✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
NA
*ABDULAZIZU AAJ*✍
Da
*NEERATLURV*😍
Via O.H.W📚
*31-35*
_*BAYAN WASU KWANAKI*_
“Mama ce ta shigo cikin gidansu Abdul tana zubar da hawaye, tana shigowa ta tarar da Mahaifin Abdul zai fita, sai ta durkusa agabansa tana kuka, ta dubesa tace.
“Abba dan Allah ku taimaki rayuwarmu wallahi bazan iya rayuwa babu abdul ba, idan kuka rabamu hakan zai sanadiyar halakarmu, ka tausaya muna”.
“cikin yanayin fushi Mahaifin Abdul ya dubi Mama yace “Wai ke bazaki ji maganar iyayenki bane, tunda har suka nemi su walakanta mu, ba zamu yarda da wani zancen auren ku ba, mu Hausawa bamu ce D’an mu bazai auri Fakanci ba, amma su zasu ce ba zasu aurar da ‘yarsu ga hausawa ba, dan haka ki tashi kibar gidan nan”
“ sai Mama tace “Abba kayi hakuri da duk abinda suka gayamuku, wallahi acikin rashin sani ne, basu san irin wahalar da zuciya take ba, aduk lokacin da ta rasa abinda take so, ni zan zauna tare daku, bazan iya komawa gida ba.”
“Kibar gidan nan nace tun kafin raina ya sake baci” Mahaifin Abdul ne ya fadi haka cikin fushi.
“Abdul na daki kwance ya jiyo muryar masoyiyarsa Mama, da hanzari ya fito ya tarar da Mahaifinsa yana korarta, sai yayi sauri yaci gaban Mama, sannan yazo inda Mahaifinsa yake ya durkusa tareda Mama, ya kalli mahaifinsa yace “Abba ka dubi irin halin da wannan yarinya take ciki, ka dubi irin halin da na shiga a lokacin da kazo ka gayamin iyayenta sun ce ba zasu bani aurenta ba, ka dubi irin azabar da zukatan mu suke ciki na rashin amincewarku. Dan Allah ku daina zancen Yare atsakanin soyayyarmu, wallahi ina sonta kuma bana tunanin zan iya sake son wata bayan ita, dan Allah Abba kabarta ta zauna anan har lokacin da iyayenta suka gane kuskurensu suka amince da auren mu” sai Mahaifinsa yace “idan kai bakada hankali to ni inada, sannan yanzu koda iyayenta sun amince da aurenku to ni bazan amince ba, kuma babu kai babu ita, idan kuma kace sai ita zaka aura to sai dai ka sake wani uban amma bani ba” sai kuma ya dubi Mama yace “ke kuma kibar gidan nan nace tun kafin ki fuskanci walakancin da baki yi zato ba” sai Mama ta tashi tsaye da nufin fita daga cikin gidan, amma kafin ta fita sai ta dubi Abdul tana Kuka tace “Abdul Duka ko Zagi basa fitar da sonka daga cikin zuciyata koda a bangarenka ne ballai bangaren iyayenka, dan haka zan tafi amma kasani tafiyata bata nufin rabuwarmu dakai ba, dan kuwa nasan rabuwarmu dakai abu ne wanda bazai taba yuyuwa ba har abada, sannan wannan korar da iyayenka suka yimin bazan ga laifinsu ba, kuma bazan tafi da haushin su ba, na dauki wannan abin kawai yana daga cikin kaddarar rayuwata” sai kawai ta juya ta tafi........
"Bayan ta fita Abdul ya dubi Mahaifinsa, sannan ya dubi Ummarsa dake gefe tana kallonsa cikin yanayin tausayi, bai cewa kowa uffan ba ya shige daki. Mahaifin Abdul ya dubi Mahaifiyar Abdul yace “Hajiya kada ki yarda yaron nan ya fita daga cikin gidan nan, dan nasan idan ya fita zai iya bin bayanta su tafi tare” sai Hajiya kada kai tace “to Alhaji insha Allahu zan kiyaye” sai Alhaji ya fita cikin gidan fusace.
***BAYAN SATI DAYA***
Alhaji ya fito firgice daga cikin dakin Abdul inda ya tarar da Hajiya tana shirin shiga dakinta, cikin kakkaurar Murya yace da ita “Hajiya shin ina Abdul ya shiga kwana biyu bana jin motsinsa, yanzu kuma na shiga dakinsa ban gansa ba?” sai Hajiya tace “wallahi Alhaji bansani ba, dan ni nayi zaton yana nan, kasan tun lokacin da abin nan ya faru Abdul ya daina fitowa waje ko abinci daina ci yayi, amma yana yuyuwa ya tafi wurin abokansa ne” sai Alhaji yace “Amma idan yaron nan guduwa ne yayi tabbas saina bata masa rai, ni zai rainawa da wayo, nace kada ya fita amma ya fita” Batare da Alhaji ya sake cewa wani abu ba, sai ya shige cikin dakinsa, itama Hajiya takarasa shigewa dakinta.
“Abdu ne acikin wani karamin Daki wanda da kagansa kasan dakin gaye ne, ko gayen wanda bayada ko sisi. Abdul na cikin dakin abokinsa mai suna Usman a kwance, sai ga Usman ya shigo cikin dakin yana tsaki, batare da yayi sallama ba ya je ya samu wuri ya zauna yaci gaba da tsaki, cikin yanayin mamaki Abdul ya taso zaune ya dubi abokinsa Usman yace “Wai abokina me yake damunka ne kake ta wannan tsakin haka?” sai Usman ya juyo da hankalinsa wurin Abdul yace “Wallahi Madam din nan ce ‘yar rainin wayo naje wurinta karbar bashin Garin Kwaki Naira Ashirin amma taki bani, kuma abin haushi agaban jama’a take fadan wai ina cin bashinta kullum amma bana biya”
Sai Usman ya nunfasa sannan yaci gaba da cewa “Allah Abokina in badan jama’a na kusa ba, dana mammake ta, abinda ya hanani aikata haka kuma ina tsoron nayi mata rauni narasa wanda zai bani bashi gobe” sai Abdul yayi dariya yace “To kai in banda abinka me zai sa kayi fushi da wanda ke taimakama yana baka bashi, ai dole kayi hakuri kabita a hankali” sai Usman yace “Yauwa abokina akwai Hamsin awurinka?” Abdul yace “Wallahi yau kwana biyar kenan ba kudi a aljihuna” sai Usman yayi tsaki yace “Ai kaji tsiyar, inama gudun haka amma baka gani, yanzu gashi awurinka an rasa Hamsin kaida kullum ‘Yan Dubu-dubu bugun Abuja ake gani a aljihunka, amma yau gashi ko Hamsin bakada. Na gayama ka koma gida ka hakura da wannan yarinya, sai kace ita kadai ce Macce a duniya, duk matan nan da suke duniyar nan karasa wacce zaka so sai ‘yar wani gari kuma wacce ma ba bahausa ba” sai Baffa yayi murmushi yace “daman ina jiran zuwanka dan muyi wata magana” sai Usman ya gyara zama yace “Yauwa Aboki ai daman nasan idan Talauci ya isheka zaka koma gida kadaina zancen yarinyar nan, dan yanzu wa yake ta soyayya ana ta Kudi” sai Abdul ya sake wani guntun murmushi a karo na biyu, sannan yace “Abokina ba wannan bane, kadai ga irin halin da nake ciki, kullum kunci baya fita daga zuciyata, so nake ka taimake ni ka rakani garin masoyiyata Mama, ko zan samu sukuni a zuciyata” “Wa! Ni zan raka ka, tab gaskiya banyi mafarkin na mutu ba, mu je gari bamuda kowa acan, sannan bamu da kudi, ka dubi yadda suka yiwa iyayenku da suka je ballai mu kananan alhaki, wallahi abokina nikam ina tsoron zuwa” Usman ne ya fadi haka yana zare idanu, sai Abdul yace “to miye kake tsoro da mutuwa, wallahi koda zasu kasheni ne sai naje, bazan hakurin rashin ganin Mama ba tsawon kwanaki, wai me yasa mutane basa fahimtar wanda ya fada tarkon soyayya, me yasa mutane suke tunanin cire so acikin zuciya haka yake da sauki kamar yadda ake cire sutura daga jiki, me yasa mutane suke tunanin masoyi zai iya hango wani wanda yafi masoyinsa bayan zuciya ta riga ta makantar da idanuwa daga hango kyawon wani wanda ba masoyinta ba, sannan ta toshe dukanin kofofin jin dadin sautin wani wanda ba masoyinta ba, Usman wallahi duk wanda yake cewa nabar Mama naso wata ji nake tamkar yana sambatu a barcinsa wanda bai san yana yi ba”.
Sai ya tashi tsaye sannan yaci gaba da cewa “Ban damu da zuwa da kudi don yin guzuri ba indai har zan samu kudin mota, dan na tabbata idan naje can nasamu ganin Mama to na wadatu da komai, ni fa koda yaushe idan natuna Mama sai naji damuwa ta yayemin, amma kuma idan natuna bata kusa dani sai naji tamkar ana dibar naman zuciyata, zan tafi idan kai bazaka rakani ba, kuma da yardar Allah zanyi nasara” sai Usman yayi ajiyar zuciya yace “Abokina shin ya akayi kayi nisa acikin soyayyar wannan yarinya kuma me yasa bazaka iya cireta a zuciyarka ba dan kasamu salama a rayuwarka tunda iyayenta sun ce bazasu baka aurenta ba” sai Abdul yayi murmushi yace “Wai abokina kai kuwa me yasa bazaka daina wannan sambatun ba, wa ya gayama Son Mama shiga zuciyata yayi, ai soyayyar Mama itace Zuciyar tawa gaba daya, sannan yanzu babu wata kofa a zuciyata ta karbar wata magana ko shawara ballai nace na tsaya nayi nazarin shawarar da kabani, sannan kwakwalta bata daukar zancen kowa a yanzu don ganin take ba dai dai bane, zancen Mama kawai take dauka dan shi ne dai-dai, kunnuwana kuwa basa tantance kowane irin yare mutum yake fada ballai su fahimci abinda ya fada, in ba maganar Mama ba, idanuwana kuma basa gane kalar kowa a yanzu ballai nagane muhimmancin mutum awurina in ba Mama ba, dan haka kayi hakuri da wannan sambatun naka saina dawo” sai Abdul ya fita, bayan ya fita Usman ya rinka kada kai yana magana shi kadai yana cewa “Lallai wannan yarinya ta mallake Abokina wannan So haka tab Allah ya kyauta” sai kuma Usman ya dawo tunanin yadda za’ayi ya samu kudin sayen garin Kwaki.”
“Hajiya ce ta isko Mahaifin Abdul zaune a dakinsa, itama tasamu wuri ta zauna, sai ta dubi Alhaji tace “Alhaji tsawon kwana biyar fa Abdul baya gidan nan, me zai hana aje anemo inda yake koda hankalin mu zai kwanta?” cikin fushi Alhaji ya dubeta yace “kwanciyar hankali kuma, ai sai in kece hankalinki yake atashe, ni kam hankalina akwance yake kuma ba inda zan je nemansa tunda ba karamin yaro bane, yaje duk gidan uwarda zashi, ai dai bayada wasu uwayen bayan mu, dan haka ki kwantar da hankalin ki duk inda yaje shi ne mai dawowa” sai Hajiya tace “Amma….” “Amma me?, ki canza zance idan zaki canza na gayamiki kidaina zancen aje anemo shi, shi da kansa zai dawo ya iske mu” Alhaji ne ya katsewa Hajiya magana ya fada mata haka. Sai Hajiya tayi tagumi batare da ta sake cewa komai ba.
Daga alkalamin:-
*NEERATLURV*😍
&
*ABDULAZIZU AAJ*✍
(Na England..)
_Dedicated to Maryam (Mama)_❣
New Post
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Popular Posts
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO* 🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ Na *Abdul azizu AAJ* ✍ ...
-
11/2/2017 6:55pm *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis_...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ❣ ...
-
❣❣ ❣ MAYA! ❣❣ ❣ Via OHW📚 Neeratlurv.blogspot.com Wattpad@neerat_lurv 36_37 ***Sati daya da auren Ba abinda ya canza ku...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *Abdulazizu AAJ*✍ Da *Neeratlu...
-
❣❣ ❣ *MAYA! 🙍🏻♀* ❣❣ ❣ 1⃣1⃣ Via O. H. W📚 Neeratlurv.blogspot.co.ke Wattpad @neerat_lurv *** Tafiya suke kan hanya...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *NEERATLURV*😍 Da *ABDULAZIZU AAJ*✍ Via O....
-
15/3/2017 1:33pm *Muneerat*✍ *JININ JIKINA* _*111-115*_ NA *NEETATLURV*😍 _Based on fiction and love tale story_ _Dedicated to Aun...
-
19/2/2017 7:00am *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis...
No comments:
Post a Comment