❣❣
❣
*_MAYA!ππ»♀_*
❣❣
❣
1⃣4⃣
Via O.H.Wπ
neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad
@neerat_lurv
Kwanaki sun ja abubuwa da dama sun faru Maya taxama yar gida Momi na kokarin kulawa da ita Sosai dama Maya badai kwalliya da son kamshi ba sai Gashi tasamu Momi ma akoi ado ai nan da nan Maya ta wanku tayi tas da ita yanxu tasami 3weeks a gidan tsakanin ta da Nawaz sai harara idan takan yi kawana biyu zuwa uku basu hadu ba ita kam hakan ma yafi mata dan da zaran sun hadu toh fa wani bakon lamari take tsintan kanta ciki bugun zuciyarta na tsananta yana fita da sauri2 ga kuma wannan sexy eyes dinsa idan ya zubamata yana rikitata wani irin abu take gani cikin idon Wanda Bata San Meye shiba.
Yau ma kamar kullum Suna kitchen ita da Momi Suna girke, dan Daddy yana gari, Momi macece wacce takasance mai kishin mijinta shiyasa Sam bata barin masu aiki suyiwa mai gidanta girki takan shiga kitchen ta girkamasa ita da kanta ko Nawaz ma yasaba da girkinta Sosai.
Sun hada breakfast kala2 kusan abin ci Kala uku, part na Daddy suka nufa suka jera kan dinning komai yayi tsab kana Momi tace suje suyi wanka.
9:30am Momi, Daddy, Dan Maya sun hallara kan dining Nawaz ne kadai bai isoba basu minti 5 da zama ya shigo cikin shiga na half jamba yadin kakarta sky blue yasha hula sai kamshin turaensa na zauj-al-ud yayi matukar kyau fuskansa a dan sake da fara'arsa yakasara sa inda suke bai ko kula akoi Maya a wajen ba yasoma zuba shagwa6a yana gaida iyayen nasa sukuma sai biyemasa suke, idan da sabo Maya tasaba da wannan abinda da Nawaz keyi shiyasa Sam bai damunta amma can kasar zuciyanta haushi yadda yake abu kamar karamin yaro take, sai bayan sun gama gaisawan ne Momi ta dubeta tace "daughter baki gaida yayanki ba " uhmm tace sannan ta daga ido dan ta gaidasa karab idonta cikin nasa yana watsamata kallonsa data fi tsana a hankali ta janye idonta cikin nasa can kasa2 tana murguda baki tace "Ina kwana " a taikace ya amsata da cewa "lpy" yana sane da murguda bakin da take cikin ransa yayi kwafa yace zanyi maganinta.
Sunyi breakfast Lpy qalau da suka gama Kan Nawaz ya fita Daddy yake tunatar dashi batun sa Maya a makaranta yace "Daddy na manta ne amma yau insha Allah zanje na duba dama I think asata a Ruby Springfield school naga wajen akoi kyau kuma akoi discipline " Daddy yace "OK make the arrangements zanma transfer din kudi a account dinka sai ku gama anything necessary" toh insha Allah Daddy da haka yamusu sallama ya fita.
Juyawa Daddy yayi yace " Mamana kina son makarantar ai ko?"
"Ae Daddy ina so"
"Masha Allah gobe sai kuje kugama komai ko."
"Toh Allah ya kaimu tace ta dubi Momi tace "Momi Pls kiban wayanki inje inbuga game" A'a daughter zandan yi amfani dashi yanxun, kukan shagwa6a tashiga yi Daddy yace "Mamana ki daina kuka yau za'ayi sayamiki wayan ki kinji koh " Yeeee tayi ihun murna nan da nan Daddy ya dau wayansa yakira PA dinsa yace yanason zuwa nan da anjima akawowa daughter dinsa waya mai kyau da tsada, PA Ya amsa da toh ranka shidade.
2:30pm PA ya kawowa Maya wayan kirar iPhone 7+ Wayyo murna wajen Maya ba a magana nan da nan tajona sa a charging, saida yayi full charge ta dauka tadawo wajen Momi ta koyamata kan wayan, ta koyamata ba laifi ta gane Sosai sabida kwakwalwar Maya nada saurin daukan abu da ganewa, aiki yasamu zama tayi sai buga game dinta take.
*** ****
*_Zara plaza_*
Nawaz na hango yana sauri dan yafita a plazar ko gabansa bai kallo diff yaji yayi Karo da abu ga kuma tarwatsewan abubuwa da sauri ya daga ido da niyan zabga matsifa fuskan nan tasa kamar hadiri amma ya tsaye chak sakamakon ganin wata xukekekiyar yarinya fara mai dan kyau tanada tsayi dai-dai misali hancin tama ba laifi daga kasanta akoi dan shape Masha Allah sanye take da doguwar riga Wanda akamasa dinkin fitted gown ya matseta idanuwanta sanye da sunglasses zarewa tayi taga wanda yamata wanga barnan ai kuwa itama chak ta tsaya, kame2 tasoma tace "em. em.... Pls am sorry I was in hurry shiyasa" no no Pls I must be the one to say so inji na Nawaz yana dukawa kasa yafara tsince abubuwan da suka zube ya maidasu cikin jakan ya mikamata yace" Am Yusuf Aliyu Haidar amma ana cemin Nawaz and you ya tambayeta, tace Zainab Adam kime ana cemin zee. Oh nice to meet you yace, me too ta maida masa yace can we be friends yakashe mata ido daya. Gira ta daga masa tace "sure " yace wow thanks Gaskiya, you're welcome tace, phone number sukayi exchanging nan kowa yatafi da zullumin cikin ransa.
Nawaz na driving yana tuna irin yadda ya hadu da Zee sai yadan yi murmushi yana rausaya kansa yace wo ni yana dan buga stairing motansa har ya isa Ruby, ya shiga yagama komai an basa form da duk wani abinda yakama ganinsa yasa sukace basai sunyi ma sister'nsa interview ba she is admitted to jss3 ya musu godiya Ya tafi.
A gida ya bai wa Momi komai takardu, school bag daya saimata dasu uniform har sandals da toms duk ya saimata ya shedamata ran Monday Maya zata fara zuwa Amata passport kuma shi zai kaita ran Monday din dun yagama sauran abubuwan, albarka Momi tayita samasa yaji dadin hakan kuwa duk rashin jin Nawaz yana matukar son parent dinsa kuma yana so Suna samasa albarka.
Momi ta kaiwa Maya kayayyaki duk inda ta gwada komai daidainta kamar ya aunata daga uniform da shoes din daidanta murna kam ba'a fada tayi ba adadi...
#vote
#comment
#share
#love
*_Daga Alkalamin ✍_*
*_NEERATLURVπ_*
*_DA_*
*_ABDUL MR SMILEπ_*
New Post
Monday, 1 October 2018
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Popular Posts
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO* π· ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ Na *Abdul azizu AAJ* ✍ ...
-
11/2/2017 6:55pm *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*π _Dedicated to Aunty Sis_...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ π©π» *MAYA* π©π» ❣❣ ❣ ...
-
❣❣ ❣ MAYA! ❣❣ ❣ Via OHWπ Neeratlurv.blogspot.com Wattpad@neerat_lurv 36_37 ***Sati daya da auren Ba abinda ya canza ku...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*π· ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *Abdulazizu AAJ*✍ Da *Neeratlu...
-
❣❣ ❣ *MAYA! ππ»♀* ❣❣ ❣ 1⃣1⃣ Via O. H. Wπ Neeratlurv.blogspot.co.ke Wattpad @neerat_lurv *** Tafiya suke kan hanya...
-
❣❣ ❣❣ ❣ ❣ π©π» *MAYA* π©π» ❣❣ ...
-
✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ❤ *SHAUKIN SO*π· ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨ ✨✨ ✨ NA *NEERATLURV*π Da *ABDULAZIZU AAJ*✍ Via O....
-
15/3/2017 1:33pm *Muneerat*✍ *JININ JIKINA* _*111-115*_ NA *NEETATLURV*π _Based on fiction and love tale story_ _Dedicated to Aun...
-
19/2/2017 7:00am *Muneerat*✍ ♦ *JININ JIKINA*♦ _Based on fiction and love tale story_ NA *NEERATLURV*π _Dedicated to Aunty Sis...
No comments:
Post a Comment