New Post

Friday, 28 September 2018

❣❣
  ❣

*_MAYA!πŸ™πŸ»‍♀_*

❣❣
  ❣

1⃣3⃣

Via O.H.WπŸ“š

neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad @neeratlurv


**Lafiya kalau suka isa Maiduguri da misalin 3 na rana direct gida suka wuce tunda Maya Tasha kuka tayi bacci jikin Momi mota na parking Momi tayi tapping dinta tace"Maya tashi mun isa gida."

A dan firgice ta tashi tana xazzare ido tana mitsikesu nan Momi ta fita hade da xaga wa ta bude wa Maya kofan da take, kafafunta ta fitar a hankali sai sannan ne ta daga idonta hakan yayi dai-dai da fitar Nawaz a mota shima harara ya bankamata ya wuce su fuuu yayi site dinsa.

  Da taimakon Momi ta fita tana rike da hannu Momi sai kalle2 take cikin ranta kuma tace aljannar duniya kenan gidan ya matukar haduwa tsaya wa na kimata gidan bata lokacine amma just imagine yadda gidan senator Aliyu zai kasance har Momi ta kula da yadda take kallon gidan murmushi tayi kawai tana Jan hannunta har suka karasa part na Momi ma'aikata suna biye dasu da trolley dinsu, Ai kuwa nan Kallo yakoma sama dan tsaruwan part na Momi komai yaji falon golden color ne komai a ciki, Fallon yasha royal chairs dakuma manyan show glasses sai babban plasma wow falon ya hadu iya hadu, kan kujera Momi ta zaunar da ita itama ta zauna yar aikin Momi ne taxo da tray cike da ruwa da drinks tasoma jera gaban Momi da Maya, ita dai Maya tace ko mafarki take ne irin wannan hadu da gidan yayi duk cikin ranta take wanga magana bata sake tsintan kanta cikin duniyar mafarki ba saida Momi ta tsiyayamata lemon kwakwa da madara mai sanyi tasha har lumshe ido take though a gidansu tana shan abi mai sanyi but na gidan nan daban yake.

Sai da suka Kore ishin ruwa tukun Momi ta dada kama hannunta suka haura sama nan Momi ta bude wani daki dake facing nata mai girman gaske suka shige wow Masha Allah abinda Maya take ta nanata wa cikin ranta komai na dakin maroon ne Katon Italian bed ga wardrobe da sauran tarkace kamar dakin wata amarya Momi tace " daughter nan ne dakinki daga yau akoi komai cikin dakin can kuma ta nunamata toilet tace wancan bandaki ne akoi towel, bath suit da su bath jel da sauran su a dakin yanxu ki cire kayanki before na shiga nawa dakin sai nazo na nunamiki yadda zakiyi wanka kishiga ki daura towel , toh kawai Maya ta bita dashi nan ta fice ai kamar jira take nan da nan tasoma Shafa gadon da sauransu sai murna take har da dan guntun karkada jiki ta dade before ta wuce toilet ai kuwa kusan mutuwar tsaye  tayi dan ganin yadda toilet din ma ya hadu nan ma saida tayi shirmenta before taja towel ta daura da tarage kayan jikinta.

  Kusan kamar minti ishirin Momi ta shigo cikin dakin cikin shigarta na dogon riga mara nauyi tace "kina ta jirana ko daughter am sorry wuce muje na hadamiki ruwan tana fada tana wuce wa gaba Maya na biye da ita a baya a cikin toilet din sai da tahadamata ruwa cikin Bathtub da jel masu kamshi kuma ta nunamata yadda zatayi kan ta fita tana mai shaidamata tayi alwala tayi sallah sai tasamesa a falon kasa.

  Bayan minti 40 Maya ce ta sauko cikin dogon rigar atamfa bawata makeup amma skin dinta na glowing har ta karasa wajen Momi, murmushi dauke fuskar Momi tace "yar Momi kin fito."

 "Eh Momi."

"Yauwa good girl."

"Gefen Momi takarasa ta zauna."

"Mikar da ita Momi tayi suka jera zuwa dining nan suka ci abinci Maya dai yar Kallo ta koma ga girki iya girki dauke da Manya Manya nama rago gana kaza ai kuwa taci abinci ba laifi.


**** **** ****
 2days later da dawowarsu tunda suka dawo  Nawaz bai je part na Momi ba Daddy'nsa kuma tun washa gari ya wuce Abuja.

Yau da misalin 9 na safe yayi wanka ya shiya cikin pencil trouser dinsa dawata shirt fara wadda akayi rubutu da bakin abu a jiki  _We are the best_ aka rubuta ga kamshi turaraensa na Armani code sai tashi yake Kai tsaye part na Momi ya wuce da sallamarsa ya shiga Momi kadai ya Tatar a falon tana zauna cikin shigarta na Matan Manya hade rai tayi da ta gansa  shikuma karsawa yayi yana murmushi yace.

"Momi am very sorry I know i offended you almost 2days banzo na dubaki ba am sorry"

  Yi tayi kamar bata gansaba ba ta dauke kanta.

 Nan yasake matsowa kusa da ita ya kama hannunta duka biyu yana murzawa a hankali yasake cewa "Momi i said am sorry fah."

  tsakanin uwa da d'a nan ta jawosa jikinta tace Nawaz you don't seems to care about your Mom anymore yau kwana biyu baka lekani ba kuma muna gida d'aya."

   "Yes yes Momi kiyi hakuri am damn tired ne tunda muka dawo i have been resting for a while shiyasa but i miss you Mom yakare maganar cikin muryan sa mai sanyi da dadin sauraro."

  "Kansa ta Shafa tace is okay son na hakura but don't try doing this again huh."

  "Yeee insha Allah Momi I will not yabata peck a gefen kumatunta, dai-dai nan Maya ta sauko cikin riga baka da wando mai ratsin jaja a jiki kanta sanye da hula fuskarta dauke da powder sai dan lip gloss data Shafa idonta yasha kwalli tayi kyau ba laifi tana turo dan karamin bakinta tayi wajen Momi sai ganin Nawaz da tayi jikin Momi nan da nan da hade fuska, shikuma Nawaz ya ma manta da ita a gidan sai yanxu ya tuna Ashe tare suka dawo daga tafiyar da ita hade fuska shima yayi kamar bai taba dariya ba ya ballamata harara janye jikinsa yayi daga na Mom yakoma dayan kujeran ya zauna, tana ganin ya bar wajen takarasa wajen Momi tana gunaguni kasa2 ba Wanda yake jinta duk tsinewa Nawaz take a ranta.

  Janyota Momi tayi jikinta tace" my baby sai yanxu kenan kiki gadamar tashi".
 
  "Tura bakin ta kuma yi tace ni ba ke bane kika ki tashi na tun dazu cikin shagwa6a take maganar. "

  "Toh ai baby bana so kanki yayi ciwo shiyasa amma nan gaba idan na tashi sai in rinka tadaki ai yayi miki koh."

  "Eh Momi yayi uhmm Momi yunwa fah nake ji."

  "abincinki na dinning table je ki ci kuma kiyi sauri zaki rakani unguwa kinji, ai da tsalle tayi tasake dalewa jikin Momi tana dariya tace Yeeee xan fita yau ta tashi da gudu tayi dining na soma serving kanta."

  "Duk abinda suke Nawaz na kallonsu sai harara dayaketa aikawa Maya duk haushinta yake ji yarinya sai shagwa6an tsiya ji yadda take abu Mtssw yaja dogon tsaki ya cigaba da kallon sa haushi yagama cikasa.

  Sarai Momi tajisa ta share kamar bata jiba cikin ranta kuma tace Nawaz problem.

  Maya bata fi minti ishirin ba tagama nan ta garxaya wajen Momi tace tagama su tafi toh, dariya kawai Momi Ke yi ganin yadda ta kagu su fita.

  basu Bata lokaciba suka shirya suka fice sun bar Nawaz shi kadai a gida.

  Gidan kawar Momi suka je daga nan suka wuce shopping a 2days dake gidan madara kaya Niki Niki Momi ta sai wa Maya,  bayan sun fita suka sake garxayawa zuwa 3G gallery nan ma ta saimata abubuwa iri iri sunyi yawo da ita Sosai sabida har sidis ta kaita tasha ice cream sai yamma lis suka dawo Zuciyar Maya cike da farinciki ga kayan sawa dana kwalliya da Momi ta jidamata da takalma harda gyalluka da hijabai wow she damn happy. _wannan kenan_


#vote
#comment
#share
#Love


*_Daga Alkalamin_*

*_NEERATLURV😍_*

  *_Da_*

*_ABDUL MR SMILE😊_*

Tuesday, 18 September 2018

❣❣
   ❣

*_MAYA!πŸ™πŸ»‍♀_*

❣❣
  ❣

1⃣2⃣

Via O.H.WπŸ“š
Neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad
@neerat_lurv

*_Alhamdulillah Tnx for d prayers dearest Naji sauki nakuma ga sakonninku know that Neeratlurv always heart you and she loves y'all ocean and galaxies_*#oneloveπŸ’ž
 
***
 Kashegari da misalin Karfe biyu bayan sallah'n juma'a aka daura auren Aliyu jama'a dayawa ba dama sun hallaci Bikin sabida Aliyu yaron kirkine uwa uba ga Malam Umar shima.

Andan hada walima Wanda yadan kayatar na maza xalla a kofan gida can na hango Nawaz da Makinta Zaune daga dayan bangaren.

Hannu Makinta ya kai yadan taba Nawaz yace "guy  what are you  staring gabadaya hankalinka is not here. "

 Fuskansa ya dauke kamar bada shi Makinta ke maganaba ya wani sha mur cikin ransa kuma yana duba wane ko zai ga small brat dinsa because he wanted to see her again yarinyar tayi tsiwa dayawa kuma kana ganinta kasan shag6abbiya ce shikuma akasari bai son mace mai tsiwa gani yake hauka ke dibansu in suna haka.

  Wayar hannunsa yacigaba da dannawa bai ko kula Makinta ba seconds -seconds ya kan dan waiga ko zai yi nasaran ganinta amma da zaran yaga Makinta na kallonsa sai ya wani dauke Kai yana shan kamshi.

Makinta kam ikon Allah yake gani shima banza yayi da Nawaz because inda sabo toh yasaba da Hali irin na Nawaz.


  Misalin 8 na dare aka dau amarya zuwa gidan sirikai cikin yan daukar amarya harda Makinta amma banda Nawaz daya kasance cikin mota yana chatting abinsa.

Biki yayi biki kusan kwana uku ana abu daya acikin kwana na hudu ne duk aka watse aka bar yan gida da kadan daga cikin dangi.

Duk cikin kwanakin nan Nawaz na yinsa ne but he really need to be at home and duk iya yinsa nason ganin yasake ganin MAYA bai yiba har yagama hakura.

Yau Monday yakasance misalin Karfe 10 na safe granny dasu Mummy Zaune a falo Maya na daga gefen granny Senator Aliyu  suka doka sallama a bakin kofan amsawa akayi nan aka musu izinin shiga.

Shigarsu keda wuya ai Maya na hango Nawaz tayi bayan granny da saurinta tace kaka shine wancan din haka take fada tana sake shigewa jikin granny.

Kallo Kallo kowa yake idan take nunawa su Daddy dasu Malam Umar suka sami waje suka zauna Abban Maya ne yace "Maya ki fita bayan Inna kan na isa wajen."

Kambu! harda kai Umaru Kake son doke ta ko! toh bismillah Inna tafada tana jawo Maya daga bayanta da duk tagama tsorta dan ba kadan ba Marin da Nawaz yamata ya rikitata shiyasa duk take tsoransa.

kusa da Inna ta zauna kamar zata shige jikinta tukun Inna tace "ai ni dama nasan wannan mai jan kunnuwan shi ya doke min jika kuma ai sai na rama mata."

Ba shiri Inna ta Mike tayo kan Nawaz takai masa dundu a baya dan kara ya saki ya Mike nan suka soma xagaye dakin Inna tace dole sai ta sake dukansa shikuma yace A'a su Daddy kam kallonsu suke shikuma Nawaz sai da ya tabbatar ya gama gajar da ita ya kyaleta da kanta ta nemi waje ta zauna tana haki tace "ja'iri yaron "

Tabe baki yayi alamar ko a jikinsa.

Inna tace kai Aliyu yi maza ka dau wannan hege yaron naka ku barmin gida kan ya kasheni da jikata.

Daddy yace toh Inna gobe ma ai sai mu wuce ko.

Da sauri tace ni yau ma ku tafi dariya ta baiwa yan falon yadda ta dage su tafi a yau din.

Nawaz yace "yar tsohuwa kwantar da hankalinki ni ko yanxu ma na iya tafiya."

toh katafi mana dan banza kawai.

Fuskansa ya kwabe yana yatsine wa shi duk ya kagu su bar garinnan Wlh.

Inna kuwa gaisuwa sukayi da ya'yan nata can Daddy yace Maya ba makaranta yau ne ya tambaye ta.

Cike da shagwa6a tace akoi nidai kawai naki zuwa ne yau ta dan turo dan karamin bakinta.

Kajimin 'ya yanxu wasa kike hala baki son karatu infact kina ma jss nawa.

Uhmm ina jss 3 zamuyi junior Waeca term dinnan.

Toh Masha Allah zaki bini birini insaki makarantar yan gayu Daddy ya tambayeta.

ai kuwa da saurinta tace eh kawu zan bika nima nazama irin kulawa ta gidansu ramatu itama can birni taje taxama kamar yar Indian.

Yauwa my daughter zamu tafi tare da ke kinji.

Yeee tafasa ihu tana tsalle cikin jin dadi zata je birni cike da murna ta fice a dakin zata kaiwa su ramatu Labari.

Lalle Aliyu toh fa ba inda xaka kaimin jika Wato Kaje can danka Ya kashemin ita ko.

Mummy da tunda taga Maya yarinyar tashiga mata rai tace "Inna dan Allah kibarmin ita Wlh ba abinda zai samata I promise to take a good care of her."

Tafi can ai bakin ku dayane duk Zakuje ku kashemin jika kawai.

Daddy ne ya sassauta murya yana ta magiya har saida su Malam Umar da Daddy'n Makinta suka sa baki da kyar ta amince nan ma saida Umman Maya tasa baki amma ta gindaya musu sharadi Wlh duk abinda yasami jikarta toh fa basu kwashe da kyau ba suka ce sunji sun amince.

Nawaz da duk haushi yagama cikasa yayi tam kamar zai fashe sai Kallo dayake bin Mummynsa dakuma Daddy dashi zaman falon ne yagama basa haushi Ya fice gaba daya ko ta kansu bai biba.

Maya dai an zaga anata fada kawaye za a tafi Maiduguri gidan kawunta sai murna take ita a dole zata zama yar gayu.

Nawaz ko da yafita gida ya wuce ya kulle kansa a daki da haushi bacci ya daukesa.


Kashegari suka shirya dan tafiya nan fa Inna da Umman Maya suka rungumeta kamar bazasu sake ganin junaba Suna ta kuka
Ali da Abba ba karamin juriya suka yi ba dan yadda suka saba da Maya itama tayi kukan rabuwa da yan uwanta ba kadan ba har saida Mummy tajata jiki ta rinka lallashinta.

Duk wannan abinda ake Nawaz na a mota sai kallonsu yake yana yatsine fuska duk sun cika kunnuwansa da koke2.

Toh fa nan suka dunguma cikin mota suka kama Hanyar borno garin shehu..


*_Vote_*
*_Comment_*
*_Share_*
*_Follow_*
*_Love_*

*_Daga Alkalamin✍_*

*_NEERATLURV😍_*

     *_Da_*

*_ABDUL MR SMILE😊_*

MAYA

❣❣
  ❣

*MAYA! πŸ™πŸ»‍♀*
❣❣
   ❣

1⃣1⃣

Via O. H. WπŸ“š
Neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad
@neerat_lurv


***

  Tafiya suke kan hanya Makinta na danne2 a waya while shikuma Nawaz na agefe sai tsuka yake ta ja a hankali fuskarnan tasa a dan murtuke juyawa Makinta yayi  idanunsa suka Kai fuskan Nawaz dariya ne yazomasa ba shiri dan haka yasha dariyarsa abin ya baiwa Nawaz haushi shifa he hate someone laughing or smiling without reason infact shi ko da akoi reason he usually don't do it balle a yananyin da yake dun haka ya sake yatsine fuskansa hade da dauke kansa daga kallon Makinta can.

 Can makinson yadan dubesa yace ."

  "Guy Wai Meye Kake Hakane you don't even look at your face and look how it turn please relax and calm down. "

  I will not huh!  Kai ni wai ina ruwanka danine A'a. "

  Yace "akoi and let me tell you something tafiyan ne munriga da munkama hanya so is better Kayi calming kanka and enjoy the journey. "

  'Mtssw! dan karamin tsaki Nawaz yaja tare da ciro earpiece ya maka kunnensa bcoz he's tired of hearing all that bulshitt of Makinta.'

'Tafiya tayi nisa almost 2hours kan suka isa iya kod'uwa Nawaz yayi dan jin gargada duk inda suka fada gargada sai dai kaji yayi tsaki amma da suka shiga garin biu tuni yadan fara sakin ransa dan wani irin ni'ima daya ke ji. "

   "Anguwa mai Suna  tashan dan Fulani suka nufa bakin wani gida gini zamani dai-dai misalin suka faka gidan nada dan girma da babban gate. "
   
  'sarai yasan sun isa dayaji mota ta tsaya amma dan isa da takama ya lumshe ido kamar bai sani ba Makinta dayasan halinsa yayi tapping dinsa kadan nan ya bude ido hade da zare earpiece din yace.

  "what happen?"
 
 Cewa yayi "Mun iso sai kafita. "

  Sai da yabata almost 2mins kafin ya fita ya rufamusu baya. "

  'cikin gida ne babba part yakai uku a gida cike yake da dangi da abokan arxiki sai diban gaisuwa ake amma banda Nawaz.

  'Wani babban Palo suka nufa nan nahango wata tsohuwa Zaune kan darduma sun hira da wani dattijo da wata mata sai dan saurayi dake gefe Suna hango su Daddy Tafara fadin .

  "Lale Lale yan Maiduguri sannunku da zuwa cikin fara'a take maganan ."

 'karasowa sukayi dukka nan Daddy ya matsa kusa da ita ya zauna yasoma kwasan gaisuwa an gaggaisa can ta hango Nawaz gefen Mummy yana dan tabe baki tace Kai ja'iri xonan.

 Bonsewa yayi kan yace "nifa ba inda zani kin wani tsufa amma sai fitina soyayyace nace bana yi dake sai da yar budurwa.

Lalala nicema akayi ina sonka ina zan kai Mijinda bai son xiyara.

  Shagwa6e fuska yayi kan yace "yo ai dan kina kauye yasa ban son zuwa."
 
 "Ai kuwa ya tabo ta tace "inaji ji a kauyen a ka haifi uban ka ja'iri kawai."

 'Tabe baki yayi alamar I don't care dinnan.

 Nan kowa ya fashe da dariya yana kallon jika da kaka na matsifa.

   Girki Kala2 aka shigar musu hade da jibge wa gabansu kowa na serving kansa amma Nawaz ko kallon inda abincin yake bai yiba.

  Mummy ce tadan zunguresa kasa2 tace "kadiba abincin mana."

  Kamar mai rada yace "no am not hungry ."

 Jin abinda yafada tadan kauda kanta

Mikewa su granny sukayi dan subasu waje su ci abinci

Suna fita kuwa Daddy ya tambayesa dalilin kin cin abinci nan yacemasa baya jin yunwa sharesa Daddy yayi yace "ai shi ba yaro bane in yana jin yunwa he know the way to get food. "


Mikewa yayi yace Zai dan fita idan Makinta yagama he should meet him outside toh kawai makinta ya bisa da shi.

Tafe yake cikin gidan kansa na a kasa yake tafe yana tafiya sai kace bai son taka kasa cike da izza da yanga amma kuma da zafi2 sabida cikkaken namiji ne mai jini a jika dai2 inda zai sadasa da gate na gidan yake dosowa. "

  Wata matashiyace wacce baza ta wuce shekaru sha hudu 14yrs ba a duniya sanye take cikin Riga da wando na Indian dress blue tana sanye da dan karamin hijab pink colour tana da dan tsayi ba gajeruwa bace sannan bata cika jiki ba amma ta kugunta da dan fadi duk da karamace baka ce ita irin black beauty dinnan idanuwanta Manya ne masu daukar hankali bata da dogon hancin yana nan dai-dai misali tashigo gidan hannunta rike da wani dan madai daicin roba da gani daga markadai take tafe hankalinta sam bai Kai ga gabanta ba sai jitayi taci Karo da abu ta dan razana Bata san lokacinda ta sake roban hannunta ba saukar roban yayi dai-dai bisa jikin Nawaz.

 Da hanzari ya janyeta daga jikinsa hade da kai kallonsa ga kayansa What! Yayi exclaiming yana sake Kai dubansa ga markaden geron da ya zube a jikinsa ai maza yayi kanta da iya karfinsa ya fincikota hade da hadata da jikin bango.

Wani irin bahagon Mari yakaiwa fuskanta cike da tsan-tsan bacin rai yasoma magana yana cewa.
 
  "Baki da hankaline are you blind bakya ganine ko jakancine da hauka ke damunki. "

Shiru ne yarinyar tayi dan ko kwakwaran motsi bata iyawa jin irin rikon da ya mata sai hawaye dake bin kuncinta dan shigar Marin da ya saukemata tun da uwarta ta kawota duniya ba'a taba maremata fuska irin na yau ba.

Shikuwa jin Shiru yasa sa sake harxuka Wato yarinyar nan yar rainin hankali ce ina mata magana ta wani basar dani I know what to do nan yasa ke kifata da Mari Wanda yayi sanidiyan da tayi tangal tangal zata fadi kasa yayi dai-dai da fito wansu Daddy da sauri Makinta ya taro ta shikuma sai huci yake kamar Wanda yayi gudu.

Daddy ne yasoma magana yace "What are you doing Nawaz Zaka kasheta ne?."

  Nawaz yace" Dad look at how she spoil my clothes don't she look is she a blind."

  Daddy yace "Kayi hakuri mana maybe she's in hurry and beside karama ce bazata juri irin abinda Kake shirin yimata ba kuma ma ai bada gangan tayiba. "

Shiru yayi dan bacin rai yarasa mai zai fada.

Daddy yakai duban sa ga yarinyar har yanxu kuka take ta na bisa gefe dai dai nan malam Umar ya shigo hango kaninsa yayi tsaye ga kuma Nawaz sai can kuma Maya da sauri ya karasa yace.

 "Maya mai ya faru? ne mai ya sameki? ya naga kina kuka?"

Duk lokaci daya ya jeromata tambayan cikin kuka ta nuna Nawaz wa baban ta sannan tace.

"Abba na shigo ban ma gansa ba kuma ba da gangan nayi ba amma ya rinka marina."

 Sai sannan ne Daddy yace Maya ta wuce cikin gida shikuma Mal Umar juyawa yayi kan Nawaz yana basa hakuri Daddy yagama harxuka yace wa yayansa ya sharesa ya daina basa baki nan yaja hannunsa suka fice tare da Daddy'n Makinta suka bar Nawaz tsaye da Makinta.

Dan bacin rai fuskar sa har ta rine tayi ja Makinta ya karasa ya ja sa gefe yace wait for me here am coming.

Cikin gida makinta ya wuce inda aka sauke su Mummy dama su kenan sun fito da shirin Tafiya gidan Daddy dake garin suka tadda wannan ta'asan Ya faru su Mummy na kan Maya dake ta kuka tana fadan wani Dan makka ne ya mareta dan ita ko wuka aka samata bata San sunansa ba kuma kallon balarabe tamasa hakuri akebata nan aka jata zuwa dayan bangaren juya wanda Mummy tayi suka hadu da Makinta nan yafadamata abinda ya faru da hanzari tace su je wajen Nawaz din.

Suna isa a wajen suka samesa yadda taga ya Bata fuska kaman karamin yaro abin yaso yabata dariya amma ta danne gudun mai Zai iya faruwa karasowa tayi tace "son let go in sai ka gyra jikinka."

Shiru yayi bai da niyan motsawa da kyar ta lalla6asa  suka wuce ciki direct side dinsa aka ajesu ta wuce dashi tashiga toilet ta hadamasa ruwan wanka ya shiga nan tacewa Makinta yaje ya dauko masa trolley dinsa."

Cikin minti da basu wuce 15 ba ya shirya again cikin jeans da shirt hakuri sukayi ta basa ita da Mummy'n Makinta sai da taga ya sauko ta barsa suka fice shida Makinta."

 Suna cikin mota driver na tukaso Suna baya Nawaz yacewa Makinta "that small brat I have to teach her a lesson Tamin abinda ba'a taba yiminba.

 she's your cousin sister fa inji Makinta and Maya is middle age ka yafemata kawai.

Maya ya maimaita sunan cikin ransa can kasan zuciyarsa  yace her name was nice yayi Shiru bai sake magana ba har suka isa wani hadadden gida aka wangale gate suka shige.

Side dinda aka ware musu suka nufa da tunanin abinda Maya tayi masa da yanayinda tayi shiru da yake tambayanta yayi bacci. _wannan kenan_


*_DAGA ALKALAMIN✍_*

*_NEERALURV😍_*

     *_DA_*

*_ABDUL MR SMILE😊_*

Monday, 17 September 2018

MAYA

❣❣
   ❣
*MAYA*.....
❣❣
   ❣



1⃣0⃣

Via O. H. WπŸ“š
neeratlurv.blogspot.co.ke
Wattpad
@neerat_lurv


  ****
 2days later

  "Yau kwana biyu da dawowarsu Nawaz bai fita ko inaba Yana gida Yana hutawa abinsa Yama manta dawani alkawari daya  daukawa Malika kan zuwansa"
  "kwance yake kan 3seater ya lumshe ido kamar Mai bacci azahiri amma ba baccin yake ba
 kwatsam wayarsa ce kirar iPhone X Tafara ruri alamar kira ake ido yadan Kai Ya duba Mai kiran yaga Maly a rubuce dan karamin tsuka ya ja hade da yamutse fuska ya kauda Kai gefe. "
 
    "Wayar tayi ringing wajajen sau uku ana na hudun yakai hannu ya dauka fuskar sa a hade "
 
   "Daga bangaren Malika jin andauka yasa tasaki ajiyar xuciya yana jiyo wa ta wayar tace. "
 
 " Hello baby "
   
     "kamar baxai amsata yace Uhmm ina jinki "
 
  "tace baby tun shekaran jiya kace Zaka xo but i didn't see you "
 
  "Look Malika dama dan wannan kika kirani ok to hell with zuwan dana nace zanyi din am not coming "
   
  Ko bin ta kan abinda zata fada bai yiba ya tsinke wayar hade dajan tsaki yace oh gosh problem
 
  Malika najin ankashe wayar dama tasan za'a yi haka so just ta calming kanta hade da ajen wayanta gefe guda tace what can I do Gashi wani feelings ne ke furzgarta dan karamin tsaki taja hade da tashi taja mayafinta tayi ficewarta gaba daya

  Shi Kuwa Sarkin iyayi yi mood dinsace ta sauya gabadaya yaji zaman gidan ya fitamai a rai.
 
  Mikewa yayi ya shige daki hade da cire kayansa yaja towel Ya daura yayi shigewarsa toilet dan yin wanka.

  Mintuna da basu wuce 10mins ba ya fito yana tsane ruwan da ke kansa da jikinsa cikin dan kankanin lokaci ya shirya cikin kananan Kaya dasuka yi matukar karban sa sai kamshi dayake tashi ajikin sa Haka ya fice part dinsa ya wuce na mum dinsa "
 
  Kai tsaye ya shige dakin  ya Tarar da mummy hakimce kan kujera mai aikinta Mary na mata tausa "
 
  "Tana hangosa tafad'ad'a murmushinta tace oh son so you are coming as i expected ai na dauka kamanta nine yau kwata-kwata baka shigoba "
 
    "Dan murmusawa yayi yace "
 
   " No mummy not again complain ai gani nazo yana fadan haka yana zama kusa da ita "
 
   "Shafa kansa tayi hade da jan pointed nose dinsa tace how will i not be able to complain bayan you didn't miss me ta karasa maganar tana murmushi."
 
   "Ok fine I admit it but gani nazo and I miss so much today ya Bata light peck a hannu "
 
  " lol na yarda tace and by the way ya Kake "

   " Lpy qalau mummy "
   
  "yadan Mike yace am in hurry mum zan fita dama na biyane in dubaki kuma tunda you're fine i will be going."

   " ok a dawo lpy  tafada cike da nuna kulawa. "
 
   "Thank-you mummy I love you "
 
  " love you too son."
 
  " Kai yasa yafice yana murmushinsu irin na yan hutu direct parking space yanufa hade da zura key cikin black Benx  nasa aka hangame masa gate ya fice a gidan "
 
  " Yana tafiya a hankali kamar Wanda bai son jan motan music ne Ke tashi a motar wakan Lil kesh ta water bottle kansa kawai yake kadawa yana bin wakar can ya zaro wayan yayi dialing number din makinta bugu daya aka dau wayar. "

    " hello makinson kana ina fadar Nawaz kenan "
 
  "Ina nan Gaba wajen circular road "

   "okay you should wait there gani tahowa yanxu bai jira mai makinta zaiceba yayi hanging call din cike da isa. "
 
    " Figar motan yayi ya kama hanyan circular road cikin Mintuna da basufi  biyar ya isa can ya hango motan Makinta "
 
   "Kai dan iska na hangoka ka Karaso cewar Nawaz daya Kira makinta"

    " Makinta na karasowa yabude gaban motan ya shige hade da kaiwa Nawaz punch cikin wasa yace.

  " Kai Wai wa ka raina Hakane dazakana yiwa magana cikin command. "
 
  "Mtssw! Nawaz yaja tsaki yace ban son iskanci yanxu dinma dan na nemekane shiyasa"

  " Toh sarkin miskilai mai ke tafe dakai. "
 
  " Nothing just zaman gidan ne was boring and wannan mayar tadameni dakira that's all"
 
  "ko ba'a fadamasa ba yasan Malika yake referring so ya share zancen kawai hade da cewa let's go have fun dude"

  "okay let's go "
 
  " nan Makinta yashige motarsa Suka baxa yawo "


  ****
  8:30pm
 
 " Zaune suke kan dining table abinci suke ci cikin nutsuwa Daddy yakai kallonsa kan Mummy yace Swthrt kinsan Ali dan gidan Ya Umar Auren sa next week ne koh"

  "Yes sure honey ai ina kan shiri ma "
 
  "Yauwa next week Thursday zamu wuce insha Allah "
   
  Ok Mummy tace Allah ya kaimu "

  "Ameen ta amsa "

  "Nawaz dake kallonsu yace Dad wai  kana nufin Ali dincan Aure Zai Yi "

  "Of course Aure Zai yi "
 
  "Chab ya iya fada hade da jinjina Kai "

  "Dukkansu biyu kallonsa sukayi Suna masu murmushi. "
 
  " Daddy yace I forget to tell you  da kaifa zamu je. "
 
  "Daidai lokaci da ya kai abincin bakinsa ai kuwa ba shiri ya shake nan da nan. "
 
  "sai da yasha ruwa before yayi exclaiming What! No Dad you're just kidding right "
 
  " Dan hade rai Daddy yayi yace inama wasane garin mahaipan nawa zanyi maka wasa da shi "
 
  "Pls Daddy Karkace sai naje Wlh Bazan iya dazaman mota ba and beside kauye nefa "

  "Dan murmushi Daddy yayi sannan yace who tell you biu is a village kama sa a ranka tare dakai zamu tafi because umma na complain na rashin zuwanka."

   " Yana ya mutse fuska haka har yagama cin abinci badan yasoba ya fice ko da safe ma Bai yimusu ba "

  " Murmushi Mummy tayi tace wa Daddy Kaga Ka korarmin da D'a Ko "

  " shima smiling yake yace barsa kawai nan suka sauya hiran tasu


   " Nawaz part dinsa Yayi wucewarsa bedroom direct ya watsa ruwa yasa pajamas ya haye gado hade da jan laptop dinsa yana dannawa har bacci ya kwashesa"

    ****
" Washegari tun da safe misalin Karfe goma ya farka batare da yadamu yayi sallah ba yayi wanka Ya shirya abinsa tsab cikin wata dakkakiyar shadda sky blue dinkin half jamba ya feshe jikinsa da turarae Kai tsaye ya wuce site na Mummy tunda yanada tabbacin Daddy ya fita tun dazu. "

   "Da Sallama ya shige tana Zaune dakin duk kamshi turaren wuta yake lumshe ido Yayi don yana son turaren wuta yace Mummy Gaskiya turaren nan akoi dadi. "
 
   " Uhmm kaidai Kasani tafada tana murmushi."

   "Karasowa yayi yazauna gefenta ya dan kwanto da kansa kan cinyarta yana yamutse fuska yace good morning Mummy."

  "Morning my baby how was your night."

  "My night was flattered Mum but it's little disgusting."

  "Kansa tashafa tace Kai dai tashi kaci abinci bansan kanazama da yunwa."

  " Cikin shagwa6a yace Kai Mummy kedai sai kiyita cikawa mutum ciki da abinci."

  "karan hancin sa taja tace oya je kaci."

  "okay yafada yana Mikewa zuwa wajen dinning table din  nan yaga favorite dinsa Wato masa da miyan allayahu ai kuwa zama yayi yaci Sosai sannan yamike yamata sallama ya fice daga gidan."

  *_Command guest inn_*

   misalin sha daya 11:00 na Rana yana Zaune cikin wani wajen shakata dake wajen idonsa lumshe yake sai iska dake kadawa kadan kadan yadau tsawon lokaci ahaka kafin daga bisani Ya dau waya yayi dialing number din Malika."
 
  "Ai kamar jira take tanajin wayarta na ringing ta Kai hannu da sauri tadau wayar kafin tace wani abu tuni ya rigata yace."

   "Ki sameni a command yanxu Karki Bata min lokaci yana gama fadan haka ya tsinke wayar yana wani shan kamshi. "

 "Sanin halin abinta batawani Bata time ba taje tasamesa kamar yadda ya bukata nan suka Shana abinsu. " _wannan kenan_

   "Kwanaki Suna shudewa har yau yakama da ranar alhamis kuma shine randa Daddy yace zasu wuce Biu Dan haka sun shirya tsaf Nawaz kaidai suke jira kusan tundazu aka tura kiransa Gashi kusan 1hour yakara bai fita ba tsaki kadan Daddy yaja yace wai makinta baka fadamasa da wuri zamu wuce bane."

  "Makinta yace Dad na fadamasa fa."

  "Tsaki Dad yaja ya Kalli Mummy yace Aeesha kirasa Pls yazo mu wuce it's almost time."

  " Haka Mummy ta tawuce side na Nawaz a kwance kan couch tasamesa yana kallon music haushi ne yakamata takai masa Mari a cinya da karfi tace tashi shashasha."

 " Aucch! Yayi exclaiming yace Haba Mummy dubafa kiga hannunki jikine fa dasu."

  " Rufemin baki tace and only 10mins nabaka ka shirya ina jiranka a nan."

  "Hade rai yayi yawuce yana tura dan karamin bakinsa."

  "In less than 15mins ya shirya harda trolley bag dinsa ya fito  cikin Kanannan kaya yayi matukar kyau."

  "Haka Mummy tasa sa gaba suka wuce ."

  "Koda suka isa Daddy surutu yata masa Makinta kuwa kasa kasa yake mar dariya. "

  "Nan suka wuce cikin mota shida makinta Driver ya ja motar."

  "Haka su Daddy da  Mummy sai Kuma iyayen Makinta suma Nan aka hada convoy aka kama hanyar Biu. "




*_DAGA ALKALAMIN✍_*

*_NEERATLURV😍_*

         *_DA_*


*_ABDUL MR SMILE😊_*

Popular Posts