New Post

Friday, 28 September 2018

❣❣
  ❣

*_MAYA!πŸ™πŸ»‍♀_*

❣❣
  ❣

1⃣3⃣

Via O.H.WπŸ“š

neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad @neeratlurv


**Lafiya kalau suka isa Maiduguri da misalin 3 na rana direct gida suka wuce tunda Maya Tasha kuka tayi bacci jikin Momi mota na parking Momi tayi tapping dinta tace"Maya tashi mun isa gida."

A dan firgice ta tashi tana xazzare ido tana mitsikesu nan Momi ta fita hade da xaga wa ta bude wa Maya kofan da take, kafafunta ta fitar a hankali sai sannan ne ta daga idonta hakan yayi dai-dai da fitar Nawaz a mota shima harara ya bankamata ya wuce su fuuu yayi site dinsa.

  Da taimakon Momi ta fita tana rike da hannu Momi sai kalle2 take cikin ranta kuma tace aljannar duniya kenan gidan ya matukar haduwa tsaya wa na kimata gidan bata lokacine amma just imagine yadda gidan senator Aliyu zai kasance har Momi ta kula da yadda take kallon gidan murmushi tayi kawai tana Jan hannunta har suka karasa part na Momi ma'aikata suna biye dasu da trolley dinsu, Ai kuwa nan Kallo yakoma sama dan tsaruwan part na Momi komai yaji falon golden color ne komai a ciki, Fallon yasha royal chairs dakuma manyan show glasses sai babban plasma wow falon ya hadu iya hadu, kan kujera Momi ta zaunar da ita itama ta zauna yar aikin Momi ne taxo da tray cike da ruwa da drinks tasoma jera gaban Momi da Maya, ita dai Maya tace ko mafarki take ne irin wannan hadu da gidan yayi duk cikin ranta take wanga magana bata sake tsintan kanta cikin duniyar mafarki ba saida Momi ta tsiyayamata lemon kwakwa da madara mai sanyi tasha har lumshe ido take though a gidansu tana shan abi mai sanyi but na gidan nan daban yake.

Sai da suka Kore ishin ruwa tukun Momi ta dada kama hannunta suka haura sama nan Momi ta bude wani daki dake facing nata mai girman gaske suka shige wow Masha Allah abinda Maya take ta nanata wa cikin ranta komai na dakin maroon ne Katon Italian bed ga wardrobe da sauran tarkace kamar dakin wata amarya Momi tace " daughter nan ne dakinki daga yau akoi komai cikin dakin can kuma ta nunamata toilet tace wancan bandaki ne akoi towel, bath suit da su bath jel da sauran su a dakin yanxu ki cire kayanki before na shiga nawa dakin sai nazo na nunamiki yadda zakiyi wanka kishiga ki daura towel , toh kawai Maya ta bita dashi nan ta fice ai kamar jira take nan da nan tasoma Shafa gadon da sauransu sai murna take har da dan guntun karkada jiki ta dade before ta wuce toilet ai kuwa kusan mutuwar tsaye  tayi dan ganin yadda toilet din ma ya hadu nan ma saida tayi shirmenta before taja towel ta daura da tarage kayan jikinta.

  Kusan kamar minti ishirin Momi ta shigo cikin dakin cikin shigarta na dogon riga mara nauyi tace "kina ta jirana ko daughter am sorry wuce muje na hadamiki ruwan tana fada tana wuce wa gaba Maya na biye da ita a baya a cikin toilet din sai da tahadamata ruwa cikin Bathtub da jel masu kamshi kuma ta nunamata yadda zatayi kan ta fita tana mai shaidamata tayi alwala tayi sallah sai tasamesa a falon kasa.

  Bayan minti 40 Maya ce ta sauko cikin dogon rigar atamfa bawata makeup amma skin dinta na glowing har ta karasa wajen Momi, murmushi dauke fuskar Momi tace "yar Momi kin fito."

 "Eh Momi."

"Yauwa good girl."

"Gefen Momi takarasa ta zauna."

"Mikar da ita Momi tayi suka jera zuwa dining nan suka ci abinci Maya dai yar Kallo ta koma ga girki iya girki dauke da Manya Manya nama rago gana kaza ai kuwa taci abinci ba laifi.


**** **** ****
 2days later da dawowarsu tunda suka dawo  Nawaz bai je part na Momi ba Daddy'nsa kuma tun washa gari ya wuce Abuja.

Yau da misalin 9 na safe yayi wanka ya shiya cikin pencil trouser dinsa dawata shirt fara wadda akayi rubutu da bakin abu a jiki  _We are the best_ aka rubuta ga kamshi turaraensa na Armani code sai tashi yake Kai tsaye part na Momi ya wuce da sallamarsa ya shiga Momi kadai ya Tatar a falon tana zauna cikin shigarta na Matan Manya hade rai tayi da ta gansa  shikuma karsawa yayi yana murmushi yace.

"Momi am very sorry I know i offended you almost 2days banzo na dubaki ba am sorry"

  Yi tayi kamar bata gansaba ba ta dauke kanta.

 Nan yasake matsowa kusa da ita ya kama hannunta duka biyu yana murzawa a hankali yasake cewa "Momi i said am sorry fah."

  tsakanin uwa da d'a nan ta jawosa jikinta tace Nawaz you don't seems to care about your Mom anymore yau kwana biyu baka lekani ba kuma muna gida d'aya."

   "Yes yes Momi kiyi hakuri am damn tired ne tunda muka dawo i have been resting for a while shiyasa but i miss you Mom yakare maganar cikin muryan sa mai sanyi da dadin sauraro."

  "Kansa ta Shafa tace is okay son na hakura but don't try doing this again huh."

  "Yeee insha Allah Momi I will not yabata peck a gefen kumatunta, dai-dai nan Maya ta sauko cikin riga baka da wando mai ratsin jaja a jiki kanta sanye da hula fuskarta dauke da powder sai dan lip gloss data Shafa idonta yasha kwalli tayi kyau ba laifi tana turo dan karamin bakinta tayi wajen Momi sai ganin Nawaz da tayi jikin Momi nan da nan da hade fuska, shikuma Nawaz ya ma manta da ita a gidan sai yanxu ya tuna Ashe tare suka dawo daga tafiyar da ita hade fuska shima yayi kamar bai taba dariya ba ya ballamata harara janye jikinsa yayi daga na Mom yakoma dayan kujeran ya zauna, tana ganin ya bar wajen takarasa wajen Momi tana gunaguni kasa2 ba Wanda yake jinta duk tsinewa Nawaz take a ranta.

  Janyota Momi tayi jikinta tace" my baby sai yanxu kenan kiki gadamar tashi".
 
  "Tura bakin ta kuma yi tace ni ba ke bane kika ki tashi na tun dazu cikin shagwa6a take maganar. "

  "Toh ai baby bana so kanki yayi ciwo shiyasa amma nan gaba idan na tashi sai in rinka tadaki ai yayi miki koh."

  "Eh Momi yayi uhmm Momi yunwa fah nake ji."

  "abincinki na dinning table je ki ci kuma kiyi sauri zaki rakani unguwa kinji, ai da tsalle tayi tasake dalewa jikin Momi tana dariya tace Yeeee xan fita yau ta tashi da gudu tayi dining na soma serving kanta."

  "Duk abinda suke Nawaz na kallonsu sai harara dayaketa aikawa Maya duk haushinta yake ji yarinya sai shagwa6an tsiya ji yadda take abu Mtssw yaja dogon tsaki ya cigaba da kallon sa haushi yagama cikasa.

  Sarai Momi tajisa ta share kamar bata jiba cikin ranta kuma tace Nawaz problem.

  Maya bata fi minti ishirin ba tagama nan ta garxaya wajen Momi tace tagama su tafi toh, dariya kawai Momi Ke yi ganin yadda ta kagu su fita.

  basu Bata lokaciba suka shirya suka fice sun bar Nawaz shi kadai a gida.

  Gidan kawar Momi suka je daga nan suka wuce shopping a 2days dake gidan madara kaya Niki Niki Momi ta sai wa Maya,  bayan sun fita suka sake garxayawa zuwa 3G gallery nan ma ta saimata abubuwa iri iri sunyi yawo da ita Sosai sabida har sidis ta kaita tasha ice cream sai yamma lis suka dawo Zuciyar Maya cike da farinciki ga kayan sawa dana kwalliya da Momi ta jidamata da takalma harda gyalluka da hijabai wow she damn happy. _wannan kenan_


#vote
#comment
#share
#Love


*_Daga Alkalamin_*

*_NEERATLURV😍_*

  *_Da_*

*_ABDUL MR SMILE😊_*

No comments:

Post a Comment

Popular Posts