New Post

Tuesday, 14 March 2017

JININ JIKINA

{17/1/2017 11:28AM} *Muneerat*✍


      *JININ JIKINA*

_Based on fiction and love tale story_


*NA*  NEERATLURV😍

_Dedicated to Aunty Sis_💞

        ® O.H.W

         *36-40*

__________
______

 _*Cigaban labari*_

   Washegari

Da safe misalin 8:00am na safe MUSKAN ce  gaban mirror tana shiryawa cikin uniform kasancewar yau suna da papern biology, humaira ma ta fito wanka tana tsane ruwan jikinta ,fareeda CE ta shigo dakin tana murmushi tace yawwa MUSKAN nake jira ki tashi , lpy yadai MUSKAN tafada tana kokarin sa baret nata kan Dan karamin hijab na kanta, ehh lpy kawai dai ina so ki tayani anjima kanwata zaki min duk abinda nafada ai ta karasa maganan cikin fuskan tausayi, ina jinki malamata MUSKAN tafada tana hararanta cikin tsigar wasa, uhmm dama nace Ba in kuka dawo pls kidafamana Dan waken ki mai dadin nan, nasan dama aiki zakisani shiyasa kike wani yin fuskan tausayi toh ni bazan dafaba inji MUSKAN tafada tana kokarin daukan instruments na makarantan ta, fareeda tace pls mana matan big bro haba baby boo na ya FARIS wlh ke kadaice nasa Ba wata saike nan taringa kodata har tasamu tayarda kan zata dafa musu in suntaso daga paper,humaira kam banda dariya Ba abinda take yadda taga an koda MUSKAN da sunan ya FARIS ta yarda zatadafa Dan waken, nan suka fita bayan sun gama shiryawa suka bar fareeda ita kadai a daki, suna fita fareeda ta kyalkyale da dariya harda rike ciki lalle MUSKAN wlhy yanxu na ringa cin Dan wake kenan ina kodaki da sunan ya FARIS"


 Suna fita falon yana shigowa sanye yake cikin jenci mai dagon hannu da dogon wando kana ganinsa kasan ya tasone daga training kayan sun amshesa yayi kyau dukda Ba wata ado yayi va zubamasa manyan idanunta tayi fuskanta dauke da murmushi shima ita yake kallo tayi bala'in yimasa kyau duk da itama uniform ne a jikinta  shima fuskansa dauke da murmushi har ya karasa wajensu, su suka soma gaidasa ya amsa hade da cewa yan matan Mommy sai ina yanxu ya tambayesu, sai school muna da papern 9-12 yau zamu rubuta biology suka basa amsa'"

 Yace toh kuje kuyi breakfast kamin na shirya sai na kaiku, toh suka bisa da shi suka wuce dining table Dan yin break, shima daki ya nufa Dan shiryawa,"

   Cikin 30mins duk suka kammala shima har ya shirya cikin wasu kananan kaya shirt blue da jeans baki, hannunsa dauke yake da wata haddadiyar agogon na kamfanin Gucci, yatsunsa kuma suna dauke da zobunan azurfa guda uku daya a hannun hagu ,guda biyu kuma a hannunsa na dama har ya karso wajensu MUSKAN couldn't stop staring and admiring his beauty cikin zuciyarta kuwa cewa tayi gaskiya idan ta mallaki ya FARIS tagama morewa Dan yakai namiji iya namiji da duk burin mace ta mallaki irinsa tana cikin tunanin nan taji ya ja karan hancinta, shagwa6e fuska tayi tace wlhy ya FARIS da xafi fa, yace toh meye kina ta wani kallona tundazu baki ma San nazo wajenkuba kin kafeni da idanunki, bu66uga kafa ta soma kamar wata karaman yarinya cike da shagwa6a tace nifa Ba kai nake kalloba kawai kawai sai kuma tayi shiru ganin yadda ya zubamata ta idanunsa masu rikitar da ita, kwaikwayanta yayi ya marairaice fuska yace kuma meye ai baki karasaba, humaira CE tace ya FARIS Dan Allah ni Ka kaimu school tundaxu kunxo kuna ta zuba soyayya kalan Ku samu late invigilator ya hanamu paper ke kuma MUSKAN gaki lover girl kinata biyemasa ko, LA LA yarinyarnan ni kike fadawa hk tho baza a kaiba invigilator'n ya hana papern Oya wuce ki ban waje kona bugemiki baki stupid girl kawai yafada yana nuna mata kofan fita"

 Fita take tana gunguni ai gaskiya na fada kuna wani shan love bako jin kunya kuma ai laifin MUSKAN ce dake biyemasa wlhy zan hadu da ita yau, meye kike fada?yayi tambayan yana nnufota, ai Ba shiri takwasa da gudu tayi waje, shi ko ya koma yace Baby boo mu tafiko karna saki late invigilator ya hanaki paper, murmushi tayi suka jera har wajen motan cikin bakin accord 2016 ya jasu zuwa school din yana ajesu ya cire 1-1k yabasu duk suka masa godia har sunfara tafiya yace baby boo! nan ta komo yace I LOVE YOU murmushi tayi tace I LOVE YOU TOO hade da cewa Take good care of ur self yace I will insha Allah bye-bye yayimata tana dagamasa hannu har ya bace, saukan dundu taji abayanta tana juyawa taga humaira ce murmushi tayi takama hannunta tace zo muje Sis fisgewa humaira tayi tace zakice muje ai bayan kingama shan love wlhy ki kiyayeni inba haka Ba nagayawa Dad ya kori ya FARIS ya koma wajen aikinsa in yaso naga yadda zakuyi love din yar air kawai, yi hakuri Sis inji MUSKAN takama dukka kunnuwanta biyu alamara tayi hakuri, rungumeta humaira tayi tana dariya tace ai dolena na hakura matar yaya guda suna dariya har suka shiga Hall aka fara exams"

   Basu suka gama exam Ba sai wajajen 12:30 nan driver ne yazo ya daukesu ya kaisu gida, basu tarar da kowa agidanba illah mai aikin su daki suka nufa bayan sun watsa ruwa suka nemi lpyn gado nan da nan bacci ya kwashesu"

 FARIS na hango zaune da abokansa biyu wato Anwar da Aliyu suna hira sai dariya suke faman kwasa ina ganin hk ni diba a 360🏃🏃 na isa wajensu Dan dauko wa makaranta rohoto lolz!

 FARIS yace Anwar kazata bazan ga baby boo dinaba ko naga kadaukeni kamar mahaukaci kullum in namaka maganta sai dai kayitamin dariya toh wlhy yanxu danake gayamaka tana gidanmu ni nan yanuna kansa ni na kaisu school da humaira, Nan ya kwashe musu labarin MUSKAN tun randa yatafi ya barta a bauchi har kadeta da Mum tayi da zamanta agidansu har kawo xuwa randa ya hadu da ita a airport"

 Aliyu yace tab babbar magana a gaskiya na tausayamata abokina allah ya jikan iyayenta da rahma"

 "Ameen" dukkansu suka amsa a tare Anwar da FARIS"

Anwar yace abokina kasan Allah ni duk tunanina Kai kadai kake hauka akanta na zata ita tuntuni ta mance da Kai"

FARIS yace ina wlhy idan za'atara Mata duka na duniya toh MUSKAN ta dabance tana sona kamar yadda nake sonta kumafa kar Ka manta yarinyace am her first and last love insha Allah da soyayyata ta tashi kuma da soyayyata zata rayu kamar yadda nima ban taba son wata ya`mace Ba face ita kuma insha Allah ita zata kasance mace ta karshe a rayuwata nayi alkawarin sonta a raina son dan Bana wa wata irin sa sai mahaipiyata da kannena, My lyf is all depend on her lobe   I cannot do without her,she mean a lot to me, I lobe her so much"

Anwar da Aliyu dai sunsan gaskiya abokinsu ke fada Dan idan akoi waenda sukasan halin FARIS bayan iyayensa toh sai su biyunan they are childhood frnds, sun girma  atare basa boyewa dayansu damuwarsu karatunsu iri daya suka yi dukkansu pilot ne tun suna kanana inka gansu zaka dauka yan uku ne, gidajensu Ba nisa duk suna anguwa daya wato maitama dake birnin tarayya yadda suke abokai yasa iyayensu kulla abota duka matan da mazan Anwar da Aliyu suma iyayensu Nada arxiki iya gorgodo,,,, wannan kenan"

 Aliyu ne yakatsemusu tunani da fadin hey dudes lokacifa na tafiya har karfe 4:00 fa yakamata mu je gida wlhy ni yunwa nake ji"

FARIS yace ragon namiji kawai kai kullum yunwa "

Anwar yace gaskiya kafada Aliyu nima nan yunwa nake ji wlhy mu tafi gida, kuma gidan Ku zamu FARIS sai Ka nunama Baby boo din naka, koya kace"

  Baza a jeba' nifa Ba Wanda zai ganmin Mata yafada yana mikewa"

 Sai kayi amma wlh sai mun ganta, nan kowannensu ya nufa motansa ya ja fuuuu sai gida"

  MUSKAN ce dasu fareeda a kitchen suna dafa Dan wakensu ita MUSKAN na kwashemusu a ruwa sukuma sai zuba surutu suke sallamar su FARIS ne ya katse surutun da suke fareeda ta fita,tana amsa sallaman"

 Sanda zuwanku ya Anwar da ya Aliyu,,, Yawwa fareeda ya kk? Lpy qalau,, Ya karatu? Tace alhamdulillah,, Toh Masha Allah"

  Ke fareeda bamu abinci yunwa muke ji FARIS yake fadamata" ya FARIS sai dai a girka muku yanxu nan wasu sukazo wajen Dad muka juyemusu sauran abincin da ya saura"

Humaira da MUSKAN ne suka fito hannunsu dauda  da bol na danwake yasha eggs da sauran kayan hadi suka tarar da su ya FARIS gakuma fareeda dake bayani, sannunku ina wuninku duka suka fada,, lpy suka amsa, suna kokarin hawa sama zuwa daki FARIS yace kai Ku dawo meye wanann acikin bol dinnan ya tambayesu,"

 Suna karasawa sukace ya FARIS Dan wake ne fa suka fadamasa suna nuna masa cikin bol din, aiko yana hango cikin bol yasa hannu ya karbe tare da fafadin jeku kukawamanacruwan sanyi da drinks"

Ido suka zubamasa dukkansu badai ya FARIS cinye musu Dan wake zaiyiba basu ida tunaninsu sukaji yace dudes Ku sauko muci mana and Ku kuma ban aike Ku bane kun wani tsayamana a ka, TAFIYA suka soma kowa na gunguni su fareeda kam tana zuwa kitchen ta fashe da kuka wai ita ala dole ya FARIS ya cinyemata Dan wake, hk suna ji suna gani suka yi tasss da Dan waken, sai da suka sake dafa wani suka ci suma Dan cire kwad'ayi"

 Bayan sun gamane FARIS ya gabatar wa su Aliyu MUSKAN ita ma ya gabatar mata su Anwar, sun sha hira sosai har sun saba da juna a dan kankanin lokaci, sunyaba da zaben abokinsu  kuma vasu karyata shi Ba gaskiya yayi dacen Mace kamila,kunya,nitsuwa dakamun kai,sai maghriba suka bar gidan"

Nan suma suka gabatar da al'amuransu yadda suka saba aiwatarwa a kowani dare"

 'Lovers bird kam yau hira suka sha a waya kamar Ba gobe sai wajajen 11:00 na dare sukawa junansu sai da safe suka kwanta ko wannensu cike da so da kaunan juna"....

  _Nima nan zan barku na Dan huta sai mun hadu a babi nagaba_ 😉

I love y'all my fans❤


 © *NEERATLURV*😻

No comments:

Post a Comment

Popular Posts