New Post

Sunday, 2 December 2018

❣❣
  ❣

MAYA!πŸ™πŸ»‍♀

❣❣
  ❣

23_25

Via O.H.WπŸ“š

Neeratlurv.blogspot.com
Wattpad@neerat_lurv


  Sati biyu suka yi a Makkah suka dawo nan gida Nigeria...

  Maya tayi kyau tayi haske jikinta yazama so smooth sai yalki da daukar ido take, tsaraba kam ba'a magana daga sadeeya,inna,babanta,mamarta,yayanta,matarsa da Daddy saida tasai musu kayyayaki barin kayan kwalliya data jidamusu da sadee,turarruka da sauran su duk abinda tasaya bata saiwa Nawaz ko tsinkeba,shikam dasuka dawoma baya nan ya Dan yi tafiya Kaduna sai kusan kwanan su uku da dawowa ya dawo already yan sanda zuwa sun watse.

Koda akaiwa su inna kayayyakinda Maya ta musu tsaraba inna harda kukan farinciki tana ta sawa Maya albarka..

   Kamar yadda Momi tamata alkawari haka tacika tasa hakorin hajji yadda takeso kuma yamata kyau ga open teeth(wushirya) dazaran tayi dariya  abin saiya burgeka..

  Satinsu daya da dawowa takoma skul sabida junior waec dasuka fara kuma alhamdullillah sunyi sunkammala lafiya yanxu tana Hutu a gida..

  ***  ***
 Yau takasance Wednesday tun safe Maya takejin ciwon ciki kadan kadan tun tana daurewa yanxu hartakai stage dinda takasa tabuka komai, kwance take kan bed dinta dafe da mararta sai juye juye take ita daya.

  Da sallama Momi ta shiga dakin saidai hangota datayi yasata yin saurin karasawa gareta ta dagata ta hadata da jikinta ta rumgumeta tana shfa kanta tace.
 
   “What happen daughter ?”

  Bata iya maganaba illa hannunta dake dafe da mararta take nunawa Momi, Momi na ganin haka ta gane maye yake damunta Dan haka a hanxarce ta sauko kasa takira rejoice house  help dinta tace sukamomata Maya susata a mota already tama driver magana, haka suka cincibeta suka sanyata mota suka kama hanyan hospital, tun a hanya Momi tasanarwa Daddy Dan haka before sukarasa hospital din har ya rigasu..

   Suna isa akayi A/E da ita duk wani taimako likotoci sunbata kuma alhamdullilah she's feeling much better yanxu su Daddy na nan tsaye aka gangaro da ita zuwa extra room Dan ta huta Momi ta bi bayansu while Daddy kuma yabi doctor zuwa ofis dinsa.

   Suna isa ofis din likitan yadan yi dube dubensa hade da gyra zama yasoma magana Kamar haka yace.
 
   “Yace a gaskiya honourable bazan boyemaka yar ka takawo stage dinda magani kadai bazai taimaka mata wajen healing ba.”

   Daddy ya gyra zama yace ban fahimcekaba doctor..

  Eh what i mean is dat yanxu ba magani yarka ke bukataba she needed a man with her.

  Ajiyan zuciya Daddy yasauke hade dajan numfashi yace “if I got you right kanaso kacemin aure is the solution to her condition.”

   Likitan yayi saurin cewa exactly what I mean.

  Uhmm Doctor naji but amma is she not to Young to be with a man?”
   
   No she's not takai 16yrs what is it there dantayi aure taraya sunnar ma'aiki kuma beside nafadaamaka tanada karfin sha'awa so is better amata auren kan wani mummunan Abu yazo yabiyo baya duk da bama fatan hakan amma duk da haka kana da lokaci go and think.

  Daga haka Daddy yace ya gode insha Allahu zaiyi tunani kuma zai sanar dashi inya yanke shawara, nan yabasa sunayen magani dayayi prescribing da allurai yamasa sallama yafita..

  Saida Daddy yabiya yasai maganin before yasami Momi, nan ya Tatar da Maya na bacci, yadda sukayi da likitan yakorawa Momi before yacemata jibi zashi biu yasanar da Umar sai su San abinyi,nan Momi tace hakan ma yayi kyau...

  Kawanansu daya aka sallamosu sosai Maya tasa mu sauki sosai kuma ta mulmule tana shan magani kuma ga allura da akemata.

  Cikin ikon Allah Kamar yadda Daddy yafada haka akayi Dan yau yaje biu wajen brother dinsa domin tattauna matsalar Maya...


   ***   ***

  Zaune suke dukkansu su ukun Daddy sai malam Umar da inna duk sunyi shiru bayan Daddy yagama fadamusu yadda sukayi da likitan...

   Shiru sukayi har nawasu lokaci kafin daga baya Daddy ya yanke shirun tahanyar cewa yanxo mai mafita yaya?.

  Kanina ae mafitar dayane sai amata auren inyaso tacigaba da karatun a gida majin tunda ka dage da karatunta ko ya kace?.
 
  Hakane kam, Inna tayi saurin cewa "ae matsalar badaga nan bane ita takwarar tawa akoi matsayinta kun tambayeta.

  A'a inna amma ae sai a tambayeta ko, nan Daddy yacire waya yakira Momi bayan sun gaisa yake tambayarta Maya tace gata nan kusa yace tabaiwa Maya wayan tana karba tayi sallama nan suka gaisa bayan sun gaisa Daddy yajehomata tambaya yace.

 “Daughter shin akoi Wanda yake sonki kuma kike son sa ma'ana kuke soyayya?”.

   Shiru tayi kamin daga bisani tace a'a Daddy ni banda saurayi kuma ni ko maza sun min magana bana tsaya.

  Masha Allah haka akeso nan ya yanke wayar, yamaido hankalinsa Kansu inna ya koramusu yadda sukayi da Maya, saida inna ta furxar da iska tace toh yanxu Ali ya kakeso ayi kaji daimai yartaka tace..

  Ajiyan zuciya ya sauke kamin daga bisani ya sassauta murya irin Wanda yake kashe jikin mai sauraro yasoma koro bayani kamar haka yace

  “Inna ai wannan bawani abin tada hankali bane dama ni na dade dayin wani tunani ince tunda ga yayanta shima ba auren yayiba kuma kullum maganarda muke fama dashi keanan mai zai hana akahadasu tare amusu auren.”

  Kul! Inna tace bazai yuba wannan mai bakin halin zaku hada da jikata yaje ya kashemin ita ko toh wannan abun  bamai yuwabanae ehen.

  Malam Umar na ganin haka yasake sassauta muryansa fiye da tunanin mai sauraro yasoma rokon inna da nunamata value yin haka da yadda zumunci xai Dada karfafa tsakinsu da kyar da sudin goshi inna ta yadda amma bayan tace duk abinda za'ayi saidai takoma Maiduguri da zama Dan tasamusu ido ta yadda bazai cutarda jikanta kuma wallahi bisa sharadi duk ya yarda ya wa jikanta ba kyau koto kadai zata rabasu, abun yaso yabaiwa su Daddy dariya amma suka dake sukace sunji sun yarda."

  Nan taro ya watse cike da farinciki a ranar Daddy ya dawo kuma shima nawaz ranar ya dawo daga guntun tafiyar da yayi sabida duka wainar da ake toyawa baisan da zancenba..
 
  Koda Daddy yafadawa Momi yadda sukayi tafi kowa farinciki da zancen Dan itama inbadan bakinta yayi nauyi ba taso bawa Daddy wannan shawaran...

  Koda dare yayi bayan sun hallara Suna bisa dinning Suna din abinci kamar yadda suka saba.

  Saida suka gama Daddy ya umarci Maya da taje daki shikuma Nawaz ya tsaya zasuyi magana..

  Suna Zaune Nawaz na Zaune bisa gefe Daddy yayi gyran throat yace "Yusuf da full name dinsa ya kirasa abinda Daddy baitaba yiba keanan nan duk tsawon zamansu Nawaz yasan maganar da za'a yi mai girma da muhimmancine ya amsa da na'am.

  Daddy yace karka kawomin rainin hankali da wannan jijji da kan naka I want all your attention zan tambayeka shin kacire matar aure?”

   Kansa akasa ya dago yaga fuskan mahaifinnasa bawasa yace a'a Daddy ban cireba"

  Okay shin kana da wacce zaka cire ko kuwa?.

  Nan ma yadan yi Jim kamin daga baya yace a'a Daddy ni fa a gaskiya bansami test dinaba har yanxu shiyasa nakasa cirewa mace kuma bana jin zan samu nan kusa yadafada Kansa tsaye batareda yasan mai ke shirin faruwa dashiba.

  "Good Daddy yafada"

  Yasake gyra zama yace "Nawaz I am your Father I am d one who brought you to this world and kasan bazan taba cutarda kaiba beside inada hakki kan zabamaka mace dakuma duk wani Abu dazai zamanto alheri tattare da kai Dan haka nan da sati biyu zan dauramaka aure kana iya auren duk wacce kakeso gaba za ka iya tafiya am done with you and no More words from you, yana kaiwa nan ya mike yabar wajen leaving Nawaz daskare a wajen kamr an dasasa da kyar yadago jajjayen idonsa yadubi Momi dasu da niyar magana itama ta bangamasa harara tamike tayi gaba abinta.

  Yazauna awajen more than 40mins without moving his fingers kamin daga bisani yayi gattering courage yawuce part dinsa yana shiga toilet yanufa yasakarwa kansa shower idonsa lumshe yasoma tuno maganganun Daddy tiryan tiryan suka soma dawomasa fresh wayyo he's totally speechless not knowing a words to say koda yafita daga wanka direct fridge dinsa yawuce giya yadauka yasoma kwankawada saida yaji Kansa a sama tukun ya sauke kwalbar nan yayita surutai irin nasu na bugaggu har bacci ya daukesa..

   Bangaren Daddy kuma ya kira Dan uwansa yasanar masa hukuncin da ya yanke na auren nan da 2weeks kuma yasake shedamasa dukkansu yakeso su shirya nan da 3 days zaisa a gyra gidajensa guda biyu daya inna ta zauna aciki daya kuma shida dansa da matarsa yanaso duk su kasance kusa dashi ba yadda malam Umar zai yi haka ya amince yace toh kuma Daddy yakara dacewa kayan sawansu kadai zasu zo dashi komai na amfani zaisamusu...

_wannan keanan_

Toh readers d Battle has just beganπŸ˜„πŸ˜„
 

Daga alkalamin✍

NEERATLURV😍
   
      Da

ABDUL MR SMILE 😊


Vote
Share
Comment
Love..


 Ana tareπŸ’ž

No comments:

Post a Comment

Popular Posts