New Post

Friday, 17 March 2017

SHAUKIN SO

✨✨✨✨✨✨✨✨✨
       ❤ *SHAUKIN SO* 🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨
Na
*Abdul azizu AAJ* ✍
              da
*NeeratLurv* 😍

Via O.H.W📚


_*Bismillahir Rahmaniir Raheem*_

_*Dukkan Yabo ya tabba ga Allah SWT, ina rokon Allah'n da bamu ikon Fara wannan littafin ya bamu ikon karasawa, Allah yasa mufara littafin nan Sa'a, Yakuma bamu ikon Isar da sakon da ke ciki AMEEN*_


~ _*wannan littafin bamu yisa dan cin zarafin wata/wani ba idan labarin yazo daya Dana wata kowani toh yayi hakuri akasi akasamu*_


~ _*Godia gareku masoyanmu aduk inda kuke a fadin duniya we love u so much*_#onelove..

_*muna mika gaisuws ga kungiyoyin mu kamar su*_

1-Online Hausa writerz(OHW).
2-Perfect Hausa writerz (PHW)
 Da sauran waenda bamu ambataba kuna ranmu...

       *1-5*

Saurayine dan kimanin shekara 30yrs yake Jan mota kirar Accord 2016, cikin kwanciyan hankali yake tuki cikin motan kuma wani kidine mai sanyi yake tashi wakar Jennifer Lopez _what is love_ shi yake tashi, shikuma sai faman kada Kai yake alamar yana jin dadin wakar".
  "Parking yaja a daidai harabar _Sahad_ dake garin kano, sanye yake cikin  fariin yadi Wanda yasha aiki kana ganin kayan zaka San mai tsadane, kafarsa kuma wata takalmi mai kyaun gaske shima fari, hannun sa daure yake da agogon axurfa kirar campanyn Rolex,yasha kyau iya kyau fuskansa dauke da murmushi ya shige super market din."

" yana shiga ya fara binciken abinda zai saya, yana cikin duba kaya ya ga wata Yarinya kyakkyawa ya kalleta sama da kasa amma bai ce mata komai ba, ya ci gaba da sayayyarsa har ya kammala ya zo aka yi masa total din kayan ya biya ya fita, yana zuwa wurin motarsa ya bude bayan boot ya saka kayan da ya siyo, sannan ya dawo gaban motarsa yayi tsaye yana jiran wannan yarinya ta fito."

"Bai fi minti bakwai ba, sai ga yarinyar ta fito tare da sayayyarta ta tsaya bakin titi tana jiran mai taxi domin ya dauketa, yayi sauri ya shiga motarsa ya je ya faka kusa ga yarinyar ba tare da ya fito ba, ya sauke glass din motarsa tare da cewa “Assalamu alaiki ‘yan mata” sai ta amsa masa “Wa’alaikas salam” ya ci gaba da cewa “’yan mata ina zaki, kuma naga kamar kina jiran taxi ko?” tace “eh taxi nake jira” sai yace “to gani nima direbane kuma biyana ake sai ki shigo muje ko?” sai tace “a’a nagode” sai yayi dariya yace “aini ba godiya nake so ba, dan biyana zakiyi, in kai ki inda kike so sai ki biyani, ke ga ko ai baidace kiyimin godiya ba, ki shigo muje” tace “ni ba irin wannan mota nake son  shiga ba, taxi nake bukata dan haka kaje kawai wallahi nagode” sai yace “karki yimin haka dan Allah! Ai ci gaba ne nasamu shiyasa kika ganni ina yin taxi da wannan mota, amma can asali ‘yar taxi ce gareni, ki shigo kawai muje dan Allah karki yimin walakanci, ai duk dayane dani da dan Taxi, bai dace ace kamarki kina tsaye a titi ba rana tana dukanki” da kyar ya samu ya shawo kanta, sai ya fito ya kwashi kayanta ya saka Mota, sannan ya dawo ya bude mata kofar mota ta shiga ya rufe ya dawo ya shiga suka tafi."

 " Suna cikin tafiya kowa bai cewa wani uffan ba, sai tafiya suke can sai ya dubeta yana murmushi yace “au nayi mantuwa ban tambayeki inda muka dosa ba, sai faman tafiya nake”.

"Murmushi tayi kan  tace “Borno avenue zaka kaini” yace “ok” daga nan bai sake cemata komai ba har suka kai kofar gidan ya fito ya dauko mata kayanta, ta dauko kudi zata bashi sai yayi dariya yace “ai bada wannan zaki biyani ba” sai tace “to dame zan biyaka?.”

" sai yayi murmushi yace “bazan gayamiki ba yanzu, amma kibani lambar wayarki dan idan natashi karba sai nakira ki, sannan kifadamin sunanki dan nayi saving dashi”.

" sai tayi murmushi mai alamar mamaki tace “hmm lamba kuma me zakayi da ita?”.

" sai yace “ai nariga na gayamiki abinda zanyi da ita, zata yimin amfani duk ranar da natashi karbar bashina agurinki zan kira ki na sanarda ke, kuma inason nasan sunanki dan nayi saving”.

"Tana murmushi a ranta kuma tana mamakinsa irin yadda yamaidata yarinya kawai sai tabashi lambar wayarta sannan tace “Suna kuma ka saka wacce kake biya bashi”.

"Da sauri yace “a’a gwara dai ki gayamin sunanki dan baki sani ba  ko wadan da nake biya bashin suna da yawa”.
  "sai tace “hmm idan suna da yawa sai ka sakamin sunan da zaka iya gane ni” sai yace “duk da haka zan so naji sunanki domin saka sunan yafi muhimmanci”.

 "Cikin sanyin muryanta  tace “nima sunana na sayarwa ne” yayi murmushi yace “tow, amma duk da haka bai kai tsadar driving din da nayi miki ba, dan haka sai ki cire daga ciki, in yaso sauran na biyoki” tace “ai sunana ya zarce kudin driving din da kayimin ba” sai yace “ke dai tsadar naki kika sani, dan haka ki gayamin idan nakira ki zamu warware” ta dan ja aji, sannan tace “sunana Maryama amma ana kirana da Mama”.

"Dan guntun murmushi yayi tare da cewa “sweet name, ni kuma sunana Abdallah amma ana kirana da Abdul.’’
"Murmushi tayi tace kaima sunanka mai dadi ”.
" sai tayi masa bankwana tace zata shige cikin gida."

" shi ma bankwana hade  kuma da shige wa motarsa cikin farin ciki ya ja motan sa zuwa gida.....



 *NEERATLURV*😍
         &
*ABDUL AZIZU AAJ*✍
 (Na England)..

 _Dedicated to Maryam (mama)_❣

1 comment:

Popular Posts