene kai da zaka shigo tsakiyar mu muna kan aiki” Abdul bai samu damar mayar masa amsar tambayarsa ba saboda tunda ya fado tsakiyarsu kallon Mama kawai yake har ya manta da akwai wasu akusa dasu.”

 “Cikin yana yin fushi dayan Mafarautan yakai masa duka wanda yayi sanadiyar faduwar Abdul kasa, Abdul yana kasa ya dubesu cikin mamaki yace “ku kuwa su waye da kuka zagaye masoyita, me kuke so” sai suka amsa masa da cewa “ita muke so mu tafi da ita” cikin dariya Abdul ya tashi ya kakkabe jikinsa yace “au daman akwai wanda duniya zai iya daukar masoyiyata daga gareni, daman akwai wanda zai iya tabin jikin masoyiyata agabana, wallahi duk wanda yayi yunkurin tabin masoyiyata sai yayi nadama, abu mafi sauki ku tafi kawai kubarmu da abinda ya ishe mu” sai Babbansu yace “Lallai yaron nan ka raina mu, to bara ka gani” sai yaje da niyar rike hannun Mama, da hanzari Abdul yazo wurinsa yakai masa naushi wanda yakaisa kasa, sai saura suka farma Abdul daganan suka cigaba da fafatawa, cikin ikon Allah Abdul ya samu damar dokesu su duka, da suka ga alamun babu riba suka ruga da gudu suka bar Abdul tareda Mama.”
Bayan sun gudu, sai Abdul ya dubi Mama yana shesshekar gajiya yace da ita “Ke kuwa me ya kawo ki wannan gungurumin daji?” sai Mama tayi murmushi tace “Ni ne da mamaki ba kai ba, ya akayi kasan ina wannan dajin?” sai Abdul yayi murmushi yace “shin kesan cewa koda yaushe zuciyoyin mu suna tare gangar jikin mu kadai ne a rabe, aduk lokacin da na runtse idanuwana nakan ganki acikinsu da kuma yanayin da kike, sannan idan ina bukatar sanin inda kike zuciyata ita take gayamin inda ‘yar uwarta take ma’ana inda kike, nakan bi dukkanin inda lumfashin zuciyata yake bugawa dan na tabbata kina wurin, kuma sai yanzu nakara tabbatar da hakan, tunda ta gayamin nazo nan kuma nazo na sameki” sai Mama tasake yin murmushi a karo na biyu, sannan tace “tun lokacin da nabaro garinku, na dawo gida amma nakasa zama, shiyasa naje wurare da dama amma duk inda na zauna aka tambayan matsalata nakan fada, amma kowa abinda yake gayamin nayi hakuri dakai, ni kuma nagaji da jin wannan mummunar kalma, shiyasa nayi nesa da mutane, dan nahuta dajin wannan mummunanr kalma, wannan wurin da nake yana debemin kewa saboda soyayyarka ita kadai ce abar hirata, tunaninka kuwa shi ne abinci na, nazarin kalamanka su suke debemin kewa” sai yayi murmushi yace “to albishirin?” “Goro” Mama ce amsa haka tana cike da fara’a, sai Abdul yaci gaba da cewa “Mahaifinki ya amince da auren mu, shi ne ma yabani damar nemoki, dan haka mu hanzarta mu koma gida” Mama tana murna ta dauko mayafinta ta daurewa Abdul rauninda mafarautan nan suka yi masa abaya, suka kama hanyar zuwa gida.”
Bayan doguwar tafiyar da suka yi acikin daji har suka iso gida, suna zuwa Kawunta ya gansu ya kuma yi murna sosai tareda jinjinawa Abdul, sai kuma matarsa ta dauko mayafi ta baiwa Mama, sannan Kawu ya shiryo dan biyo su Mama gida tare. Sun je tashar mota sun shiga motar zuwa Kano cikin sa’a basu jima ba mota ta cika suka kama hanyar Kano."

”Bayan sun iso Kano suka zo gida, suna isa cikin gida mahaifin Mama ya tarbesu cikin fara’a, mahaifiyarta ta rugo ta rungume Mama, sai Mahaifin Mama ya dubi Abdul sannan ya dubi kanensa, sai ya cewa Abdul “Mun gode sosai Abdul Allah ya biyaka kuma naso na baka auren Mama amma kuma sai gashi wata kaddara ta gifta?” cikin tsananin mamaki Mama ta saki mahaifiyarta ta dubi babanta tace “Baba wace irin kaddara kuma” sai ya kalleta yace “Kin fi kowa sanin bama baiwa duk wanda yaji rauni a bayansa auren ‘ya’yan mu kuma gashi Abdul yaji rauni agurin” Mama tana kuka tace “Baba wannan  al’ada ai ba daga wurin Allah ta fito ba, sannan katuna awurin cetona ya samu wannan rauni” Abdul na tsaye sai jiri yake ya kasa cewa komai saboda tsananin mamaki, sai Mahaifinta yace “Nadai gaya miki” Mama bata kara cewa komai ba, taje ta nemo wuka ta yanka a bayanta, cikin Firgita Babanta yace “Mama miye haka, kin yi haukane kike yankawa kanki wuka” Mama na hawaye tace “Baba a wannan lokaci wallahi zan iya aikata abinda  mahaukaci bazai aikata ba, na yankawa kaina wuka abaya ne saboda nima nayi irin raunin da Abdul yayi, idan kuma hakan baisa kuka amince da auren mu ba, wallahi saina kashe kaina” a lokacin Kawunta yace “Yaya kawai ka amince da aurensu in har ba so kake muyi hasararta gaba daya ba, na tabbata a yadda take ji a zuciyarta zata aikata abinda tace” sai kuma Abdul yace “Mama kada ki aikata hakan, ki bi umarnin iyayenki mu hakura da juna indai basa son auren mu” sai Mama tace “Wallahi bazan iya hakuri da kai ba koda kai zaka iya hakuri dani, kuma yanzu zan aikata abinda nace”.
Sai Mahaifinta yayi sauri yace “Mama ajiye wukar na amince ki auri Abdul, kada ki aikata wannan mummunan zunubi, bazan yi sanadin fadawar ‘yata cikin wutar jahannama ba, na amince” sai Mama tace “sai kayimin alkawari sannan zan ajiye” sai mahaifiyarta tace “Ki ajiye Mama basai yayi miki alkawari ba, nasan ya amince har azuciyarsa” sai Babanta yace “Nayi miki alkawari na amince da aurenku” sai Mama ta ajiye wukar ta rungume Mahaifiyarta.”
  “Bayan amincewar Mahaifin Mama, sai kuma ya umarci Abdul suje dashi da Mamar da kuma kanensa, dan ya baiwa mahaifinsa hakurin abinda ya aikata musu, tareda rokonsa shima ya amince.
Sun shigo mota su hudu sun hawo hanyar Bauchi, Abdul da Mama murna kawai suke a zuciyarsu amma sai suka boye basu bayyana a fuskarsu ba, amma kuma da kagansu kasan akwai farin ciki atattare dasu.”
  “Allah ya kawo su garin Bauchi
lafiya, sannan suka je gidansu Abdul, inda suka tarar da mahaifin Abdul yana batun fita, da sauri Abdul yaje ya durkusa gaban mahaifinsa yana kuka yace “Dan Allah Abba ka gafartamin laifina dana aikata muku wallahi banida zabi akan hakan ne” sai kuma yaje gaban Mamarsa yace “Hajiya dan Allah ku gafartamin” yana cikin kukan ne Hajiya ta riko hannunsa ta tasuwa shi tsaye batare da tace komai ba, itama ta dinga zubar da hawaye. Sai kuma mahaifin Mama yazo wurin Alhaji yace “Alhaji kayi hakurin abinda muka aikata, cikin rashin sani ne da sharrin shaidan, mun dade muna kyamar aurar da ‘ya’yan mu ga Hausawa, sai yanzu ‘ya’yan mu suka fahimtar damu wani abu wanda muka dade bamu fahimta ba, ashe shi SO babu ruwansa da Yare, sannan Allah yakan hada kauna tsakanin duk wadan da yaso, dan haka ina mai nemanka gafara ka yafemin abinda na aikata maka, na amince kuma inason kaima ka amince, ta yuyu ta wannan hanyarce zamu samu magance nuna banbancin Yare, sannan mu sakawa wadannan yara albarka shi ne alkhairi agaremu bamu yi kokarin rabasu ba” sai Alhaji ya dubi Mahaifin Mama yace “Babu komai, komai ya wuce Allah yakara ganar damu, a baya harna yanke shawarar ko ka amince ni bazan amince ba, amma yanzu ba abinda zance bayan Allah yasa ayi damu, sannan Allah ya albarkaci aurensu” sai kowa dake wurin yayi murna, musamman su Abdul da Mama.”

“Soyayyar Abdul da Mama ta dawo cikin farin ciki da jin dadi batare da wani shamaki ko fargaba ba, daman ita rayuwa mai hakuri yake da nasara, sannan kuma soyayya abu ce mai daraja wacce take da wuyar samu cikin sauki, haka zalika duk tsanani sauki yana nan zuwa. Yanzu gashi iyayensu sun amince da auren su wanda basu yi tsammanin samun wannan nasarar ba a baya, amma da yake komai na Allah ne gashi yanzu sun cimma nasara.”
    “An saka ranar auren Mama da Abdul an yi komai da ake na aure kamar su, Lefe kudin Sadaki komai anyi har an saka rana.
Ranar Aure anyi biki cikin farin ciki da jin dadi, sannan an yi shi abin burgewa, an je Kano an daura auren Abdul da Mama,.”

“Da daddare abokan Ango su Usman da Bashir da Ibrahim da Mansur da dai sauransu sun kai abokinsu Ango wato Abdul dakin Amaryarsa wacce aka kawo masa tun sallar Isha’I da yake ba gari daya bane wato Mama. Sun yiwa Ango da Amarya huduba harma da zolayar da abokan Ango suke idan sun kawo Ango duk anyi suka tafi suka bar Ango da Amarya acikin daki su kadai.”

“Sun je sun yi Sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, sun zo sun zauna suka fara hirarsu, acikin hirar Mama ta kalli Angonta Abdul tace “Angona ashe daman zamu ga wannan rana a rayuwarmu?” cikin murmushi Abdul yace “Amaryata kenan, aini daman ban taba cire tsammanin ganin wannan ranar ba, saboda bana tunanin akwai wanda zai iya rabamu a duniyar nan in ba Allah ba” sai Mama ta lumshe ido cikin shagabawa tace “Hmm kaida kace ka yafe ni” “Wa! Hmm ai kawai fada ne nayi a baki amma ba haka bane a zuciyata ba, ya za’ayi na yafe wacce na sallamawa dukkanin lamarina, wacce kullum mafarkina itace, wacce zuciyata batasan kowa ba sai ita, ai ni dake babu mai rabamu” Abdul ne yace haka, sai Mama tace “to Allah yabarmu tare, sannan ya albarkaci rayuwarmu ya bamu zuri’a dayyiba” sai yace “Amin Amaryata shalelena” sai suka tashi domin kwanciya, a Daren ranar Abdul ya karbi hakkinsa wajen Mama Tasha wuya hannun Abdul shikuma sai faman zubamata Rowan, albarka yake, ya gasamata jiki bayan sunyi wanka suka haye gado rungume da juna haka bacci ya debesu.”

“Rayuwar auren Abdul da Mama ta kasance cikin farin ciki da jin dadi, don kuwa babu wanda ya taba jin kansu, shima kuma Usman ya samu wurin cin abinci koda yaushe, dan kullum acan yake zuwa yana kwasar girki ya huta da karbar bashin garin kwaki.

  "BAYAN WATA HUDU"
   “bayan wata hudu Allah ya azirtasu da samin ciki sosai sukayi murna kula na mussamman Mama ke samun wajen mijinta da dangi.”
."Ciki Nada 9mnth ta haiho yan biyu duka maza, basai mun tsaya fadamuku farincikin da zasuyiba just imagine readers."
  "Ranar suna yara suka ci sunansu Anwar da a
Ammar, anyi shagali har mun hangosu xarah bukar, Yar Ficika, walliya,Maryam G,Anker, Belly badaru, asy Khallel,RAZ,da sauransu sunata kwasan rengem, bamubar su Mr smile, ililee, raheem jegs anyi shagali lpy an watse."
   “haka rayuwa taci gaba da tfy cikin jin dadi dakwanciyar hankali,yara suna girma suna kyau da wayo, Abdul yasami Karin girma a wajen aiki komai yana tafiya dadai ALHAMDULILLAH..... Muna wa Abdul da Mama fatan alheri a rayuwarsu Allah yasa mu dace ameen....
TAMMAT BI HAMDILLAHI….


JINJINA GAREKU MARUBUTANMU
AneeLurv..
Kausar luv..
Waliya wally ce.
Seemaluv.
Futhalurv.
Amrah pinky Durling
Rabe'atu SK mash
Zarah b~b
Sdy Jegal..
Aneesa didi.
Fedoo Yar Ficika.
Miemie bee.
Billylosh.
Melody..
Asy Khalil.
Beelybadaru.
Bilkin Abdul.
Maryam G.
Pherty.
Ummi Aisha
Maryam Yar Mama.
Ayusha iliasu.
Herwerh Jiddah.
Dija waziri.
Jidda Mowajoo.
Mjay.
Mummy sultan.
Mummy ihsan.
Mummy twins.
Nafee anker.
Ayusha Muh'd.
Sadnaf
Mr smile.
Ililee.
Raheem jega.
Sa'ed bebeji.
Da sauran da bamu ambataba kuna ranmu (Allah ya hada kanmu baki daya Ameen).

GODIYA GA KUNGIYOYIMU
Online Hausa writers O.H.W
Perfect Hausa writers P.H.W
      Groups dinmu kuna ranmu
AneeLurv Novels.
Sadnaf Novels.
Mjay novels.
House of novella.
Cute xarah bukar novels.
Dandalin feedo Yar Ficika.
Dandalin Billylosh..
  Da sauran waenda bamu ambataba. Muna godiya da kaunarku garemu.

  ~Sadaukarwa gareki Maryam (Mama) wannan littafin naki ne~

_*Anan Ni MUNEERAT (Neeratlurv) tare da Dan uwana ABDULAZIZU AAJ (Na England/Gwarzon naja'atu) muke muku fatan alheri kuma anan muka kawo karshen littafin mai tattaken SHAUKIN SO sai kuma mun sake haduwa awani littafin da yardar Allah*_.

ABDULAZIZU
         ⬇
07068636566

NEERATLURV
        ⬇
08088771486

©copyright@2017 Febuary..

_*Love You All Our fans*_❤❤❤

No comments:

Post a Comment

Popular Posts