26/2/2017 9:00pm *Muneerat*✍
_*JININ JIKINA*_
_*96-100*_
NA _*NEERATLURV*_😍
_Based on fiction and love tale story_
_Dedicated to Aunty Sis_💞
_*Here in a page of honour for you my mommah FATIMA BATSARI and my one and only namesake MISS NEERAT this is a page for you, I love you guys more than words can explain,ILYSM♥*_ #onelove 💞
*****
"ɗaki Mum ta wuce rai bace, shima Dad biyota yayi."
"A bakin gado ya ganta zaune tayi tagumi ta tafi duniyar tunani, zuwa yayi yazauna kusa da ita yayimata side hug sannan ya kira sunarta ZAINAB."
"Na'am ta amsa sa amma bata ɗago ta kallesaba."
"Look at mie we need to talk huh! "
"Alhj ina jinka ta ɗan ɗagowa a karonnan."
"Kidaina ɗaga hankali kan abinda yaron nan yafaɗa bai isaba yayi kaɗan yace zaiyi wannan auren nasan matsalar ki muskan ce, toh ki kwantarda hankalinki ba'abinda zai faru da ita, ko kin manta nace itama ɗiyatace zan zamemata uwa kuma uba wannanfa alkawarine dana ɗauka kuma saina cika, ZAINAB idan harɗai ina nunfashi a doron kasa muskan bazata yaɓa yin kuka ba insha Allah Bazan bari FARIS ya sata bakin cikiba, wannan auren ban goyi bayansaba matata idan har hakan shine kwanciyar hankalinki da farincikinki kinji koh."
"Fuskarta sake kuma ɗauke da murmushin jindaɗin zancen mijinta tace na goɗe mijina a kullum ina alfahari da kai kasancewarka matsayin mijina uban 'ya'yana."
"Bakomai matata ina son ganinki cikin farinciki, kwanciyar hankalinki shine nawa."
"Peck ta kaimasa a cheek tace amma wani hanzari ba guduba nifa wannan al'amarin yaban mamaki."
"Wani al'amari kenan inji dad da faɗa."
"Gani nake kamar faris baya hayyacinsa anya kuwa ba wani abin a kasa."
"Kai ya jinjina maganar ki gsky ne nima haka nake gani sabida bantaɓa tunanin faris zai iya furta waɗannan maganganun ba musamman yadda nasan yakeson muska da alama akoi abu a kasa."
"tayani gani mijina nasanfa halin yaron nan kumafa dacan yarinyar na sonsa amma shi kullum cikin tsanarta yake, kai gsky da sake kasan mai hankali shiyake ganin ɗingishin ƙkwaɗo."
"gasky kam karmuyi sake yanxi yakikeganin za'ayi sabida nace masa yatafi london a gobe kina tunanin zaitafi kuwa?."
"Ina ai ban tunanin haka, wannan yarinyar fatima idonta a ɓuɗe suke nasan duk yadda za'ayi idan shi faris yaje yafaɗamata bamu yarda da zancenba, toh daga nan zatace zatayi wani abu akanmu kaga tunda dama gwanda mu mike tsaye, nafiloli zamu sake kan wanda muke a da sa'annan zamu sami malamai suyita saukar Qur'ani da yanka ana saɗaka koya kace.?"
"Excellent matata haka kawai zamuyi kuma muja shi faris jikinmu mununa mun yarda da auren kinga haka zaiyarda damu aikinmu zaitafi mai kyau."
"Haka za'ayi, abuna kuma biyu muskan zamanta can ita ɗaya kaga ba daɗi nace ko zata dawo itama sai amata nata neman tsarin a amata saukar al qur'anin itama."
Toh sai gobe zanwa su anwar magana su sata a jirgi saita dawo ko? "
"Eh haka za'ayi , nan suka sauya hiransu da tasu salon soyayyar."
***
Allah ne kaɗai yakaisa giɗa sabida wani irin tukinda yake, koda yashiga gida da gate man ya hangamemasa gate ya shige @360 parking ɗinma yayisane kawai sabida akarkace yayi, rai ɓace yafita yanufi cikin gida, ɗakinsa direct yanufa, kayan jikinsa ya rage yashige toilet, shower yasakarwa kansa idonsa runtse yana cikin jacuzzi ruwa na sauka a dukkanin ilahirin jikinsa,yana jin daɗin ruwan, duk haushin su Dad yakeji kamar ya shakesu ya huta kawai haka yakeji a ransa yana ganin hakkan shizaifi samamasa farinciki a halin yanxu."
"Ya ɗau tsawon lokaci a haka kan yayi wanka yafito, ya shirya cikin kananan kaya, fitayayi bayan yazari key yaɗau mota ya fice,hanyan gidansu faty yaɗauka dancan kaɗai yakeji idan yaje zai ji sanyi cikin ransa."
"Ya isa gidan yasanar da faty ta shirya tasamesa kofan gidansu yanajiranta."
"Cikin shirin wata doguwar rigar material blue ta fito tana rankwasa tana yauki harta karasa wajensa."
"Shikam faris ganinta dayayi kawai ya nemi ɓacin ransa ya rasa sai ma murmushi dayake kamar bashibane wanda ya murtuke fuska ɗazu."
"Gaisawa sukayi data shiga motar,ya amsa yacemata fita zasuyi zuwa gari, tace ba matsala suje."
"Suna tfy suna hira abinsu anan ne ta tambayesa ko yasanar da Dad maganarsu yacemata eh yasanardashi yace daya kammala abinda yke zaisami daddy'nta suyi magana, farinciki tayi sosai harta kasa boyewa."
"shidai kallonta yake batasan karya yamataba, shikuma yama rasa dalilinsa na mata karya."
Da haka sukaje wajajen shakatawa dayawa sai dare sukadawo ya ajeta gidansu shima ya wuce gidansa.....
***
_*2 days later*_
Bayan kwana biyu Da maganarsu Dad kan ɗauko muskan da za'ayi, yasamu yakirasu Anwar yasanar dasu su sata d jirgi tadawo gida."
"Sunyi komai shida aliyu yadda Dad ya bukata sunsama mata viza,."
"FARIS kam tunranda su Dad sukaki amincewa su nemamasa auren faty yaɗaina zuwar musu gida ko kiransu a waya ya daina yi sam kuma su ko sunkira baya picking wai yana fushi dasu. kuji wani zancefa anan."
"Fanin su Dad ma dasuga abin na faris yayi kamari suka kyalesa sunsan baya hayyacinsa ne, kuma har yau su fareeda basuda masaniya kan abinda yake faruwa a gidan."
***
" Ranar Wata alhamis tana zaune a falo tayi tagumi tafi wata uwa duniya can tana tunani, ba komai take tunawa ba illah faris, ya canza kota kota gashi yaki yadawo, gashi kullum cikin kawomata korafi yake da zarar tace bayakiranta saiyace aikine yamasa yawa ita a gsky yanxu tasoma gajiya zuciryarta tasoma mata hasashe kan ba gasky faris ke faɗamata ba, takasa sakewa kwanan tana yawan yin mafarkai iri iri."
"Tana yawan ganin faris dawata mata fuskarta baki kirin gashitana neman halakasa,itakuma muskan duk lokacin ta dososu wani farin haskene ke bayyana kuma da zarar ta dososu ko wancan matar tayi niyan kashe faris ɗin idan wannan hasken muskan ya bayyana saita kasa yin komai."
"Toh fa muskan wannan abin shi kedamunta gashi takasa gane mai wannan mafarkin ke nufi, tana cikin wannan tunanin ne tajiyo sallamarsu Anwar, take ta komo hankalinta taɗan daidata nutsuwarta waje ɗaya ta amsa su haɗe da basu izinin shigowa."
"izini tabasu suka zauna, bayan sun gaisa, tawuce taɗaukomusu abin motsa baki, hannunta ɗauke da tire da jug saikuma kofuna da plate cike da snacks ta zo dashi, a gaban kowannensu ta ɗirarmasa kan wasu kananan stools tace dasu bismillah."
"Sai da suka ɗan taba abin da takawo musu tukun suka tamabayeta ya zaman kaɗaice? ya makaranta kuma? duk tace abgodewa Allah zaman kaɗaici kuma tana fama."
"Anwar yace faris ya makale acan yaki yadowo kuwa, sai Aliyu yace nimadai abinda nagani."
"Murmushi tayi tace zai dawo insha allah bada daɗewaba coz nasan yayi missing ɗina kamar yadda nima nayi missing ɗinsa kunga duk inda yake hankalinsa na gida na tabbata."
"Suma murmushin sukayi Aliyu yace toh sarauniyar iya magana da soyayya kyafaɗamana haka ai dama tunda kika kasance matar faris kam."
"Anwar ne ya amashesa da faɗin faɗi kanka tsaye abokina gori takemana da wayancewa."
"la muskan tafaɗa tana mai rufe fuskarta da hannu biyu alamar taji kunya tace nifa ba gori nakemuba."
"Toh muskan munji faɗar Anwar, yace dama gaidaki mukazo yi saikuma visa da muka tahomiki dashi inji Dad yace gobe zaki 9ja yana maganar ya ciro visa card ɗin yamikamata."
"full of suprise take kallon card ɗin a ranta tace 9ja Allah dai yasa lafiya ne, murmushi ta kakaro tace musu na gode insha Allah yau zan shirya."
"Toh suka amsata Aliyu yace gobe zamuzo mukaiki airpot insha Allah."
"Toh ba komai sai kunzo Allah ya kaimu."
"Ameen, muzamu wuce sukace da ita suna mikewa."
"Har bakin kofa tarakasu ,tamusu godiya yadawo ciki, tana sake sake cikin ranta, waya taɗauko takira fareeda kozata bata information amma kash wayar baya shiga haka ta gwaɗa na Dad shima, duk saida ta gwada wayar 'Yan gidan amma batasaminsu, hakura tayi kawai."
"Tashi tayi taje ɗaki tasoma haɗa kayayyakinta na tafiya duk wani abinda tasan zata nema tahaɗa su a babban troley'nta cip cip."
****
Washegari jumma'a kamar yadda su anwar sukace zasu zo ɗaukarta toh suncika alkawari sunzo sun ɗaukota sun kaita airpot."
"Kafin jirginsu yaɗaga saida suka kira Dad a Waya suka haɗashi da muskan sukayi magana."
_Readers karku manta duk wannan abinda ake faris baida masaniya akai_
"basuɗau lokaciba a maganar dadukayi da Dad wanda ni neerat banji abinda sukafaɗaba amma sai ganinta nayi tana murmushi alamar maganan da sukayi yamata daɗi kenan, wayar ta mikamusu lokacinda ake bukatar pasinja su shiga jirgi tamusu sallama tawuce abinta.."
"baifi 30mns ba jirginsu yaɗaga zuwa nijeriya."
_Nima neerat nan na tattraro na ɗiba a guje dan na biyo muskan nijeriya😂😂na ɗaukomuku rohoto_.
© _*NEERATLURV*_😍
New Post
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Popular Posts
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO* 🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ Na *Abdul azizu AAJ* ✍ ...
-
11/2/2017 6:55pm *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis_...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ❣ ...
-
❣❣ ❣ MAYA! ❣❣ ❣ Via OHW📚 Neeratlurv.blogspot.com Wattpad@neerat_lurv 36_37 ***Sati daya da auren Ba abinda ya canza ku...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *Abdulazizu AAJ*✍ Da *Neeratlu...
-
❣❣ ❣ *MAYA! 🙍🏻♀* ❣❣ ❣ 1⃣1⃣ Via O. H. W📚 Neeratlurv.blogspot.co.ke Wattpad @neerat_lurv *** Tafiya suke kan hanya...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ 👩🏻 *MAYA* 👩🏻 ❣❣ ...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*🌷 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *NEERATLURV*😍 Da *ABDULAZIZU AAJ*✍ Via O....
-
15/3/2017 1:33pm *Muneerat*✍ *JININ JIKINA* _*111-115*_ NA *NEETATLURV*😍 _Based on fiction and love tale story_ _Dedicated to Aun...
-
19/2/2017 7:00am *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*😍 _Dedicated to Aunty Sis...
No comments:
Post a Comment