✨✨✨✨✨✨✨✨✨
❤ *SHAUKIN SO*🌷
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
Na
*Abdulazizu AAJ*✍
Da
*Neeratlurv*😍
Via O.H.W📚
*36-40*
Baffa yaje wurin Abokinsa Bashir ya ranto kudin mota wadan da zasu kaishi garin masoyiyarsa Mama wato Garin kano, Abdul ya shiga motar zuwa Kano tun daga Bauchi ba tareda yanada kudin cin abinci ba ya kama hanya. Suna tafiya acikin mota Abdul baya cewa kowa komai har suka isa garin Kano misalin karfe Goma Sha Daya na dare.”
“Bayan an Sauke Abdul tashar mota sai yayi tsaye yana tunani, ya rasa inda zai dosa, gashi dare yayi kuma gashi bai san kowa ba agarin sai gidan kawunsa gashi sun koma bauchi saikuma gidansu Mama, shi kuma gidansu Mama koda yaje ba zai samu shiga ba dan yana tsammanin sun kulle kofarsu. Yana cikin wannan tunani ne ya yanke shawarar yaje masallaci wanda ya hango a kusa dashi dan ya kwana in yaso idan gari ya waye yaje gidansu Mama dan ya ganta, haka kuwa yayi yaje masallacin ya iske shi a rufe, sai yayi kokarin budewa, yana budewa ya tarar an kashe wutar masallacin ya sussuda dan samun inda zai kwanta, yana zaunawa kafin ya kwanta ji kawai yayi ance “Ihu ga Barawon na kama” sai kawai aka kunna wutar masallacin, Abdul yaga mutane da yawa kowannensu da sandarsa, batare da bata lokaci ba suka farmasa da duka, Sahahu yana ihu yana fadan “Wallahi ni ba barawo bane” amma basu daina dukansa ba.
Bayan sun ga Abdul ya jigata, sai wani daga cikinsu ya dubesu ya daga hannu alamun su dakata, sai yace “Mu barshi a haka kunsan Liman yace kada mu dauki hukunci da kan mu, idan kuma muka kashe shi to lallai za’a yi muna hukunci mu ma, dan haka mu daure shi har gari ya waye mu nunawa Jama’a shi” sai su duka suka ce “hakane, kuma wallahi sai ya biya duk abinda ya dauka” sai kuma suka ajiye sandunan su suka dubi abdul suka ce “Barawon banza, kullum aka ajiye kaya saika dauka, to yau dubunka ta cika daman ance rana dubu ta barawo rana daya ta mai kaya” sai suka je suka samu wani ginshikin masallaci suka daure Abdul.
“Abdul yana daure jikinsa na zubar da jini, ba abinda yake tunani face wannan yanayi daya shiga, wani bangare kuma yana tunanin halin da zai tsinci kansa gobe, amma sai yayi addu’a ga Allah dan neman sauki.
Washe gari da Asuba an kammala sallar Asuba sai wani saurayi yazo kusa ga kunnen Liman yace “Allah gafarta Malam jiya da daddare an kama Barawon nan” sai Liman ya idar da addu’arsa, sannan ya dubi saurayin yace “Jeka ina zuwa”.
Liman ya fito waje don ganin Barawon, sai ya tarar da Yara da Manya sun zagaye Abdul, yana isa gurin suka bude masa hanya ya isa kusa ga Abdul. Yana zuwa ya dubi abdul sama da kasa yaga jikinsa jina-jina da jini, sai ya dubi nakusa dashi yace “me yasa kuka yi masa wannan dukan, to idan da ace ya mutu fa?” sai saurayin dake kusa ga Liman din yace “Allah gafarta Malam, wallahi saida nace adakata da sai dai aji mummunan labari” sai Liman ya dawo da kallonsa wurin Abdul yace “Kai kuwa me yasa kake wannan mummunan dabi’a, karasa abin sata sai kayan Dakin Allah, ka kuwa san mummunan zunubin dake tattare da aikata hakan?” Abdul na shessheka ya dubi Liman yace “Wallahi ni ba Barawo bane bako ne ni, jiya jiya na sauka a garin nan, na shiga masallaci ne dan nasamu wurin kwana ba dan sata ba, sai gashi wannan kaddara tafaru dani” sai Liman yace “Ta yaya zamu tabbatar da kai ba Barawo bane?” sai Abdul yace “Ni bansan yanda zani tabbatar muku da hakan ba, amma kuyi imani da Allah da cewa ni ba Barawo bane, idan kuma kuna shakka akan zancena, to kubarwa Allah idan har ni ne mai yi muku sata kada Allah ya bani abinda nakeso sannan ya debe muku alhakinku tun anan duniya kafin lahira, wallahi Malam ni ba Barawo bane” sai Liman ya dubesa yaga idanuwansa sun yi kwalla, sai Liman ya dubi saurayin dake kusa dashi karo na biyu yace “A yadda naga siffar yaron nan bangansa da alamar Barayi ba, kuma da nayi la’akari da maganganunsa na tabbatar da hakan, ku sake sa idan ma shi ne Lahira zai biya hakkin mu” sai Saurayin ya kwance Abdul.
Bayan an kwance Abdul sai ya dubi Liman yace “Nagode sosai kuma ina rokon Allah ya bayyana muku mai yi muku sata, sannan idan ya bayyana muku shi dan Allah kada kuyi masa yadda kuka yimin, domin kuwa kowane bawa da yadda Allah yake tsara rayuwarsa kuyi masa addu’ar shiriya awurin Ubangiji koda Allah zaisa sanadiyar addu’arku ya shiryu” sai Liman ya dubi wannan magana ta Abdul nan ya sake tabbatar da abdul ba Barawo bane. Sai Abdul yayi bankwana dasu, amma kafin ya tafi sai Limamin yace “Dan Samari naji kace kai bako ne kuma gashi jikinka ya jigata kuma tufafinka sun lalace sannan nasan kana bukatar abinci, dan haka muje gidana kayi wanka ka canza tufafi sannan kaci abinci” sai Baffa yayi guntun murmushi yace “Nagode Allah yasaka da alkhairi” sai Liman ya shiga gaba Abdul ya bi bayansa domin zuwa gidansa.
Da Abdul ya kammala komai na wanka da canza tufafi da cin abinci, sai yakara yin godiya ga Liman tareda yi masa bankwana ya tafi.
Tun da Abdul yabar gidan Liman bai tsaya ko ina ba sai kofar gidansu Mama, yana zuwa ya tsaya yana murmushi shi kadai yana jin farin ciki a zuciyarsa tun bai ga masoyiyarsa Mama ba, yana tsaye yana jiran yaron da zai aika, sai ga wata yarinya ta gifto Abdul ya tsayar da ita ya aika ta cikin gida don takira”
“ amma gabansa faduwa kawai yake don tunanin abinda zai faru dashi idan mahaifinta ya gansa, amma kuma sai ya kawar da duk wani tsoro da fargaba acikin zuciyarsa. Soyayya mai sauya tunani da nazari, Soyayya mai hana mutum ganin duk wata wahala ko walakanci akan masoyinsa, kamar yadda Abdul ya manta da dukan da yasha awurin mutanen gari sakamakon tuhumarsa da suke akan shi Barawo ne, duk wannan abin ya manta dashi abinda kawai yake tunani yaga fitowar masoyiyarsa.
Yana tsaye yana gyare-gyare, sai ga yarinya ta fito tace masa “an ce tana zuwa” sai Abdul yayi murmushi ya laluba aljihunsa da niyar yabata kudi amma sai bai ji ko sisi ba, sai dai yayi godiya gareta. Bayan yarinyar ta tafi sai ga Mahaifin Mama ya fito dan ganin mai kiran Mama.
Yana fitowa yayi ido biyu da Abdul, da hanzari Abdul ya durkusa kasa cikin ladabi ya gaida shi, amma yaki amsawa, sai ya dinga yiwa Abdul kallon takaici sannan daga bisani yace dashi “daman kai ne ka dawo, lallai yaron nan ko kai maye ne sai ka bar Mama, halan kunnuwanka basa jin abinda ake gayama ne, kai bakada zuciya ne?” Abdul na kasa batare da ya dago kansa ya dubi mahaifin Mama ba, sai yace “Baba kayi hakuri wallahi bana jin duk wata magana wacce ta danganci na rabu da Mama kuma bana gajiya da duk wani walakanci da zan fuskanta akan Mama haka kuma bana gajiya wurin rokonka dan Allah kabani Mama wallahi ina sonta” cikin fushi mahaifin Mama yace “to lallai kana tare da wahala, dan kuwa yau zaka fuskanci walakancin da ban taba yimaka ba, kabar kofar gidan nan tun kafin nasaka yara su koreka da jifa” sai Abdul yace “Baba wannan bazaisa naki sake dawowa ba, dan muddin ina lumfashi to bazan daina kasancewa duk inda Mama take ba koda za’a dinga yanka nama na” sai Mahaifin Mama ya kada kai yace “to shikenan zaka gani yanzu”. Sai kawai yabar Baffa ya shiga cikin gari domin kira yara.
Bayan wasu lokuta da tafiyar Mahaifin Mama cikin gari, Abdul na tsaye bakin kofar gidansu Mama bai je ko ina ba, sai ga mahaifin Mama yazo tareda gungun yara suna biye dashi, yana zuwa ya dubi yaran yace “kun gansa nan shi ne nakeson ku korar min shi da ruwan duwatsu” “Tau Baba” yara ne suka amsa da hakan, sai kawai suka dinga tsintar duwatsu suna jifar Abdul”
Abdul na tafiya yara na binsa da duwatsu suna kiran “Mahaukaci, ga Mahaukaci” haka suke fada suna jifarsa, bayan sun yi nisa da gidan su Mama. Abdul yana kare fuskarsa suna jifan jikinsa sai ga wani Mutum ya gifto yaga yara suna yiwa Abdul wannan aiki, sai yayi sauri yaje wurin tare da tsayar dasu, bayan sun dakata da jifar Abdul sai yace dasu “ku wadan mi irin ‘ya’ya ne haka, cewa akayi kuyiwa mahaukaci haka, dubi yadda kuka jimasa ciwo, ko tunda yana mahaukaci kashe shi zaku yi” sai suka yi dariya suka gudu batare da sun ce komai ba.
Bayan sun tafiyarsu, sai mutumin ya juyo dan ganin halin da Abdul yake ciki, sai ya tarar da Abdul ya suma, da sauri ya dauki Abdul ya tafi dashi gidansa, yana zuwa ya samu ruwa ya yayyafawa Abdul, bayan Abdul ya farfado sai mutumin yace “a’a kada ka tashi kwanta ka huta dan jikinka akwai rauni garesa” sai Abdul ya koma kwance, sannan mutumin yaje ya samu wasu magunguna ya jikawa Abdul ya kawo ya baiwa Abdul ya sha, sannan kuma ya samu Bandeji ya daurewa Abdul duk inda suka ji masa rauni.
Mutumin nan yayi dawainiya da Abdul sosai kuma ya bashi wasu tufafi ya saka bayan yayi wanka, sannan daga baya ya fahimci Abdul da hankalinsa, haka yasa ya tambayi Abdul yace “Bawan Allah me ya Hadaka da wadannan yara suka biyo ka sunama wannan aiki tareda kiranka Mahaukaci” sai Abdul yayi murmushi yace “Bakomai Bawan Allah, kasan halin kurciya wani abu ne nayi wanda ko mahaukaci bazai iya yi ba amma acikin kuskure na aikata shi, shi ne suka rinka yimin haka” Abdul ya boye wannan sirri ne saboda baya son kowa yasan halin da yake ciki, ba dan komai Abdul baya son kowa ya sani ba, sai dan gudun abashi wata shawara wacce zata danganci yayi hakuri da Mama, sai mutumin yace “to Allah ya kiyaye gaba” “Amin” Abdul ya fada, sai mutumin yace “to amma kabari gobe da safe sai ka tafiyarka, tunda kaga yanzu dare yayi sosai” Abdul ya amince da hakan yayi kwanciyarsa a gidan mutumin...
Daga alkalamin:-
*NEERATLURV*😍
&
*ABDULAZIZU AAJ*✍
(Na England)..
_Dedicated to Maryam (Mama)_❣
New Post
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Popular Posts
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO* 🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ Na *Abdul azizu AAJ* ✍ ...
-
11/2/2017 6:55pm *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis_...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ❣ ...
-
❣❣ ❣ MAYA! ❣❣ ❣ Via OHW📚 Neeratlurv.blogspot.com Wattpad@neerat_lurv 36_37 ***Sati daya da auren Ba abinda ya canza ku...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *Abdulazizu AAJ*✍ Da *Neeratlu...
-
❣❣ ❣ *MAYA! 🙍🏻♀* ❣❣ ❣ 1⃣1⃣ Via O. H. W📚 Neeratlurv.blogspot.co.ke Wattpad @neerat_lurv *** Tafiya suke kan hanya...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *NEERATLURV*😍 Da *ABDULAZIZU AAJ*✍ Via O....
-
15/3/2017 1:33pm *Muneerat*✍ *JININ JIKINA* _*111-115*_ NA *NEETATLURV*😍 _Based on fiction and love tale story_ _Dedicated to Aun...
-
19/2/2017 7:00am *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis...
No comments:
Post a Comment