New Post

Tuesday, 13 November 2018

❣❣
  ❣

*MAYA!πŸ™πŸ»‍♀*

❣❣
  ❣

2⃣1⃣

Neeratlurv.blogspot.com
Wattpad
@neerat_lurv



       ***

Zuwan Inna ba karamin dadi yawa Maya ba, tanadawowa daga skul toh suna tare da Inna zasu yini tare..kamar yadda Inna tayi alkawari haka ta cikasa domin taje gidansu makinta sun sha hira da mamar makinta sai dare suka dawo..

   Sunfita yawo a Dan kawanakin da tayi Sadiya kuwa har gida taxo ta gaida inna, satin inna daya tace zata koma biu nan Maya harda kukanta wai Inna ta zauna karta koma da kyar Daddy ya lallasheta bayan yamata alkawarin zasu tafi Umara tare da Momi sati biyu masu zuwa nan da nan tayi shiru jin zata hau jirgi kuma ta ga kanta a Makkah wayayo ae tuni ta manta dawata tafiyar Inna...

   Ana gobe Inna zata koma suna a zazzaune a babban falon kasa na site din Daddy suna hira banda Nawaz da ya fita tun safe bai dawoba, suna cikin hiranne Nawaz ya doka sallama.. Duk suka amsa masa inna tace.

  “Ja'irin yaro kabi kasa yawo gaba ba maganan ajiye iyali ko?”

  Bakinsa ya tabe yaja karamar tsaki, Kayiwa uwar nace inna da fadin haka.. Amma Aliyu kana ganin yaron nan yake suburbudamin rashin kunya yake min tsaki wlh na tabba zai iya marina nan gaba mutum dogo ba wayo tana ta sababi saida Daddy yace"kiyi hkr mana Innata ae zan masa magana zai daina fah, toh naji tace... Shikuma gogon naku waje yasamu gefen Momi ya zauna yana jingina da kujera yace“auchh! Am damn tired wlh”, Sannu ya kasuwar Momi ta tambayesa cikin kulawa.

  Alhamadullilah Momi kasuwa tana kyau masha Allah, Okay haka ake so Momi tafada cikin kulawa, Baby bakiga yayanki bane ko sannu da xuwa babu bale ruwan sha Momi ke tambayar Maya...

  Baki ta cuno gaba kasa2 tace"toh ni ina ruwana da zuwan sa da rashin dawowarsa can fa ta matse masa, Idon Momi ta faka tawatsa masa harara sannan tace"barka da dawowa can kasan makoshi"  "yauwa" ya amsata a takaice bayan shima ya faki idonsu Daddy ya ballamata harara...

   Ruwan ta tashi ta kawomasa ta wuce daki abinta tana charting a waya da sadeeya..

 Bayan Maya ta bar wajen inna ta juyo da kallonta kan Daddy tace..

 “Aliyu sai yaushe kake shirin aurar da wannan tuxurun ne?”

   Inna wa keanan Daddy ya tambaya Kansa a kasa.

Au! Bakamasan kanada tuxuru aje gidanka ba sai na fadamaka sunan toh ina nufin mai gidana karamin wato wannan ta nuna Nawaz da yatsa.


  Toh inna ae nayi nayi dashi yayi auren amma sai cemin yake bai sami matar ba Daddy yafada cikin girmamawa...

  Hmmm! Lallekam biri yayi kama da mutum yanxu har wannan  mai idon magen zai cema baida wacce tayimasa toh nidai bai shiga kainaba kuma abinda nakeso so da kai kayi maza kadamasa ya cire matar aure amasa tun wuri ehen!ta gama maganar tana jinjinawa.

   Daddy yace haka za'a ayi insha Allah innata, Sa'annan ya juyo da kallonsa kan Nawaz daya saki bakin yana kallon inna dake ta faman sharhi kansa can underneath his breath kuma yace lalle kam matar nan ta taro match... Gyra murya Daddy yayi yace.

  "Son I hope you've had what inna says kuma nima since I have been begging you toh yanxu is a command sabida farin cikin mahaifiyata I gave you only a month kafitar da matar aure if not na fitarmaka da kaina.

  He was totally speechless and dumb can yayi gathering courage yace" Daddy I had you saying xaka fitarmin matar aure if ban fitar ba?"

  " Yeah that's what I say and am willing to do so" Daddy yabasa amsa in a serious tongue..

  "Auren dole Kenan ake shirin min?"

  "Duk yadda ka dauka you've Chance by choosing it before time goes Daddy yasake fadamanasa"

  "Oh C'mon Dad I know you're just kidding you can't do that."

  "Nawaz be serious am not joking with you huh! Daddy yafada in a loudly voice"

 Ido ya fiddo waje jin yadda Daddy yayi maganar da zafi zafi    yace" I didn't settle of getting married now beside i have not found my wife yet and I will not that's my decision yafada yana mikewa cike da kasaita yafara taku yana barin falon, ido kawai iyayen nasa suka bisa dashi"

  Sarai inna tasan ba maganar arziki Nawaz yayi ba ganin yadda yayi halin ko in kula nan ta maido da ganinta kan su Daddy kafin tace wani Abu Daddy yayi saurin cewa.

" Inna insha Allah zuwanki na gaba auren nawaz ne na miki alkawari"

  "Toh ba Matsala Allah ya kaimu"
   
     "Ameen"


  Nawaz na shiga daki ya kira makinta yace" oh boi! Aure fa Daddy zaimin"

  Dariya makinta yafashe da shi yace same with me yanxu old man yagama min maganar...

  Shima dariya yayi ya labartama makinta yadda suka yi da Daddy nan yasake kwashewa da dariyan, can yace we will talk about it later boi, OK kawai ya CE yayi hanging call din.....


  Kamar yadda inna tafada haka ko akayi gobe da misalin tara na safe inna ta bar Maiduguri takama hangar biu bayan irin artabu da akasaha da Maya da kyar aka bambareta jikin inna  tana kuka ita kanta innar saida tayi kuka....


 ****

  *_After 2 weeks_*


 Duk wani shirye shiryen tafiya su Momi sun kammala cikin satuttukan baya ciki harada yiwa Maya visa..

   Komai ya tafi daidai su Maya har gida akaje akawa sadeeya sallama..

  Yau takama jirginsu zai tashi misalin 10 na dare danhaka tun yamma sun shirya lokaci kawai suke jira already dama sun bar Maiduguri suna Abuja zasu tashi ta can..

   Suna zaune su uku da Momi, sai Daddy da Maya a babban falon gidan Daddy dake Abuja suna hira har Nawaz ya samesu, yana zama yasoma tsokanar Maya da yar kauye kar aje ayita kauyenci fa a can haka yayi tamata tun tana sharesa har ta soma matse hawaye saida Daddy yamasa magana ya daina..

  10 daidai  suna airport ana kiran sunan masu tafiya suna a tsaye dukkansu Nawaz ya zagayo gefen Maya daidai setin kunnenta ya kai bakinsa yace.

  "Idan akaje a roki Allah ya ragema mutum sha'awa mutum kwaila amma sai jarabar tsiya."

   Juyowa tayi ta kallesa sai ta kauda kallonta daga garesa sannan tace

  "Idan zan roka zansa harda kai Allah yaragema biyebiyen mata da shaye shaye tunda ni ba jiyau bane ganau ne naga bro makinta rannan na shigar da kai daki a buge kuma naji kana waya da yan mata dayawa and...bai Bari takarasaba yasa yatsansa ya bugemata baki."

   Auchh! Ta fada tana yarfe hannunta ta dago da niyan magana aka kira sunanta Dan haka da wuri ta bar wajen shikuma kallo yabita dashi na zaki gane kurenki idan kika sake, daga nan yayi wajen Momi sun sallama da ita...


  Suna nan tsaye har jirgin ya tashi.....



*_Daga Alkalamin✍_*

*_NEERATLURV😍_*

     *DA*

*_ABDUL MR SMILE😊_*


#Vote
#Comment
#Share

  1. #Love

Sunday, 11 November 2018

❣❣
  ❣

*MAYA!πŸ™πŸ»‍♀*

❣❣
  ❣

2⃣0⃣

Via O.H.WπŸ“š

neeratlurv.blogspot.co.ke

Wattpad
@neerat_lurv

 
    **Kwanaki biyu tayi a asibitin aka sallamota suka dunguma zuwa gida”
 
  Jikinta Alhamdullilah ta mulmule ciwon ciki na nan saidai shima Ba sosai Ba Dan tana shan magunguna ga allura dayake taimakawa wajen danne ciwon cikin”

 Saida ta share 1week lokacin jinin ya tafi kan tafara xuwa skul.

  Yau ta tashi da murnanta sabida xuwan Inna da ake tsammani a yau, ta daga hankalinta tun sanda Daddy yace Maya bataji dadiba take sababi wai sai ta zo ta duba jikallenta shine Daddy ya akai driver yaje ya daukota .

  Tun jiya Maya ke faman kai da komo a kitchen tana hadawa tsohuwa kayan kwadayi daidai Wanda xata  iya ci tayi su samosa, meat pie, dasu spring rolls, cokies da Momi ta koyar da ita.

  Saida ta hada komai ta shirya  xuwa skul har taso tayi letti Dan pass 7 kuma yau Short day 12:30 zasu tashi sabida jumma'a.

  Sanye take da uniform dinta Masu kyau da Dan karamin ash hijab dinta iya kafada tayi kyau matuka bayanta rataye da wata tsadaddiyar bag Golden littafaine ta rikesu a hannunta irin dogayen nan, A hankali take takunta mai matukar daukan hankali, yana daga balcony yana zaune waya ne hannunsa yana danne2 kamar ance yadago kansa ya hangota kasa dauke idonsa yayi kanta cikin ransa kuma fadi yake“
  _Bai  taba ganin mace datake tafiya cikn natsuwa wacce ta iya taku a hankali kamar Maya ba_”
 
  Yana cikin kallonta  ta juyo da fuskarta wow! Yafada a hankali  she looks cute this morning bai San sanda ya seta camera yasoma daukarta pics ba itakuma tana cikin gaisawa da mai Bawa flower ruwa Saida ya dauka kusan kala biyar  ya janye wayar ganin kamar zata juya yacigaba da duba wayansa, sarai ta gansa itama ta maxge kamar bata gansaba ta kwaye ta shige mota driver yaja suka bar gidan sai skul.”

  Suna tafiya Nawaz ya fiddo wayansa yashiga duba pics din Saida ya duba yaja Dan karamin tsuka yana mai jin haushin kansa na daukanta pics amma on the other side of him ya tsinci Kansa yana mai jin Dadi hade da murmushi Wanda bai San daliliba.

   ****

  12:40 dai dai Maya ta iso gida fully happy to see her Granny ko tsayawa rufe murfin Mota batayiba ta ruga guje tayi cikin gida tana ta faman kiran Innata! Innata!!, a falo ta cimmasu suna zazzaune ana hira Momi,Daddy da Granny banda Nawaz da inkacire sa yana wajen amma kallon kawai yake bai ko kallon direction dinsu, jin irin ihu da take ta faman kwalla na kiran innarta yasasa dakamata wata tsawa yace

  “Would you shut up your mouth kin bi  kin cikama mutane kunne da ihun ki mara dadin ji.”

 Ae karab Inna ta karba da cewa
 
  “Yo kaidin muryanka Nada dadin saurarone ae gwamma nata akan naka kuma har yanxu kana nan da mugun halin nan naka kana kuma takura jikalleta ko ae na cinmaka kuma zanyi maganinka”

tana ta sababi shi ko kallonta bayayi har ta gama surutun tsaki yaja yana sake tamke fuska, Inna ta harxuka tace “kayima uwarka Aeesha tsakin kuma idan Baka yi bakinka yayi tsayiba toh Baja kaiba tsaka kawai.”

 Tun da Maya ta shigo take haki ganin irin tsawa da Nawaz yadakamata yasata rakube gefe guda tana tsoronsa dan tasan muguntarsa.

  Daddy da Momi kam ido kawai suka bisu dashi, Inna ne ta tashi ta isa Inda Maya take ta rungumeta jikinta tana fadin daman nasan wannan bakin mugun yana nan da bakin halinsa baxai canxaba tajata zuwa inda take zaune ta zaunar da ita lafewa Maya tayi jikin inna tana gaidata cikin shagwa6a itakuma inna sai biyemata take Sundau tsawon lokaci haka kafin ta tashi tashige daki tayo wanka ta sauya kayanta xuwa Riga da wando na jeans da wata doguwar Riga kirar Indian dress iyaka guiwarta.

  Tundaxu Nawaz yabar falon dama Daddy kuma yafita zuwa sallah'n jumma'a sai karfe biyu suka shigo Daddy da Nawaz din suna zama bada jimawaba Makinta da iyayensa suka shigo nan waje ya kaure da hira inna abin nema ya samu sai xuba hira anci ansha sai kusan maghriba iyayen Makinta suka wuce gida bayan inna tace ran Sunday zataje gidan Nasu su yini itama.....


  *_Daga Alkalamin ✍_*


*_NEERATLURV😍_*

     *DA*

*_ABDUL MR SMILE😊_*


#vote
#Share
#Comment
#Love



# *One LoveπŸ’ž*
❣❣
  ❣
*MAYA!πŸ™*
❣❣
  ❣
1⃣9⃣
Via O.H.WπŸ“š
neeratlurv.blogspot.com
Wattpad
@Neerat__lurv


**Speed yakara sai gudu yake xabgawa, Ba abinda Momi take sai kuka tana rike da Maya, Daddy kuma sai addu'a yake kar Allah yasa yarinyar nan mutuwa tayi.
Allah kadai yakaisu hospital din dan irin gudu da Nawaz yake xabgawa, suna isa tundaga gate yarinka zabga horn tiiit! Kake ji.
Nurse! Nurse!! Nawaz ne keta faman kwalla wa nurses kira da saurin su suka karaso da gadon tura marasa lpy.
A guje suke tura gadon direct A/E ward akayi da ita likitocin wajen ne suka dukufa kanta domin ceto ranta.
Daddy yakasa zama yakasa tsaye haka wajen Momi, Nawaz na ganin ikon Allah duk da dakakkiyar zuciya irin ta Nawaz saida yaji ba dadi ganin yadda iyayensa suka tada hankulansu.
Mintuna sunfi talatin likitoci suka d'iba kafin suka fito Maya na kwance gadon marasa lpy ana turata wani private room acikin hospital din aka kaita idan dakin ya hadu.
Doctor na fitowa yacewa su Dad ku biyoni.
Suna biye dashi har suka isa ofis din nasa zama yayi suma suka sami wajen zama,yad'an zare farin gilashin idonsa yayi daidai kan kujerar sa yana share gumi, saida ya daidaita kansa before yafara cewa.
"Who are you to her?".
Daddy yayi saurin cewa "her parents and this ya nuna Nawaz yace"her brother you can feel free to talk."
Dan juyawa likitan yayi kan kujerarsa yasoma magana kamar haka.
Yace" a gaskiya yarinyar ku ta kasance daya daga cikin hallittun dan adam da sukeda karfin sha'awa kuma bugu da kari yanxun time na mensuration(jinin al'ada) shi zata fara shiya kawo ciwon ciki ya turniketa haka amma yanxu namata allura kuma zan yi mata prescribing magani da inta tashi sai a bata kafin jinin ya sauka insha Allah idan ta tashi xataji relief."
Ajiyan zuciya dukkansu suka sauke banda Nawaz daya tabe baki cikin ransa kuma yace dama kwaila ce yarinyar nan ashe yanxu ma zatafara jinin al'ada kuma wai takeda desire sosai tabdin.
Dan rubuce -rubuce Likita yayi a dan paper yabawa Daddy, godiya sosai Daddy yamasa suka fice.
Dakinda Maya take suka wuce Nawaz kam a reception yawuce ya zauna yana tabe baki.
A kwance suka sameta tafada dan lokaci guda fuskarta tayi fayau tana baccin abinta, Momi ce takarasa tana shafa dogon gashin kanta dakuma fuskarta Daddy kuma ya tsaya yana kallonta dakuma tausayinta.
****
_2hrs later_
Maya ta farfado lpy jiki da sauki saidai dan ciwon ciki daya ke damunta kadan2.
Momi da Daddy sun fita dan sayaen magunguna dakuma su pant,da always.
Nawaz ne zaune ya zubamata manya kuma oily eyes dinsa masu rikitarwa kanta na a gefe bata kallonsa.
"Ke kawaila Nawaz yafada da dan karfi."
Shiru kake ji bata amsa saba.
Dake fa nake Kwaila ke dakike kwance.
Sai yanxu ta fahimci da ita yake dan haka ta juya ido biyu sukayi cikin ranta kuma maimaita kalmar *kawaila* da ya kirata dashi take.
"Kin zubamin na mujiya kina kallona karki cinyeni mana, dan naga alama likita yace kina daya daga jerin masu yawan sha'awa ko ta kaina zaki farane yayi tambayan yana kanne mata ido daya.
Taji zafin kawaila daya kirata dashi ga kuma sha'awa dayace tana da shi wata irin kunya ce ta rufeta take ta kauda idonta daga nasa ta juya baya.
Kafada ya dage alamar ko ajikinsa hakan da tayi.
Daidai nan Momi ta shigo leda hannunta bayanta kuma Daddy ne yashigo, gefen Maya Momi ta zauna tace.
"Sannu baby"
Gyad'a kai kawai Maya take.
"ina da ina ne ke miki ciwo yanxu Momi tasake tambayarta"
ido tadan rufe tana cize lips a hankali tace"babu amma cikina yana min kadan kuma inajin yunwa."
Oppss! sorry wlh na manta duk na rikice driver na hanya da shayin yanxu zai karaso kinji."
Kai tasake dagawa alamar "toh taji"
Matsawa Daddy yayi yana shafa kanta yace"Mamana jiki da sauki koh".
Tace"Alhamdullilah"
Yace"Allah yabaki lpy Mamana"
"Ameen ya rabbi ta amasa sa"
Shirune yabiyo baya nadan wasu lokuta, ana cikin haka driver yakawo brkfast daga gida da shayin nan Momi tahadamata tasha sosai.
Daddy yakula da Nawaz da bai ci abincin ba yace"Boy kai baka abincin bafa"
"Daddy bazan iya cin abinci a hospital dinba."
"Okay na gane."
mikewa Nawaz yayi yace i will be on my way zanje gida na dan huta narama baccin da ban samuba jiya am sleepy yafada cikin sanyin murya."
"Toh" Momi tafada, daga bisani kuma Daddy yace"baza mutafi tare nima inada meeting a government house by 10 na safe."
Sallama sukayi masu bayan Daddy ya tambayi Maya meye takeso yaxomata dashi tace"Ice cream" nan yace toh zai kawomata.
Sosai Momi ke kula da ita ana haka har jinin ya sauka Momi ta koyamata yadda ake amfani da pad sai kuma ta ajiyeta tana bata darusa kan tsabtace jiki da sauransu.
Nawaz sun isa gida ya wuce part dinsa wanka yayi yaci breakfast ya kawanta nan bacci ya daukesa.

*_Daga Alkalamin✍_*
*_NEERATLURV😍_*
*_DA_*
*_ABDUL MR SMILE😊_*
_Kuyi hakuri da wannan pls wollah ina busy ne but you guys should manage i will try to make d next page a bit long enjoy it, chill heart you❤_
#vote
#share
#comment
#Love
*_One love_*πŸ’ž

Popular Posts