❣❣ ❣❣
❣ ❣
👩🏻 *MAYA*👩🏻
❣❣
❣
4⃣
Via O H W📚
Neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad
@ Neerat _lurv
*** ***
Bayan auren su da shekara daya2 Allah yasake budamusu hanya sosai suke samu Aliyu da mustapha Ba laifi kowannensu kuma na kokari wajen kula da matarsa kuma suna gwada musu so."
"Acikin 1yrs dasukayi sun ziyarci umman su Aliyu da yayansa Umar a garin Biu."
"Umma taji dadin ganinsu sosai tayita samusu albarka, haka ma Ya Umar shima yaji dadin ganin tilon kaninsa da matarsa."
"Sati daya sukayi a Biu, sun ziyarci yan uwa da dama haka abokan arziki duk inda suka shiga anata yaba su kuma duk dangi na son Aeesha matar Aliyu, itama taji dadin yadda suke Mata duk gidan da suka je saitamusu kyuata dukka manya da yaransu."
"Mustapha,Nafeesa matarsa da Aeesha sunji dadin garin Biu musamman ire iren girkin (bura/papir) dasuke ci har koya sukayi, dazasu koma garin Maiduguri umman Aliyu da matan Ya Umar suka had'o musu kayan miya kamar su daddawa, kuka,karkashi, wake da sauransu."
"Haka rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin jin dadi da kwanciyar hankali, kuma ako da yaushe Allah na buda wasu Aliyu d'an sunkasance masu hazaka da rikon amana shiyasa komai nasu ke tafiya daidai."
"Matsalarsu bai wuci rashin haihuwar da basayi Ba amma sun dukufa sunmika kukansu gun Allah, kullum cikin addu'a suke kan Allah yabasu haihuwa, Dan su a ganinsu sunyi aure amma har Ana Neman d’ebe tsawon 2yrs basu haihuwa, sundai San yin Allah ne shiyasa basa wasa da rokonsa (Dan Allah S.W.T yakasance maji kuma magani, kuma yasan duk abinda yadace da bawansa, kar kakagaji da rokonsa Dan ya hanaka abinda kake so a lokacin kacigaba insha Allah wataran zai mallaka maka..Allah yasa mu dace Ameen!!!)."
"Ana cikin haka ne lokacin su Aliyu har sunyi aniversery na 2yrs da aure k’watsam watarana Aeesha ta tashi da wani mtsanancin zazzabi Wanda ya haifarmata kasala da amai, Dan ranan duk abinda taci saita amayar ta galabaita sosai hakan ya tilasta Aliyu daukanta zuwa hospital, a Maiduguri teaching hospital (TH) suka je ganin likita (doctor)."
"Gwajin farko sakamako ya nuna,Aeesha na dauke da juna biyu har na tsawon 3month."
"Zo kaga murna wajen couples (ma'aurata) dinnan sunkasa boyewa har k’weta Aliyu yayi wa doctor da nurses na hospital din, da murna suka je gida bayan an karanta musu zawabai da dokokinda yakamata mai ciki ta kiyaye da Wanda ya kamata su bi, Ahaka suka karasa fuskarsu fal farinciki."
"Sai vayan sallah'n isha suka je suka gaya mustapha da nafisa suma sun kasa boye farin cikinsu."
"Hira sosai suka sha ranan sai dare sosai kowannensu suka tafi suka kwanta inda su Aliyu suka sake k’wantarwa su mustapha hankali kan suma suna gab da samun nasu da yardar Allah kan suka musu saida safe."
"Kulawa Aliyu ke vawa Aeesha na musu Dan duk ya daukemata aikin gidan kap shikeyi ko tsinsiya yahanata dauka balle wani k’wak’waran motsi ita dai sai tayitamasa dariya tana tsokanarsa kan yana son wannan babyn sosai, shi dai cemata yake ha ai saima kin haihu tukun zakiga yadda ake nunawa yaro gata, murmushi kawai take Dan tasan wannan babyn kam zaisha gata inyaxo duniya."
"Ana ciki haka da sati daya nafisa tasamu Nata cikin itama na 3months Kai duk familyn sunyi murna."
"Gata suke samu duka daga bangaren mazajensu da yan uwa "
"Cikinsu ya girma wata 9 har yakai haihuwa, tunkafin yaran su zo duniya antanadar musu kayan more rayuwa."
_nidai neeratlurv na kalli Mr smile nace Kai Abdul da ganin yaran nan insun Zo duniya zasu sha gata_
_Abdul yace Kai neerat Bari kawai mudai je zuwa zamu sha kallo_
"Awata Friday ne dukka matan suka tashi da nakuda tashin hankali nan aka yi saurin rushing dasu TH, tsawon awa biyu duk suna nakuda a warsu ta 3 ne suka samu damar haiho yaransu masu kyau."
"Dukkansu yara Maza suka haiho, yaran sunzo cikin koshin lpy gasu many a dasu kamar yaran turawa."
"Babaninsu da uwayensu baki yakasa rufuwa gakuma kakaninsu Dan baban mustapha da Ummarsa sunje ga na Aeesha da nafisa kowa sai son daukar yaran yake."
"Saida suka d’ebi 1hrs tukun aka sallamesu nan suka dunguma zuwa gida."
"Tunda akayi haihuwar nan mutane ke zuwa varka kullum gidan makil cike da mutane kasancewar an san familyn Alibee a kap garin Maiduguri Dan mutum ne mai kamala da daraja talakawa uwa uba ga k’wetatawa shiyasa kowa ke ziyartan gidan."
"Matar Ya Umar dashi kansa sunxo haka dangi dake can Biu sun zo"
"Ranar suna yara sukaci sunansu, yaron Aliyu yaci sunan kakansa Yusuf (NAWAZ), shi kuma yaron mustapha yaci sunan kakansa ta uwa Muhammad (Makinta)."
"Anyi shagali iya shagali tsaya dad's b’ata lokacine masu karatu kawai just imagine yadda sunan zai kasance."
"Anyi taro lpy anci ansha an raba k’ewtuttuka da dama kan aka tashi a taro."....
"Tundaga wannan lokacin kuwa su Aliyu suka dauki son duniya suka daurawa yayansu."
"Wani uban so suke musu kamar mai."
*** ***
_*bayan shekara 10*_
Su NAWAZ da Makinta sun girma gawani shagwa6a da rashin kunya Dan duk abinda suke so shi ake musu, ba'a tsawatar musu KO kadan abin ransu suke, ko a makaranta basa aje hankali Sam sai wasa kullum ana ciken repeating din su amma iyayen ko ajikinsu."
"Lokacin suna primary six (6) a Elkanemi duk primary section an sansu haka malaman su dan yaran akoi su Neman tsokana duk da NAWAZ din bai cika maganaba amma akoi zuciya anka tabasa ".
"Akoi rannan da wata Aunty English language tabasu assignment NAWAZ bai yiba datazo making taga nasa blank bai rubuta komaiba."
"Aunty tace who is that Yusuf Aliyu Yusuf come out here."
"Yana ji ya batsar kamar Ba Shiva sai da yan ajin suka nunasa Dan kanta taje desk dinsa cox NAWAZ akoi taurin Kai."
"Koda taje ta tambaya why have you done your assignment."
"Budar bakinsa yace bcoz am not in the mood of doing it."
"Aunty tace who d hell u are da har zaka cemin u are not in the mood of doing ur assignment huh! Tayi maganar in a louder voice."
"Cikin yanayi na rashin jin tsoro da rashin kunya yace bcoz am daddy's boy and mommy's son."
"Lallai tace yaronan kneel down tasa and tabasa good 10 lashes da worning na kar yasake Mata rashin kunya."
"Kuka sosai yasha har yaje gida, ai ko yana zuwa gida ya kulle kansa a d'aki yaki fitowa mummy'nsa Ba rokonsa da batayiba amma yaki budewa dan kanta ta barsa, Makinta ne yazo yake gayamata incident da ya faru a school shiyasa yake fushi."
"Da Daddy ya dawo mummy ta sanar dashi abinda ya faru har da kulle kansa dayayi a daki."
"Daddy ne yaje yata bugawa yaki budewa har saida yaji Daddy ne kan ya bude."
"Da kyar Daddy yashawo kansa after promising him gobe zai je school din a dau mataki, tukun ya yarda yaci tuwo har sukayi hira."
"Washegari Daddy yaje wajen head master yamasa bayanin ko shi waye da abinda ke tafe da shi."
"Ankira English teacher head master ya rufeta da fad'a har da cewa tabawa NAWAZ hakuri."
"Haka ta daure tabasa hakuri (yaron da zatayi 'da dashi, Allah shi kewta)."
"Aka Kara da Jan kunnenta not to beat him again coz if that happen again she will face d consequences."
"Head master yakara Ba NAWAZ da Daddy'nsa hakuri kan Daddy ya hakura."
"Toh fa haka rayuwa taci gaba da tafiya kullum NAWAZ da Makinta na Dada baci har suka shiga secondary school."
"Iskanci, rashin kunya sai abinda yakaru".
"Su Aliyu kam da mustapha arziki ya bunkasa Dan har anfara dama siyasa dasu Dan a halin yanzu suna a commissioners."
Daga alkalamin:-
*NEERATLURV*😍
&
*ABDUL MR SMILE*😃
New Post
Saturday, 25 March 2017
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Popular Posts
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO* 🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ Na *Abdul azizu AAJ* ✍ ...
-
11/2/2017 6:55pm *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis_...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ❣ ...
-
❣❣ ❣ MAYA! ❣❣ ❣ Via OHW📚 Neeratlurv.blogspot.com Wattpad@neerat_lurv 36_37 ***Sati daya da auren Ba abinda ya canza ku...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *Abdulazizu AAJ*✍ Da *Neeratlu...
-
❣❣ ❣ *MAYA! 🙍🏻♀* ❣❣ ❣ 1⃣1⃣ Via O. H. W📚 Neeratlurv.blogspot.co.ke Wattpad @neerat_lurv *** Tafiya suke kan hanya...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *NEERATLURV*😍 Da *ABDULAZIZU AAJ*✍ Via O....
-
15/3/2017 1:33pm *Muneerat*✍ *JININ JIKINA* _*111-115*_ NA *NEETATLURV*😍 _Based on fiction and love tale story_ _Dedicated to Aun...
-
19/2/2017 7:00am *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis...
No comments:
Post a Comment