New Post

Tuesday, 28 March 2017

MAYA

❣❣                       ❣❣
   ❣                            ❣


       👩🏻 *MAYA* 👩🏻

              ❣❣
                 ❣

            0⃣6⃣

Via O.H.W📚

Neeratlurv.blogspot.co.ke

Wattpad
@ Neerat _lurv

  Rayuwa yau da gobe yaci gaba da tafiya".
    "Cikin halayyen NAWAZ da Makinta Ba abinda ya ragu saima karuwa da tayi dan yanxu sunyi nisa a harkan Neman Mata da shaye shaye, sai dai Ba halayyensu bane yiwa Mace fyad'e basu tab’a yin fyad'e Ba sai dai ki kawo kanki ko su sunemeki "

  "Yanxu sun sami 2yrs a university inda sukuma sukeda 24yrs amma har yanxu suna part 1 sabida kullum cikin repeating dinsu ake kuma su ko a jinkinsu, dan ko irin yadda ake bin lecturers abasu kudi su basayi."


   "Cikin haka Matan Umar tasake haihuwa ya Mace wacce taci sunan kakar su wato Fateema bintu Zara ake kiranta da *MAYA* ( uwa kenan yake nufi cikin yaren bura/pabir) lokacin family'n sunyi murna Ba iyaka gata kam yarinyar Tasha ran suna harda yan Maiduguri sunje ciki har da NAWAZ da Makinta."
   "Goma ta arziki Daddy ya had'a aka Kai sunan."
    "Yanxu MAYA Nada shekara uku 3yrs a duniya ."

  " Makinta ne zaune da NAWAZ cikin d'akin NAWAZ phone dinsa ya soma ringing yana dubawa ya ga Daddy, dagawa yayi ya amsa bamu dai ji meye suka ceba kawai jimukayi yace ok Daddy ganin zuwa muna ma tare yanxu zamu iso."
   "Kallon Makinta NAWAZ yayi lokacinda ya yanke wayar yace hey Daddy na Neman mufa let hurry muje may b samune kasan kwanan nan Daddy akoi samu."
   "Mikewa sukayi dukkansu suka dauki hanyar bangaren Daddy suna tafe suna hiran wata babe da NAWAZ ya hadu da ita wajen clubing dasukayi jiya a pinnacle hotel har suka isa bangaren Daddy'n , sallama sukayi sannan suka kunsa Kansu."
   "Bayan sun sami waje sun zauna suka gyda Daddy da Daddy'n Makinta dan tare suke, amsawa sukayi kan Daddy yayi gyran voice."
   '"Daddy ne yace NAWAZ, Makinta ya Kira sunan su cikin wani murya ta daban."
   "Cikinsu saida ya duri ruwa kallon junansu sukayi kan suka had'a baki wajen amsawa Na'am Daddy.'
   "Son da gaskene Ana repeating dinku a school."
   "Ido suka waro waje kan sukace "REPEAT".
    "Eh shi repeat nake nufi."
   "A'a wlh Daddy saidai wasu munafukanne suke son hada kanmu daku koba Makinta? NAWAZ ne yake maganar Yana kanne wa Makinta ido."
  "Eh gsky Daddy wasu munafukai ne dai suka hada karyansu amma muda muke part 2 yanxu a Ina aka mana repeat din."
    "Okay dama nasani wannan lecturer naku kudi yakeso kuma yahad'a kanmu daku naji yanxu na yarda kuma tin da can na yarda kuna karatu am very proud of u sons karku damu da munafukai university ne ma kundena zuwa can London Zan turaku inda Ba yan sa ido yanxu kuje Ku Fara shiri cikin satinan zaku tafi."
    "Yeeeeeh that's my Dad NAWAZ yayi hugging dinsa Yana pecking dinsa a kumatu I love you Daddy Ka rabamu da nijeriya dama yan sa ido sunyi yawa thanks Dad.'
    "Makinta ma rungume Daddy'n,sa yayi sai murna suke the whole us in London studying wow thanks my super Daddy's ."
   "Da murna suka je daki. NAWAZ yace bro na jima da son yiwa Daddy magana dama ya fitar damu outside muyi karatu can amma ya rigani fad'a."
   "Makinta yace Kai tafi can ai Allah Wa wannan munafukin lecturer albarka daya kawo gulmar mu."
   "Ameen NAWAZ yace."
  "Makinta amma nifa da Daddy yakira mu we wlh bakaji yadda cikina yadau ruwa I thought ko wani abinne."
   "Dallah dama Kai matsoraci ne."
   "Haka suka ci gaba da hiransu har lokacin dasuka fita wajen Masha arsu."


   "Cikin sati dayan da Daddy yace musu duk sun gama shiri tsab unimaid kam dama tuni sunyi bye bye dashi.
    "Yau Monday misalin 8:00pm jirginsu zai daga zuwa London.
    "Sunyi shiri su tsap cikin kana nan kaya inda red shirt ne a jikinsu da blue jeans ajikin kayan anyi designing na rubutu kamar haka _Daddy's boy_ aka zana da bakin Abu they look handsome all kuma dama tun can baya kyawawane musamman shi NAWAZ dayake Kama da larabawa.
   "Dama tun Ana 2days su tafi suka dawo abuja dan anan jirgunsu zai daga zuwa London."
  "Dukkansu sunyi shiga ta alfarma haka suka dunguma zuwa airport, da isarsu aka Fara screening dasauransu cikin kankanin lokaci aka gama komai saura kawai jirgi ya daga su tafi."
    "Lokacin da suka zo sallama dasu Daddy har kwalla saida sukayi Mummy kam kuka Tasha hugging dinta NAWAZ yayi yana calming dinta with his sweetest word har yasamu tayi shiru tamishi fatan alheri."
   "Haka bangaren Makinta da Mummy'n sa shima saida ya kwantar Mata da hankali kan sukayi sallama."
  "Suna daga wa su Daddy hannu har suka shiga cikin jirgi, haka ma su Daddy."
   "Saida jirginsu yadaga kan su Daddy suka bar airport din."
 

   "Tafi sukayi na awanni kan suka isa garin London."
   "Suna isa komai yana jiransu, su Kansu Ba vakin garin bane sun Saba zuwa shiyasa vasu wani sha wuya suka isa gida.'
   "Gidane  dadai Daddy ya sai musu acan kowa da part dinsa kuma akoi komai na more rayuwa aciki basai sunje hostel Ba a gidan zasu zauna yana ma kusa da makarantar.
  "Bayan sunci sunsha suka huta har bacci ya daukesu, kuma a gobe zasu soma fita school."....


      ***             ***

_*Oxford university London*_

  "First day d'insu NAWAZ a Oxford university sun ga changes d'an va kamar unimaid yakeba."

   "Suna zuwa school kuma suna attending lecture sosai Ba kamar nan Maiduguri dasuke kin zuwa sai dai basu bar shaye shaye Ba amma basa sha yadda zasu bugu sabida tsaron da ke garin London Ba kamar nan Nigeria Ba."

   "Watansu daya dafara zuwa school sukayi wasu abokai guda biyu Abdul da Ahmad, suma yan Nigeria ne Abdul dan Maiduguri ne shima babansa mai kudine a garin Maiduguri suke da zama, shi kuma Ahmad dan yobe state ne shima suna da kudi sosai a familynsu "
    "Tun da suka hadu nan suka kulla abota ga halayyensu daya duka dansu Abdul manya ne a harkan nan da nan su NAWAZ ido yasake budewa."
   'Sun zama manyan yara ga yan Mata na rububin NAWAZ yaran masu shi dan NAWAZ Nada qualities da duk wata hadadiyar Mace zata so sa ya hada komai duk da shi din (bura/pabir) ne."

  "Abu kamar wasa har sunsami shekara biyu da Fara karatu cikin sherkara biyu nan su Daddy sun kaimusu visiting kusan sau hudu."
    "Ba laifi yadda su Daddy suka tarar da son's dinsu sunji dad'i dan duk wata signs da zai nuna bad habits d'insu bai nunaba shiyasa su Daddy suka rinka alfahari da son's dinsu suna samusu albarka."
   "Shege NAWAZ u know how to play games yes that's me yafada yana buga Abdul dake kwance dan yanxu duk suna gida daya.'
   "My man ya akayine."
  Shege ni wai Kai vaka ganin yadda su Daddy duk sun dauka Ba abinda muke aikatawa take a look at me bafa Wanda zai dauka ina shan abu ko Neman Mata no signs dude."
   "Gaskiya kam my man skin dinka mai kyau ne, keep d fare bunning NAWAZ."
 "Nan suka sheke da dariya Hhhhhhh."


  "Ba laifi NAWAZ suna dan gane abu a school yana dan kokari wani sa'in, wani lokaci kuma yasa wasa gaba."

  "Iskanci kam ya habaka sun rika har nuna ma sunyi, sun sake wayewa da sanin Mace."

  "Su Daddy na kaimusu visiting lokaci2 amma har yanxu basu San halinda su NAWAZ ke cikiba."


    "Suna da 28yrs suka kammala degree'n su ta fannin Mass communication, result yayi kyau Ba laifi."

  "Lokacinda su Daddy sukaje musu graduating day sun so su dawo gida tare amma suka ki haka su Daddy suka dawo su kadai."

  "Su NAWAZ dai sun ta zaga kasashe da dama,sai da suka dau kusan 1yrs and half (shekara daya da rabi) kan suka dawo gida Nigeria.'"

  " su NAWAZ anzama manyan yara ga kudi ga kyau shiyasa suke taka duk Wanda suka gadama suke kuma shuka tsiyansu."

  "Basa wani aiki kudi kawai iyayensu ke basu."

  "A birthday din NAWAZ da Makinta na cika 32yrs ne NAWAZ ya hadu da malika (maly) matashiya ce Yar 20yrs ce tanada kyau Ba laifi sai dai baYar hannunbace, suna zaune da iyayenta a damboa road wajen circular road a Maiduguri."

  "Tundaga lokacinda NAWAZ suka hadu da Maly suke shuka masha'arsu tare, NAWAZ na matikar ji da Maly kasancewar shiyayi dis vargin dinta kuma tana jin maganarsa gata da tsoronsa tana shanye duk wulakancida yake Mata kuma ya haneta da Hulda da wasu mazan."
  "Yanxu shekaransu daya da ita kenan."

  "Daddy yasake samun Karin girma yanxu yana minister of finance Daddy'n Makinta kuma minister of education."

  _*Wannan kenan*_

Muje zuwa _*cigaban Labari*_..


Daga alkalamin:-

*NEERATLURV*😍
        &
*ABDUL MR SMILE*😃

No comments:

Post a Comment

Popular Posts